Sunday, December 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ji yanda matar aure a Arewa ta yi yaji saboda Mijinta yana bata Dubu dari a wata a matsayin kudin Cefane,tace sun yi kadan

Ji yanda matar aure a Arewa ta yi yaji saboda Mijinta yana bata Dubu dari a wata a matsayin kudin Cefane,tace sun yi kadan

Duk Labarai
Wata matar aure a Arewa ta yi yaji saboda tace mijinta yana cutar da ita saboda 'ya'yansu 2 amma sai ya rika bata kudin cefanane Tace yana ajiye kayan abinci kamar buhun shinkafa da man girki, amma sai ya bata Naira 100,000 wanda baya isanta yon cefane. Akan hakane suka yi fada ta tafi gidansu. https://twitter.com/_hafsat_paki/status/1977371222385029269?t=NsYHM3ZBZ_rvBAvum_wEbQ&s=19
Wannan wani Gawurtaccen Me Shatar mutanene dan neman kudin fansa wanda yana cikin wadanda shugaba Tinubu yawa afuwa

Wannan wani Gawurtaccen Me Shatar mutanene dan neman kudin fansa wanda yana cikin wadanda shugaba Tinubu yawa afuwa

Duk Labarai
Kelvin Oniarah Ezigbe dan shekaru 44 na daga cikin mutanen da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yawa afuwa. Shugaban wasu gungun 'yan fashine dake garkuwa da mutane An zargeshi da hannu a kisan Sojoji da 'yansanda da dama. An yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari saidai saboda nuna nadama da yayi, an rage shekarun zuwa 13.
Da Duminsa: Cutar Shanyewar Rabin jiki ta kama Ministan kudin Najeriya an garzaya dashi asibitin kasar waje

Da Duminsa: Cutar Shanyewar Rabin jiki ta kama Ministan kudin Najeriya an garzaya dashi asibitin kasar waje

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, cutar Shanyewar rabin jiki ta kama Ministan Kudi, Wale Edun inda aka garzaya dashi zuwa asibitin kasar waje Sahara reporters ta bayyana cewa, lamarin yayi tsanani anma yana samun kulawa ta musamman a asibitin da aka kaishi. Rahotan yace ministan yana aiki da yawa ba tare da hutu ko cin abinci yanda ya kamata ba wanda ake ganin hakan ya taimaka sosai wajan rashin lafiyar tasa. Rahoton yace Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Cordoso ne aka wakilta ya maye gurbin ministan zuwa wani babban taron kudi da za'a yi a kasashen waje. Rahoton yace ko da ministan ya warke da wuya ya koma bakin aikinsa inda rahotanni suka ce tuni shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara neman wanda zai nada a matsayin sabon Ministan kudin. rahoton yace fadar shugaban kasa t...
Da Duminsa: Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU ta tsunduma yajin aikin gargadi na sati biyu

Da Duminsa: Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU ta tsunduma yajin aikin gargadi na sati biyu

Duk Labarai
Ƙungiyar malaman jami'a a Najeriya Asuu ta bai wa mambobinta umarnin fara yajin aiki daga gobe Litinin na tsawon mako biyu. Academic Staff Union of Universities (Asuu) ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa'adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata. Shugaban Asuu Farfesa Chris Piwuna ya faɗa yayin taron manema labarai a Abuja cewa matakin ya zama dole "saboda gazawar gwamnatin wajen biyan buƙatunmu".
Da Duminsa: Tinubu zai tafi Italiya yau Lahadi

Da Duminsa: Tinubu zai tafi Italiya yau Lahadi

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tnubu zai kama hanyar zuwa Italiya a yau Lahadi domin halartar taron Aqaba na shugabannin ƙasashe kan tsaro. Fadar shugaban ƙasar ta ce taron Aqaba Process Heads of State and Government Level Meeting zai mayar da hankali kan matsalar tsaro a Afirka ta Yamma. "Za a fara taron ranar 14 ga watan Oktoba, wanda zai haɗa shugabannin ƙasa, da shugabannin soji daga Afirka domin tattauna ƙalubalen tsaro a Afirka ta Yamma," in ji sanarwar da fadar ta fitar ranar Asabar da dare. Sarkin Jordan Abdullah II ne ya ƙaddamar da taron a 2015 domin yaƙi da ta'addanci, wanda Masarautar Jordan da gwamnatin Italiya ke gudanarwa, a cewar sanarwar. "Shugaba Tinubu zai tattauna da wasu shugabanni a gefen taron domin lalubo hanyoyin magance matsalar tsaro a yankin," kamar yadda fa...
A shirye nake in auri Maryam Sanda bayan da shugaba Tinubu ya mata Afuwa>>Inji Matashi, Sarki

A shirye nake in auri Maryam Sanda bayan da shugaba Tinubu ya mata Afuwa>>Inji Matashi, Sarki

Duk Labarai
Matashi me amfani da sunan Sarki a X ya bayyana cewa, a shirye yake ya auri Maryam Sanda a matsayin mace ta biyu. Ya bayyana hakane bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mata afuwa. Maryam Sanda dai ta kashe mijinta ne wanda dalilin haka kotu ta yanke mata hukuncin kisa. Saidai a cikin jerin wadanda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya wa Afuwa an ga sunan Maryam Sanda. Wasu dai sun alakanta wannan afuwa da cewa kudi ne suka sa aka mata inda wasu ke cewa, Hanya ce.
Kalli Bidiyon: Mafi yawancin matan aure yanzu duk Qaruwaine, kuma suna shaye-shaye, saidai ni na yi sa’a ban taba kama matata da Qwarto ba>>Inji Gfresh

Kalli Bidiyon: Mafi yawancin matan aure yanzu duk Qaruwaine, kuma suna shaye-shaye, saidai ni na yi sa’a ban taba kama matata da Qwarto ba>>Inji Gfresh

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa a duk cikin matan da ya aura babu wadda yafi jin dadin zama da ita da nutsuwa kamar ta yanzu, 'yar Yola. Gfresh yace Mafi yawancin matan aure yanzu Qaruwaine, aure baya hanasu neman maza. hakanaan yace kuma suna shaye-shayen miyagun Kwayoyi. https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7560075106840546568?_t=ZS-90U32qmFGNs&_r=1
Kalli Bidiyon: Ban ce Ahlussunah basa son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba, cewa nayi ‘yan Dariqa sun fi Ahlussunah na yanzu son Annabi, kuma ina nan akan bakana>>Inji Sheikh Nura Khalid

Kalli Bidiyon: Ban ce Ahlussunah basa son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba, cewa nayi ‘yan Dariqa sun fi Ahlussunah na yanzu son Annabi, kuma ina nan akan bakana>>Inji Sheikh Nura Khalid

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid, Wanda aka fi sani da Digital Imam ya bayyana cewa, bai ce 'yan Izala basa son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba. Abinda ya fada shine 'yan Darika sun fi son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam). Yace dalilinsa kuwa shine su sufaye sun ce duk Hadisin da ya kawo aibu ga Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) basa neman ingancinsa ko rashin ingancinsa, basu yadda dashi bane. Hakanan duk Hadisin da ya kawo Yabo ga Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) suna yadda dashi ba tare da neman inganci ko rashin inganci ba. Yace su kuma Ahlussunah na yanzu suna neman Hadisai da suka aibata Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ne suna karantar da mutane. Malam yace to a tsakaninsu waye yafi son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)? https://www.tiktok....