Saturday, December 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Hoto Yanda Likitoci suka cire Chokula 29 da Burosh din wanke baki guda 19 daga cikin wani mutum

Kalli Hoto Yanda Likitoci suka cire Chokula 29 da Burosh din wanke baki guda 19 daga cikin wani mutum

Duk Labarai
Likitoci a asibitin Devnandani Hospital, Hapur, dake kasar India sun ciro abubuwa 50 da wani mutum dan shekaru 40 ya hadiya daga cikinsa. Likitocin sun kwashe awanni 5 suna wannan aiki, kamar yanda rahotanni suka bayyana. Ranar 17 ga watan Satumba aka kaishi asibiti yana aman jini inda aka mai Scanning aka ga Cokulan karfe 29 da burosh 19 da kuma biro guda 2. Lamarin ya baiwa likitocin mamaki. Shugaban Likitocin da suka yi wannan aiki, Dr. Shyam Kumar ya bayyana cewa, bai taba ganin irin wannan abubuwan a cikin mutum daya ba. Ya kara da cewa an babballa abubuwan kamin mutumin ya hadiyesu. Mutumin ya aikata hakanne bayan da aka kaishi wani gidan horo da baya so. Rahoton yace yana samun sauki bayan da aka masa aiki.
Ganin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu sanye da Agogon Naira Miliyan dari da goma ya jawo cece-kuce

Ganin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu sanye da Agogon Naira Miliyan dari da goma ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
Wani me suna UptownofLagos a X ya wallafa farashin agogon da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu le sanye da ita. Agogon dai kamar yanda ya wallafa ana sayar da itane akan Ndata $53,290, wanda hakan kwatankwacin Naira Miliyan 110,000,000. Lamarin dai ya jawo zazzafar Muhawara inda wasu ke cewa ya kai ya saka wannan agogo da kudinsa wasu kuma na sukar hakan. https://twitter.com/Uptownoflagos/status/1973860433376522361?t=dwylhwCJ-dJLbaFsO08Lcw&s=19
Shugaba Tinibu zai tabbatar zaben 2027 ya zama sahihi>>Inji Kakakin majalisar Dattijai, Tajudeen Abbas

Shugaba Tinibu zai tabbatar zaben 2027 ya zama sahihi>>Inji Kakakin majalisar Dattijai, Tajudeen Abbas

Duk Labarai
Kakakin majalisar Dattijai, Tajudeen Abbas ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai tabbatar da zaben Shekarar 2027 ya zama Sahihi. Ya bayyana hakane a yayin ganawa da wasu turawa ranar Alhamis. Yace majalisar tarayya na kan gyaran dokar zabe dan tabbatar da sahihancin zaben me zuwa. Yace sun hada kai da majalisar Dattijai dan ganin ba'a samu banbancik ra'ayi ba game da gyaran dokar zaben.
An kama Sanata Elisha Abbo saboda zargin Aikata Alfasha da wata me kananan shekaru

An kama Sanata Elisha Abbo saboda zargin Aikata Alfasha da wata me kananan shekaru

Duk Labarai
Hukumomin 'yansanda sun kama sanata Elisha Abbo Saboda zargin aikatawa wata yarinya Fyade. Rahoton yace Tsohon sanatan wanda ya wakilci Adamawa ta Arewa ya mika kansa wajan 'yansanda a Abuja bayan da aka zargeshi da yiwa yarinya me shekaru 13 fyade. Iyayen yarinyar sun yi zargin cewa, sanata Senator Aishatu Dahiru Ahmed (Binani) ta je har gidansu inda ta rokesu da kada su fitar da maganar. Hakanan shima sanata Elisha Abbo ya rika aikawamahaifin yarinyar kudade da shirin kulle musu baki. Dan Rajin kare hakkin bil'adama kuma Lauya, Deji Adesogan ne ya bayyana hakan sannan yace har yanzu sanata Elisha Abbo na daure a hannun 'yansanda. Wannan dai ba shine karin farko da Sanata Elisha Abbo ya shiga karma-karma ba, a baya ya taba cin zarafin wata mata a ofishin sayar da kayan biya...
Bansan wace irin harka ‘yan Matan Fim din Hausa suke suna samun kudaden sayen mota da gidaje ba amma maganar gaskiya kudin Fim basa sayen irin wannan abubuwa>>Inji Isa Bello Jan

Bansan wace irin harka ‘yan Matan Fim din Hausa suke suna samun kudaden sayen mota da gidaje ba amma maganar gaskiya kudin Fim basa sayen irin wannan abubuwa>>Inji Isa Bello Jan

Duk Labarai
Dajjito a masana'antar fina-finan Hausa, Isa Bello jaa ya bayyana cewa, kudin aikin fim basu kai suka kawo ba a yanda za'a ce mutum har zai iya mallakar wata kadara dasu ba. An tambayeshi ne game da wanda ke sayen gidaje da motoci musamman 'yan mata. Malam Isa yace bai san wace harka suke yi suna samun wadannan kudade ba. Yace amma su masu shirya fim din sukan samu Miliyoyin kudade a matsayin riba saboda kudi suka zuba suka shirya fim din. Kalli Hirar da aka yi dashi a kasa: https://www.tiktok.com/@juicylifestyle7/video/7553410801923558674?_t=ZS-90Dhl1DXO7N&_r=1
Ba gaskiya bane, Ban ce zan janye wa kowa daga takarar shugaban kasa ba>>Atiku Abubakar

Ba gaskiya bane, Ban ce zan janye wa kowa daga takarar shugaban kasa ba>>Atiku Abubakar

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya musanta rahotanni dake yawo cewa wai yace zai janye wa matashi yayi takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC. Atiku ta bakin me magana da yawunsa, Paul Ibe yace wannan magana ba gaskiya bace. Yace a hirar da yayi da BBC babu inda yace zai janyewa wani dan takara, yace abinda ya fada shine idan aka yi zaben fidda gwani kuma matashi yayi nasara a zaben zai goya masa baya. Atiku yayi kira ga 'yan Jarida su daina fassara labari ba yanda ya kamata ba.