Thursday, October 3
Shadow

Abin Takaici: Ji yanda aka bar na’urar dake nuna inda ‘yan Bindiga suke ta lalace da gangan

Wani tsohon babban jami’in dansanda ya bayyana yanda aka bar na’urar dake nuna inda ‘yan bindiga suke ta lalace.

Na’urar dai ana amfani da ita wajan sanin inda ‘yan Bindiga suke a yayin da suka yi amfani da waya kuma a kamasu.

A baya an yi amfani da wannan na’ura wajan kama wadanda suka yi garkuwa da Olu Falae kuma aka kwace kudaden fansar da suka karba na Miliyan 5.

Saidai a yayin da Na’urar ke hannun kulawar ‘yansanda kuma aka rika samun shuwagabannin ‘yansanda daban-daban,wasu basu san ma yanda ake amfani da ita ba.

Yayin da wasu sun sani amma suka ki bayar da kudin da za’a rika sabuntata da kuma biyan kudin wata-wata na tabbatar da tana aiki.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Rundunar yan sandan Najeriya na neman wani bátưré ruwa a jallo bayan ta bakaɗo yana kitsa yadda za a yiwa Tinubu júyíɲ mulkí

Hakan yasa na’urar ta lalace aka daina amfani da ita kwata-kwata.

Hakanan na’urar a karshe komawa ta yi ‘yan siyasa na amfani da ita wajan bibiyar abokan hamayyarsu da kuma ‘yan matan da suke nema.

Rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa akan wannan na’ura ya nunar da cewa, amma wannan sabon shugaban ‘yansanda dake kai yanzu, yasa an dawo da na’urar ta ci gaba da aiki amma abin takaici shine, hakan bai hana ‘yan Bindigar cin karensu babu babbaka ba a yankuna daban-daban na kasarnan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *