Thursday, January 30
Shadow

Kungiyoyin kare hakkin masu amfani da wayoyin hannu sun maka Gwamnati a kotu saboda karin kudin kiran waya da kaso 50

Kungiyoyin dake fafutuka dan kare hakkin masu amfani da wayar hannu aun mikawa hukumar kula da sadarwa ta kasa NCC korafin rashin amincewarsu kan karin kudin kiran waya da kaso 50 cikin 100.

Sun mika korafinne nan ranar Juma’ar data gabata inda suka bukaci a basu amsa nan da ranar Talata ko su shiga kotu.

Kamfanonin sadarwa sun nemi a basu damar kara kudin kiran waya da kaso 100 bisa dari watau su nunka amma NCC ta basu damar kara kaso 50 cikin 100.

Wannan kari dai shine irinsa na farko a cikin kusan shekaru 10 da suka gabata.

Kungiyar NATCOMS na daga cikin kungiyoyin da suka shigar da wannan korafi, kuma shugabanta, Adeolu Ogunbanjo, ya shaidawa jaridar Punchng cewa, tunda har ranar Talata basu ji amsa ba daga NCC, to basu da zabin da ya wuce su shiga kotu.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tinubu ta bada umarnin a fara sayar da man fetur akan sama da Naira Dubu daya kowace lita

Jaridar ta yi kokarin jin ta bakin kakakin NCC, Reuben Mouka saidai yaki cewa komai akan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *