Thursday, December 25
Shadow

An dakatar da bayar da làsìsìn Màkàmì irin su Bhìndìghà ga ‘yan Najeriya dan su yi amfani da ita wajan kare kansu>>Inji Hukumar ‘yansandan Najeriya

Hukumar ‘yansandan Najeriya ta tabbatar da cewa, dokar hana bayar da lasisin Mallakar Bindiga a Najeriya dan kariyar kai har yanzu tana aiki.

Me magana da yawun hukumar, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka a wani martani da yayi game da ikirarin da wani yayi cewa ya mallaki Bindigar AK47.

Benjamin yace a doka ko da ana bada lasisi, Bindigar AK47 bata cikin wadda aka amince farar hula su rike.

Yace amma a yanzu har yanzu ba’a dage dokar data hana bayar da lasisin Mallakar Bindiga dan kariyar kai ba.

Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai inda mutane suka rika tambayar to su tsageran daji ina suka samo nasu Bindigun?

Karanta Wannan  Yanzu-Yanzu: Bayan aiko da wakilanta suka ganewa idanunsu abinda ke faruwa a Najeriya, kasar Amurka tace lallai gaba dayan 'yan Najeriya ne ya kamata a samarwa da tsaro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *