Dangote ya karyata maganar NNPCL cewa a farashin Naira 898 ya sayar musu da man fetur
Matatar man fetur ta Dangote ta musanta ikirarin kamfanin mai na kasa,NNPCL da yace ya sayo mai na farko daga Dangote akan farashin Naira 898 akan kowace lita.
Me magana da yawun kamfanin,Mr Olufemi Soneye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Yace da dala aka sayar musu da danyen man fetur dun da suka saya dan haka suma da dala suka sayarwa da kamfanin na NNPCL da tataccen man fetur din.
Ya bayyana cewa kuma mansu zai isa kowane sako da lungu na kasarnan.
Yace a saurari kwamitin da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kafa kan lamarin shine zai bayyana farashin man nasu.