Farashin Naira a kasuwar ‘yan canji ta dan farfado a ranar Laraba, 29/05/2024.
An sayi dalar Amurka akan Naira 1,375, idan aka kwatanta da farashin da aka sayi dalar ranar Talata watau Naira 1,500, za’a iya cewa farashin Nairar ya farfado.
Saidai kuma a kasuwar Gwamnati, farashin Nairar faduwa yayi inda aka sayi dala akan Naira, 1,339.33.
Tashi da faruwar Dala dai na daya daga cikin abubuwan dake ciwa Najeriya tuwo a kwarya.