Friday, February 13
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon: Samha M. Inuwa ta fito ta bayar da hakuri kan Bidiyon da ta yi wanda bai dace ba ya kuma dauki hankula

Kalli Bidiyon: Samha M. Inuwa ta fito ta bayar da hakuri kan Bidiyon da ta yi wanda bai dace ba ya kuma dauki hankula

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Samha M. Inuwa ta fito ta bayar da hakuri kan Bidiyon ta da aka gani yana ta yawo a kafafen sada zumunta. An dai ga wani Bidiyon ta inda aka ga tana share majina da takardar kudin Naira. Bidiyon ya dauki hankula sosai inda akai ta sharhi akai mutane na bayyana mabanbanta ra'ayoyi Saidai a nata jawabin tace wannan tsohon Bidiyon ne wanda ya kai kusan shekaru 4. Tace kuma ko da a wancan lokacin, tana dora Bidiyon aka kirata aka gaya mata bai dace ba kuma ta hau ta cireshi. Saidai tace har ofishin 'yansanda aka gayyace ta a wancan lokacin kuma an rufe case din. https://www.tiktok.com/@samha_m_inuwa/video/7601916804620897556?_r=1&_t=ZS-93Zzp6XcuNl https://twitter.com/i/status/2018018878945653049
Kalli Bidiyon: An min Alfarma na shiga inda Qabarin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yake>>Inji Tauraron fina-finan Hausa, Ibrahim Shahrukhan

Kalli Bidiyon: An min Alfarma na shiga inda Qabarin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yake>>Inji Tauraron fina-finan Hausa, Ibrahim Shahrukhan

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Ibrahim Shahrukhan ya bayyana cewa an masa alfarma ya shiga inda qabarin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)yake. Ya bayyana cewa ba kowa ake bari ya shiga wajan ba amma shi an masa Alfarma ya shiga. An ganshi cikin hawaye yanawa Manzon Allah SAW, Sallama. https://www.tiktok.com/@mc_mal_ibrahim_sharukhan/video/7602002782253583636?_r=1&_t=ZS-93ZySd60PTd
Kalli Bidiyon:Gfresh Al-Amin ya saki matarsa, Binta Suga

Kalli Bidiyon:Gfresh Al-Amin ya saki matarsa, Binta Suga

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya saki matarsa, wadda yakewa Lakabi da Binta Suga. Na kusa da Gfresh dinne aka ji suna ta yada maganar sakin inda wasu kuma ke ta Allah wadai dashi kan wannan sakin da yayi. Wasu kuma, matan dake yadda su aureshi ne suke zargi. https://www.tiktok.com/@mistinbestie/video/7601956553071070482?_r=1&_t=ZS-93ZxOEvu5E8 https://www.tiktok.com/@mairoo46/video/7601829355421109524?_r=1&_t=ZS-93Zxjr0n2IL https://www.tiktok.com/@meenal.arabian.scent/video/7601842751738481941?_r=1&_t=ZS-93ZxsE41LgO
Kalli Bidiyon: Tun shekarar farko ta Mulki Abba suka fara samun matsala da Kwankwaso>>Inji Sanat Rufai Hanga

Kalli Bidiyon: Tun shekarar farko ta Mulki Abba suka fara samun matsala da Kwankwaso>>Inji Sanat Rufai Hanga

Duk Labarai
Sanata Rufai Hanga ya bayyana cewa rashin jituwar dake tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta fara ne tun shekarar farko da fara Mulkin Abba. Yace a wancan lokacin Sanata Kwankwaso ya so ganin Abba amma Abban yaki zuwa shi kuma idan ya ce zai je wajan Abban sai Abban yaki yadda ya ganshi. Yace Sanata Kwankwaso ya gaya masa cewa, Lamarin ya dameshi saboda yanda yake ganin dansa Mustapha haka yake kallon Abba inda yace yana tunanin wani abu akawa Abba dan wannan ba Abban da ya sani bane. Sanata Rufai yace Kwankwaso ya nemi a saka Gwamna Abba a addu'a inda daga baya suka samu ganawa. https://twitter.com/i/status/2018096318753775892
Allah Sarki Kalli Bidiyon: Asalin dan mutuminnan da akewa laqabi da Sarkin Qarya ya fito yace dan Allah a daina ce masa Yarima

Allah Sarki Kalli Bidiyon: Asalin dan mutuminnan da akewa laqabi da Sarkin Qarya ya fito yace dan Allah a daina ce masa Yarima

Duk Labarai
Asalin dan mutuminnan da akewa Laqabi da Sarkin Qarya, ya fito yace wani da ya bayyana tun farko yace shine dan mahaifin nasu har ana tara masa kudi ba gaskiya bane. Yace su basu ma sanshi ba suma a kafafen yada labarai suke ganinsa. Ya kara da cewa, yana rokon mutane su daina ce masa Yarima. https://www.tiktok.com/@official.abdul297/video/7601483441531522325?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7601483441531522325&source=h5_m&timestamp=1769935696&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_i...
Kalli Bidiyon hira da matarnan da ake zargin ta kori mahaifiyarta daga gidanta saboda mahaifiyar ta kasa biyan kudin haya

Kalli Bidiyon hira da matarnan da ake zargin ta kori mahaifiyarta daga gidanta saboda mahaifiyar ta kasa biyan kudin haya

Duk Labarai
Matar nan 'yar garin Daura da ake zargin ta kori mahaifiyarta daga gidanta sabida mahaifiyar ta kasa biyan kudin haya ta fito ta kare kanta. Tace itama kamar yanda aka gani, haka taga lamarin a kafafen sada zumunta. Tace mijin mahaifiyarta ne ke son sai ta sayar masa da gidan wanda gado ne da mahaifinta ya bar mata amma taki amincewa, tace tana tunanin yana da hannu game da abinda ke faruwa. https://twitter.com/i/status/2017523186250690887 Wasu da a baya suka yi sharhi me kaushi akan matar sun fito sun bata hakuri. https://www.tiktok.com/@prettyme_barrister/video/7601657152842763528?_r=1&_t=ZS-93YNAAnTn5V