Wannan wani dan kasar Senegal ne da ya hadiyi zuciya ya rigamu gidan gaskiya saboda haushin yanda kasar Belgium ta ciresu daga gasar World Cup.
Mutumin ya rasu ne a filin wasa bayan da Belgium tawa Senegal 3-0.
Tuni dai aka fitar da gawarsa daga filin wasan.
https://twitter.com/i/status/2072731830516662751
Wasu manyan giwaye sun bayyana a karamar Hukumar Andoni dake jihar Rivers.
Giwayen sun bayyana ne bayan wani ruwa da aka yi inda mutane suka taru suna kallonsu.
https://twitter.com/i/status/2072590377333256664
Wadannan wasu 'yan daudu ne da suka Shekye ayarsu a shekarun da suka gabata a sabon garin Kano.
Wata jarida a wancan lokacin ta yi hira dasu inda tace mafi yawanci suna zaunene a layin Abedi, da Freetown, da Santgiwa da Weatherhead.
Rahoton yace sukan bayar da kansu ne ga maza dan su biya bukatarsu su kuma a biyasu, kamar dai yanda mata masu zaman kansu ke yi.
Sun bayyana cewa, ana biyansu kamar Naira 100 zuwa Naira 400 idan masu kudi suka daukesu.
An dauki Rahoton ne a shekarar 1988.
'Yan daudun sukan koma kawalai idan ya zamana babu kasuwar daudu, kamar yanda rahoton ya nunar.
Rahotanni sun bayyana cewa, An gano tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya gabatarwa da babbar kotu a jihar Kaduna takardar da yace babban Asibitin kasa ne ya bashi data tabbatar da cewa bashi da lafiya dan a bayar da belinsa.
Saidai ICPC dake karan Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ta bayyana cewa Daraktan Asibitin na kasa, Professor Muhammad Raji Mahmud, ya karyata cewa asibitin bai baiwa malam Nasiru Ahmad El-Rufai takardar cewa bashi da lafiya ba.
ICPC ta gabatar da takardar da babban asibitin na kasa ya bayar wadda ta tabbatar da cewa Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bai ma taba zuwa Asibitin dan a duba lafiyarsa ba.
Da wannan ne kotun tace ba zata bayar da belinsa ba akan cewa wai bashi da lafiya.
Saidai kotun tace ICPC kada ta hana Likitansa ya rika dubashi san...
An ga masoyan dan kwallon kafa na kasar Portugal, Cristiano Ronaldo sun taru a kofar otal din da ya sauka a Toronto kasar Canada.
Da yawa sun rika daga wayoyinsu suna kiran sunansa inda ya daga hannu ya gaishesu.
https://twitter.com/i/status/2072541688610890232
Idan an jima ne dai kasar Portugal zata buga wasa tsakaninta da kasar Croatia.
A yayin da kwanakin da suka gabata aka ga Cristiano Ronaldo ana masa binciken Kwakwaf a kasar Amurka inda ake buga gasar World Cup.
Shima Messi an hangoshi ana masa irin wannan bincike, lamarin dai ya dauki hankula sosai.
https://twitter.com/i/status/2072557812115186106
Wannan wata matashiyace data zargi kishiyar mahaifiyarta da cewa, tana kaita wajan maza.
Yarinyar tace daga Karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina ta taso.
Tace ana dora mata talla amma ita bata son yin tallar.
Ta kara da cewa, amma bata taba yadda mazan su yi komai da ita ba duk wajan da kishiryar mahaifiyar tata ke kaita.
https://www.tiktok.com/@haseem_media/video/7657501459885477138?_r=1&_t=ZS-97hBpXiicWf
Rahotanni a kafafen sada zumunta na ta yawo cewa, wasu mafusatan matasa sun yiwa Tauraron fina-finan Hausa, Lawal Ahmad Na jaki.
Rahoton yace ya ji jiki sosai yana can ma kwance a Asibiti.
Saidai zuwa yanzu Lawal Ahmad bai fito ya tabbatar ko karyata wannan rahoton ba.
https://www.tiktok.com/@yusufmusazango/video/7657504212607143175?_r=1&_t=ZS-97h2ky7D8KL
https://www.tiktok.com/@ahmadnakowamhd/video/7657612364518378759?_r=1&_t=ZS-97h384CwysW
Tauraron fina-finan Hausa, Tijjani Asase yayi murnar cika shekaru 14 da aure.
Ya wallafa Bidiyon sa shi da matarsa suna shaukin Juna.
https://www.tiktok.com/@real_kanabaro/video/7657628113634856212?_r=1&_t=ZS-97h1hzdVm56