Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun kashe dan sanda daya da wani dan banga da ke sintiri a jihar Sokoto.
An gano cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3 na safiyar ranar Litinin a Kwanan Milgoma da ke kan titin Sokoto zuwa Bodinga.
Ma’aikatar Gidaje da Ci Gaban Birane ta Tarayya, ta fara gina gidaje 500 a Jihar Kano.
Aikin ginin gidajen da aka yi wa laƙabi da “Renewed Hope Estate” na wakana ne a ƙauyen Lambu da ke ƙaramar hukumar Tofa.
Aikin ya haɗa da gina gida mai ɗaki biyu, ɗaki ɗaya, da kuma waɗanda ke da ɗaki uku.
A lokacin da ya kai ziyara wajen aikin, Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Ahmed Musa Dangiwa, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aikin ke tafiya. Ya ce aikin ba ya sauri kamar yadda aka tsara tun da fari.
Ya gargaɗi wanda aka bai wa kwantiragin da ya hanzarta ko kuma gwamnat ta ƙwace aikin daga hannusa. Ya kuma ce gwamnatin na son ganin an kammala aikin nan da ƙarshen shekara.”
Kwantiragin, wanda manajan aikin Haruna Lawal ya wakilta, ya bai wa ministan tabbacin cewa za su ƙara ƙ...
INNĄ LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UNlƝ.
Allah Ya Yiwa Mahaifiyar Tsohon Shugaban Najeriya Marigayi Umaru Musa Yar'adua Hajiya Dada Rasụwa Yanzun Nan A Unguwar Yar'adua Da Ke Cikin Garin Katsina
Allah Ya Jikanta Da Rahama!
Daga Hon. Saleh Shehu Hadejia
Rundunar yan sandan Najeriya a yau Litinin ta saka cigiya tana neman wani bature dan kasar Birtáɲiya dake zaune a Najeriya Andrew Wynne (wanda aka fi sani da Andrew Povich ko Drew Povey), bisa zarginsa da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
Rundunar ta ce tana da ƙwararan hujjjoji bisa zargin da take yi wa mutumin wanda ya kama haya a ginin hedikwatar kungiyar ƙwadago dake Abuja inda yake sayar da litattafai don yin badda kama, a haka yake ta kitsa mugun nufin nasa, sannan ya bude wasu wajajen kasuwanci
Me zaku ce?
Daga Comr Nura Siniya
Manya-manyan ‘yan adawa uku a Nijeriya da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar, kwankwaso da Peter Obi na tattaunawa kan yiwuwar hadaka gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Mataimakin kakakin jam’iyyar PDP na kasa Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
Abdullahi ya ce, za su ajiye muradun kashin kansu a gefe su kulla kawance mai karfi don ceto Nijeriya a cikin kangin da jam’iyyar APC ta cefa kasar a shekarar 2027.
Ana dai ganin dunkulewar waje daya na da alaƙa da zaɓen shugaban kasa 2027 don kawar da gwamnatin APC kamar yadda masu sharhi suka bayyana.
Me za ku ce kan wannan yunkuri?
Wani magidanci a jihar Abia ya danne matarsa ya kwakule mata idanuwa bisa niyyar yin kudin sihiri.
Mutumin me suna Lawrence Uzor yana sana'ar Alminiyum ne.
Lamarin ya farune a Adiele Estate dake karamar hukumar Umueze Ibeku in Umuahia ranar Asabar 24 ga watan Augusta.
Mutumin dai yayi amfani da wuka ne ya kwakule idanun matar tasa yayin da take bacci.
Me gidansu data ji ihu cikin dare ta yi kokarin kai dauki itama ya illatata amma daga baya an kamashi, inda su kuma wanda suka jikkata an garzaya dasu zuwa Asibiti.
Uwar gidan gwamnan jihar, Mrs Priscilla Otti ta bayar da tabbacin daukar matakin da ya dace akan lamarin inda ta bayar da kudi dan a kula da wadanda suka jikkata.
Wani tsohon babban jami'in dansanda ya bayyana yanda aka bar na'urar dake nuna inda 'yan bindiga suke ta lalace.
Na'urar dai ana amfani da ita wajan sanin inda 'yan Bindiga suke a yayin da suka yi amfani da waya kuma a kamasu.
A baya an yi amfani da wannan na'ura wajan kama wadanda suka yi garkuwa da Olu Falae kuma aka kwace kudaden fansar da suka karba na Miliyan 5.
Saidai a yayin da Na'urar ke hannun kulawar 'yansanda kuma aka rika samun shuwagabannin 'yansanda daban-daban,wasu basu san ma yanda ake amfani da ita ba.
Yayin da wasu sun sani amma suka ki bayar da kudin da za'a rika sabuntata da kuma biyan kudin wata-wata na tabbatar da tana aiki.
Hakan yasa na'urar ta lalace aka daina amfani da ita kwata-kwata.
Hakanan na'urar a karshe komawa ta yi 'yan siyasa na amfani d...
Rahotanni sun bayyana cewa akwai yiyuwar man fetur zai yi tsada akan farashin da ake saye yanzu saboda fitowa da kamfanin mai na kasa, NNPCL yayi ya bayyana cewa ana binsa dan karen bashin da zai iya jefa kasarnan cikin wahalar man fetur.
A baya dai kamfanin man na kasa NNPCL ya karyata rahotanni da yawa dake cewa ana binsa bashi, amma a yanzu ya fito ya bayyana da kansa cewa da gaskene.
Masu kawo man Najeriya dai sun bayyana cewa yanda ake kasuwancin shine idan suka kawo man bayan kwanaki 90 ake biyansu kudadensu amma yanzu suna bin basukan da kamfanin man na kasa,NNPCL ya kasa biya.
Kamfanin man dai ya tabbatar da wannan matsala inda yace amma yana hadin gwiwa da sauran ma'aikatu dake da alaka dasu dan tabbatar an warware wannan matsala.
Wani gurin dake yin gwajin kwayoyin halitta na DNA dake legas me suna Smart DNA ya wallafa bayanan dake dauke da wanda suka fi yin gwajin a tsakanin kabilun Najeriya.
Shi dai gwajin DNA a mafi yawanci ana yinsa ne idan miji na zargin matarsa ta yi tarayya da wasu maza a waje ta kawo masa dan da ba nasa ba gida.
Dan haka idan wannan zargi ya shiga sai a je wajen gwaji a yi gwajin na DNA dan tabbatar da dan da ake takaddama akansa ko na mijin ne ko kuwa a'a.
A bayanan da Smart DNA suka fitar,sun ce kaso 53 cikin dari watau fiye da rabi, yarbawane ke zuwa yin wannan gwaji,sai kuma kaso 33.1 Inyamurai ne ke zuwa yin wannan gwaji, sai kuma kaso 1.20 Hausawa ne kezuwa yin wannan gwaji.
Bayanan sun bayyana cewa, 1/4 na mazan da sukw zuwa yin wannan gwajin ana gano cewa ba sune suka h...