
Wannan wani mutum ne a jami’ar jihar Ebonyi me suna Dr. Enyi onyebuchi Paul wanda a shekarar 2007 ya samu aikin goge-goge a makarantar.
Saidai ya jajirce inda ya ci gaba da karatu har ya samu Digiri na daya zuwa na 3 a makarantar.
Saidai duk da wannan kokari da yayi, ba’a mayar dashi malami me koyarwa ba a jami’ar.
An ci gaba da barinsa a matsayin me goge-goge inda ake biyansa Albashin Naira Dubu 70.
An dai yi zargin saboda bashi da kafa ne shiyasa ya kasa samun aikin koyarwa a makarantar.