Friday, January 9
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Allah Sarki: A yau, Lahadi ne za’a yi jana’izar Abokan Dan Damben, Anthony Joshua su 2 a masallacin Birnin Landan

Allah Sarki: A yau, Lahadi ne za’a yi jana’izar Abokan Dan Damben, Anthony Joshua su 2 a masallacin Birnin Landan

Duk Labarai
Rahotanni sun ce a yau Lahadi, 4, ga watan Janairu na shakerar 2026 ne za'a yi jana'izar abokan dan Damben Najeriya, Anthony Joshua 2 da suka rasu a hadarin mota da ya rutsa dasu a Najeriya. Za'a yi jana'izar ne a masallacin Landan. Hakan zai baiwa 'yan Uwa da abokan arziki damar halartar sallar Jana'izar tasu a yau. Rahotanni sun ce Anthony Joshua ya koma Landan din.
Kada ADC su yadda Kwankwaso ya koma cikinsu, Ina zargin Tinubu zaiwa aiki>>Inji Chinonso Charles

Kada ADC su yadda Kwankwaso ya koma cikinsu, Ina zargin Tinubu zaiwa aiki>>Inji Chinonso Charles

Duk Labarai
Wani Inyamuri me suna Chinonso ya yi kira ga jam'iyyar ADC cewa, kada su amince da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso inda yace yana zargin zai je jam'iyyar ne dan yawa Tinubu aiki. Ya bayyana cewa shi ko fadan Kwankwaso da Abba yana ganin shiri ne kawai. https://twitter.com/i/status/2007561248528052420 Jaridar Thisday tace ana tattaunawa tsakanin Kwankwaso da jam'iyyar ADC inda yake shirin komawa can yayin da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ke shirin komawa APC. Hakanan shima a jawabinsa, Kwankwaso yace akwai jam'iyyar da suke tattaunawa da ita yake son komawa amma kuma yana son a bashi takarar shugaban kasa ko ta mataimakin shugaban kasa. j
Duk da yawan Gwamnonin da ka tara ba zaka kai labari ba a 2027>>Kwankwaso ya gayawa Shugaba Tinubu

Duk da yawan Gwamnonin da ka tara ba zaka kai labari ba a 2027>>Kwankwaso ya gayawa Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyanawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu cewa, duk da yawan Gwamnonin da ya tara, ba zai yi nasara ba a zaben shekarar 2027 me zuwa. Ya bayyana hakane a wajan taron da aka yi a gidansa dake Kano. Kwankwaso yace ba tara Gwamnoni tsaffi ko sabbi da Ministoci bane nasara, yace nasara itace a farantawa Talaka. https://twitter.com/i/status/2007568487409938766
Da Duminsa: Kwankwaso ya bayyana matakin da zasu dauka akan Abba idan ya koma APC

Da Duminsa: Kwankwaso ya bayyana matakin da zasu dauka akan Abba idan ya koma APC

Duk Labarai
Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana matakin da zasu dauka akan Abba idan ya koma jam'iyyar APC. Ya bayyana cewa wadanda suka baiwa Abba shawarar komawa jam'iyyar APC, ya kamata su kuma bashi shawarar ajiye mukamin gwamna tunda a jam'iyyar NNPP ya sameshi. Kwankwaso yace ji yake kamar a mafarki yake game da maganar komawar Abba jam'iyyar APC. Ya kuma karyata rade-radin da ake cewa wai hada baki suka yi da Abba.
”Yan Kudu da yawa na cewa wai tsoron kasar Amurka yasa Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya goge duk wata suka da yawa kasar Amurka a kafafen sada zumunta

”Yan Kudu da yawa na cewa wai tsoron kasar Amurka yasa Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya goge duk wata suka da yawa kasar Amurka a kafafen sada zumunta

Duk Labarai
'Yan kudu da yawa ne ke ta yayata cewa wai Malamin Addinin Islama, Dr. Ahmad Gumi ya gog duk wani rubutu da yayi na sukar shugaban kasar Amurka. A cewarsu hakan na zuwane bayan matakij da shugaban Amurka, Donald Trump ya dauka akan kasar Venezuela. Sun bayyana cewa, wai tsoro ne ya kama malamin.
An zargi Bukola Saraki da Munafurci inda yake nuna yana PDP amma yana zagayawa ya ga Shugaba Tinubu

An zargi Bukola Saraki da Munafurci inda yake nuna yana PDP amma yana zagayawa ya ga Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Jam'iyyar APC a jihar Kwara ta zargi tsohon kakakin majalisar Dattijai, Bukola Saraki da cewa, yana Adawa a jihar Ta Kwara amma yana zagayawa ya rika ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Me magana da yawun jam'iyyar APC na jihar Kwara, Abdulwaheed Babatunde ne ya bayyana hakan, inda yace ya kamata Bukola Saraki ya fito ya gayawa mabiyansa bangaren da yake. Yace a Kwara sai ya nuna shi dan PDP ne amma sai ya rika zuwa Abuja yana ganawa da shugaba Tinubu.
Kalli Bidiyon: Kwankwaso ya bayyana cewa suna magana da wata jam’iyyar da yake son komawa amma ya saka musu sharadin sai sun bashi takarar shugaban kasa ko ta mataimakin shugaban kasa

Kalli Bidiyon: Kwankwaso ya bayyana cewa suna magana da wata jam’iyyar da yake son komawa amma ya saka musu sharadin sai sun bashi takarar shugaban kasa ko ta mataimakin shugaban kasa

Duk Labarai
Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, suna magana da wata jam'iyya inda yace zai koma cikinta. Yace amma ya saka musu sharadin sai in sun yadda zasu bashi takarar shugaban kasa ko ta mataimakin shugaban kasa. Ya bayyana hakane a wajan taron da aka yi a gidansa na 'yan Kwankwasiyya a Kano. Saidai bai bayyana sunan jam'iyyar ba. https://twitter.com/i/status/2007548263520669734 A baya dai, Hutudole ya ruwaito muku da Thisday cewa, jam'iyyar ADC ce Kwankwaso ke shirin komawa.