
Dan Najeriya, Chijioke Igbokwe me shekaru 59 da yayi ikirarin yin kasuwancin Sayar da kaya an kamashi da hadiyar daurin hodar Iblis har guda 81.
Ya hadiyi wannan kwayane da niyyar kaita kasar Lebanon inda aka masa alkawarin idan ya kai za’a bashi dala $3000.
Saidai an yi sa’a hukumar NDLEA ta kamashi inda kuma ya kasa yin kashin daurin da ya hadiya kamar yanda aka saba.
Sai da ta kai ga an yi masa tiyata aka samu ciro guda 57 daga cikin 81 daya hadiya.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana haka inda yace sun ajiye mutumin tsawon kwanaki 5 amma dauri 24 kadai ya iya yin kashinsu daga cikin 81 da ya hadiya wanda hakanne yasa dole aka yi masa tiyata.