Wednesday, January 15
Shadow

Author: Auwal Abubakar

YANZU-YANZU: Rundunar yan sandan Najeriya na neman wani bátưré ruwa a jallo bayan ta bakaɗo yana kitsa yadda za a yiwa Tinubu júyíɲ mulkí

YANZU-YANZU: Rundunar yan sandan Najeriya na neman wani bátưré ruwa a jallo bayan ta bakaɗo yana kitsa yadda za a yiwa Tinubu júyíɲ mulkí

Duk Labarai
Rundunar yan sandan Najeriya a yau Litinin ta saka cigiya tana neman wani bature dan kasar Birtáɲiya dake zaune a Najeriya Andrew Wynne (wanda aka fi sani da Andrew Povich ko Drew Povey), bisa zarginsa da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu Rundunar ta ce tana da ƙwararan hujjjoji bisa zargin da take yi wa mutumin wanda ya kama haya a ginin hedikwatar kungiyar ƙwadago dake Abuja inda yake sayar da litattafai don yin badda kama, a haka yake ta kitsa mugun nufin nasa, sannan ya bude wasu wajajen kasuwanci Me zaku ce?
YANZU-YANZU: Atiku, Kwankwaso Da Peter Obi Sun Fara Tattaunawa Domin Hadewa Waje Daya Don Tunkarar Zaben 2027

YANZU-YANZU: Atiku, Kwankwaso Da Peter Obi Sun Fara Tattaunawa Domin Hadewa Waje Daya Don Tunkarar Zaben 2027

Duk Labarai
Daga Comr Nura Siniya Manya-manyan ‘yan adawa uku a Nijeriya da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar, kwankwaso da Peter Obi na tattaunawa kan yiwuwar hadaka gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2027. Mataimakin kakakin jam’iyyar PDP na kasa Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin. Abdullahi ya ce, za su ajiye muradun kashin kansu a gefe su kulla kawance mai karfi don ceto Nijeriya a cikin kangin da jam’iyyar APC ta cefa kasar a shekarar 2027. Ana dai ganin dunkulewar waje daya na da alaƙa da zaɓen shugaban kasa 2027 don kawar da gwamnatin APC kamar yadda masu sharhi suka bayyana. Me za ku ce kan wannan yunkuri?
HOTUNA: Kalli yanda magidanci ya kwakule idanun matarsa dan yin sihirin neman kudi

HOTUNA: Kalli yanda magidanci ya kwakule idanun matarsa dan yin sihirin neman kudi

Duk Labarai
Wani magidanci a jihar Abia ya danne matarsa ya kwakule mata idanuwa bisa niyyar yin kudin sihiri. Mutumin me suna Lawrence Uzor yana sana'ar Alminiyum ne. Lamarin ya farune a Adiele Estate dake karamar hukumar Umueze Ibeku in Umuahia ranar Asabar 24 ga watan Augusta. Mutumin dai yayi amfani da wuka ne ya kwakule idanun matar tasa yayin da take bacci. Me gidansu data ji ihu cikin dare ta yi kokarin kai dauki itama ya illatata amma daga baya an kamashi, inda su kuma wanda suka jikkata an garzaya dasu zuwa Asibiti. Uwar gidan gwamnan jihar, Mrs Priscilla Otti ta bayar da tabbacin daukar matakin da ya dace akan lamarin inda ta bayar da kudi dan a kula da wadanda suka jikkata.
Abin Takaici: Ji yanda aka bar na’urar dake nuna inda ‘yan Bindiga suke ta lalace da gangan

Abin Takaici: Ji yanda aka bar na’urar dake nuna inda ‘yan Bindiga suke ta lalace da gangan

Duk Labarai
Wani tsohon babban jami'in dansanda ya bayyana yanda aka bar na'urar dake nuna inda 'yan bindiga suke ta lalace. Na'urar dai ana amfani da ita wajan sanin inda 'yan Bindiga suke a yayin da suka yi amfani da waya kuma a kamasu. A baya an yi amfani da wannan na'ura wajan kama wadanda suka yi garkuwa da Olu Falae kuma aka kwace kudaden fansar da suka karba na Miliyan 5. Saidai a yayin da Na'urar ke hannun kulawar 'yansanda kuma aka rika samun shuwagabannin 'yansanda daban-daban,wasu basu san ma yanda ake amfani da ita ba. Yayin da wasu sun sani amma suka ki bayar da kudin da za'a rika sabuntata da kuma biyan kudin wata-wata na tabbatar da tana aiki. Hakan yasa na'urar ta lalace aka daina amfani da ita kwata-kwata. Hakanan na'urar a karshe komawa ta yi 'yan siyasa na amfani d...
Akwai yiyuwar a fada wahalar Man fetur saboda NNPCL tace bashi ya mata yawa

Akwai yiyuwar a fada wahalar Man fetur saboda NNPCL tace bashi ya mata yawa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa akwai yiyuwar man fetur zai yi tsada akan farashin da ake saye yanzu saboda fitowa da kamfanin mai na kasa, NNPCL yayi ya bayyana cewa ana binsa dan karen bashin da zai iya jefa kasarnan cikin wahalar man fetur. A baya dai kamfanin man na kasa NNPCL ya karyata rahotanni da yawa dake cewa ana binsa bashi, amma a yanzu ya fito ya bayyana da kansa cewa da gaskene. Masu kawo man Najeriya dai sun bayyana cewa yanda ake kasuwancin shine idan suka kawo man bayan kwanaki 90 ake biyansu kudadensu amma yanzu suna bin basukan da kamfanin man na kasa,NNPCL ya kasa biya. Kamfanin man dai ya tabbatar da wannan matsala inda yace amma yana hadin gwiwa da sauran ma'aikatu dake da alaka dasu dan tabbatar an warware wannan matsala.
Yarbawane suka fi kowace kabila a kasarnan yin gwajin DNA dan gano cewa ko matansu sun ci amanarsu ta hanyar basu ‘ya’yan da ba nasu ba, Hausawa basu cika yin wannan gwaji ba

Yarbawane suka fi kowace kabila a kasarnan yin gwajin DNA dan gano cewa ko matansu sun ci amanarsu ta hanyar basu ‘ya’yan da ba nasu ba, Hausawa basu cika yin wannan gwaji ba

Duk Labarai
Wani gurin dake yin gwajin kwayoyin halitta na DNA dake legas me suna Smart DNA ya wallafa bayanan dake dauke da wanda suka fi yin gwajin a tsakanin kabilun Najeriya. Shi dai gwajin DNA a mafi yawanci ana yinsa ne idan miji na zargin matarsa ta yi tarayya da wasu maza a waje ta kawo masa dan da ba nasa ba gida. Dan haka idan wannan zargi ya shiga sai a je wajen gwaji a yi gwajin na DNA dan tabbatar da dan da ake takaddama akansa ko na mijin ne ko kuwa a'a. A bayanan da Smart DNA suka fitar,sun ce kaso 53 cikin dari watau fiye da rabi, yarbawane ke zuwa yin wannan gwaji,sai kuma kaso 33.1 Inyamurai ne ke zuwa yin wannan gwaji, sai kuma kaso 1.20 Hausawa ne kezuwa yin wannan gwaji. Bayanan sun bayyana cewa, 1/4 na mazan da sukw zuwa yin wannan gwajin ana gano cewa ba sune suka h...
Mutane a jihar Sokoto sun biya ‘yan Bindiga Naira Biliyan 160 a matsayin kudin fansa

Mutane a jihar Sokoto sun biya ‘yan Bindiga Naira Biliyan 160 a matsayin kudin fansa

Duk Labarai
A yayin da al'ummar jihar Sokoto ke fama da matsananciyar matsalar tsaro, mutane a karamar hukumar Sabon Birni sun biya 'yan Bindiga makudan kudade a matsayin kudin fansa. Wata kungiya me suna, Gobir Development Association ta bayyana cewa mutanen yankin sun biya Naira Biliyan 160 a matsayin kudin fansa ga 'yan Bindigar. Shugaban kungiyar, Idris Alhassan Gatawa ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda yace kuma an tafka asarar Naira Biliyan 2 a hannun 'yan Bindigar. Ya kuma bayayyana cewa, mafi yawan gonaki mutane basa iya zuwa saboda ayyukan 'yan Bindigar wanda hakan ya kawo wahalar tattalin arziki da kuma karancin abinci me gina jiki. Ya roki gwamnati data kawowa yankin nasu tallafi.
Motocin dake kan titunan Najeriya sun rage saboda tsadar rayuwa da wahalar man fetur

Motocin dake kan titunan Najeriya sun rage saboda tsadar rayuwa da wahalar man fetur

Duk Labarai
Babban lauya me rajin kare hakkin bil'adama, Femi Falana ya koka da cewa, tsadar rayuwa da wahalar man fetur yasa an sami karancin ababen hawa a titunan Najeriya. Falana ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV. Koken nasa na zuwane bayan da kamfanin mai na kasa, NNPCL ya bayyana cewa bashi ya masa katutu wanda hakan zai iya shafar wadatar man fetur a Najeriya. Falana yace a lokacin da rayuwa ke da sauki a Najeriya, kamfanin man na kasa,NNPCL ya bayyana cewa yana biyan kudin tallafin man fetur na lita miliyan 68. Yace amma yanzu da aka shiga halin matsi, babu motoci da yawa akan titunan Najeriya, har yanzu dai NNPCL tana gayawa mutane cewa tana biyan kudin tallafi akan litar man fetur miliyan 68. Yace wannan ba abinda hankali zai dauk...
Hoto: An kama mutane na 9 saboda yin kashi a bainar jama’a

Hoto: An kama mutane na 9 saboda yin kashi a bainar jama’a

Duk Labarai
Hukumar kula da muhalli ta jihar Legas ta sanat da kama mutane 9 saboda yin kashi a bainar jama'a. Kwamishinan muhalli na jihar, Tokunbo Wahab ne ya bayyana hakan inda yace sun dukufa dan ganin sun hana fitsari da kashi a bainar jama'a a Legas dan tabbatar da tsaftar garin. Ya kara da cewa a baya sun kama mutane 17 saboda yin kashi da fitsari a bainar jama'a da kuma kin amfani da gadar sama da aka ware dan mutane.