Saturday, May 31
Shadow

Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba zai bar jam’iyyar PDP ba amma ya fadi dabarar da zasu yi amfani da ita dan kawar da Gwamnatin Tinubu

Madugun Adawar Siyasa A Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yana nan daram a cikin jam’iyyar PDP, kuma ba shi da niyyar ficewa daga cikinta. Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da mata mambobin Kwamitin Amintattu na jam’iyyar (BoT) da suka kai masa ziyara domin neman hanyoyin ceto jam’iyyar daga rushewa gaba daya.

A cewar Atiku, rahotannin da ke cewa yana shirin barin PDP zuwa wata jam’iyya kamar SDP ba su da tushe balle makama, kuma an kirkire su ne domin rikita shirin kafa kawancen jam’iyyun adawa da ake yi. Ya jaddada cewa yana nan a matsayin cikakken memba na PDP, kuma yana jagorantar yunkurin kafa kawancen jam’iyyun adawa domin kalubalantar jam’iyyar APC a zaben 2027.

Karanta Wannan  Majalisar Dattawa ta jinkirta muhawara kan ƙudirin dokar ta-ɓaci a Rivers

A wata ganawa da aka yi a Abuja, Atiku ya tabbatar da cewa yana tare da wasu fitattun ‘yan siyasa kamar Peter Obi na jam’iyyar Labour Party, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, da wasu shugabanni na jam’iyyun adawa, domin kafa kawancen siyasa da zai karfafa gwiwar ‘yan adawa wajen kalubalantar gwamnatin APC a zaben 2027.

Atiku ya bayyana cewa wannan kawance zai hada dukkan jam’iyyun adawa, ciki har da PDP, domin samar da wata sabuwar dama ga ‘yan Najeriya ta hanyar sauya akalar mulki daga hannun APC. Ya kuma karyata jita-jitar cewa yana shirin barin PDP, yana mai cewa hakan ba zai taimaka wa yunkurin kafa kawancen jam’iyyun adawa ba.

Karanta Wannan  Idan Namiji ya miki Ba daidai ba kina son yin maganinshi, kawai ki kalamai sharrin cewa ya miki Fyàdè>>Inji Wannan matar

A karshe, Atiku ya bukaci ‘yan Najeriya da su goyi bayan wannan yunkuri na kafa kawancen jam’iyyun adawa domin ceto kasar daga halin da take ciki, tare da tabbatar da cewa yana nan daram a cikin jam’iyyar PDP kuma yana da kwarin gwiwar samun nasara a zaben 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *