
Ta tabbata dai Hadaka me karfi tsakanin Atiku da Peter Obi ta kullu, APC ta kadu inda ta yi magana kan lamarin
Rahotanni na kara bayyana dake tabbatar da alaka me karfi tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi ta kullu.
Rahotannin sun ce, duka bangarorin sun saka hannu a wata yarjejeniya da suka akince da ita.
A tafiyar dai akwai tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi da sauransu.
Hakanan rahoton yace sun kuma amince da komawa jam'iyyar ADC da kuma saka kudi dan gyara jam'iyyar.
Saidai duk da El-Rufai shi yana SDP ne, rahoton yace da zarar an kammala shirya komai, za'a sanar da kulla alaka tsakanin SDP da ADC din.
A bangaren APC kuwa, sakataren jam'iyyar Ajibola Basiru ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu shine uban hada kan al'umma kuma suna da yakinin shi zai lashe zaben shekarar 2027.