Akwai yiyuwar a fada wahalar Man fetur saboda NNPCL tace bashi ya mata yawa
Rahotanni sun bayyana cewa akwai yiyuwar man fetur zai yi tsada akan farashin da ake saye yanzu saboda fitowa da kamfanin mai na kasa, NNPCL yayi ya bayyana cewa ana binsa dan karen bashin da zai iya jefa kasarnan cikin wahalar man fetur.
A baya dai kamfanin man na kasa NNPCL ya karyata rahotanni da yawa dake cewa ana binsa bashi, amma a yanzu ya fito ya bayyana da kansa cewa da gaskene.
Masu kawo man Najeriya dai sun bayyana cewa yanda ake kasuwancin shine idan suka kawo man bayan kwanaki 90 ake biyansu kudadensu amma yanzu suna bin basukan da kamfanin man na kasa,NNPCL ya kasa biya.
Kamfanin man dai ya tabbatar da wannan matsala inda yace amma yana hadin gwiwa da sauran ma'aikatu dake da alaka dasu dan tabbatar an warware wannan matsala.