Wani magidanci ya kama matarsa da kwarto akan gadonsu yayin da yake live chat da diyarsa.
A Bidiyon da ya dauki hankula a kafafen sadarwa, an ga Mutumin yana magana da diyarsa inda ya tambayeta ina mahaifiyarta?
Tace tana daki ita da wani.
Shine yace mata ta je dakin yagani, ai kuwa tana zuwa sai ga mahaifiyarta da mutumin akan gadon.
https://www.tiktok.com/@cardinaljeff2/video/7637156996478799126?_r=1&_t=ZS-96vnYo5SAmT
Wasu mutanen daji da suka dauki wasu dattawa 2 suka kuma fitar da Bidiyon su suna rokon a karbosu sun dauki hankula.
Da yawa dai sun bayyana alhini inda suka wa dattawan fatan Allah ya kubutar dasu.
Bayan fitar Bidiyon, an gano daya daga cikin mutanen dake hannun mutanen dajin shugaban jam'iyyar APC ne a garin koko dake karamar hukumar Besse ta jihar Kebbi.
https://www.tiktok.com/@chimebukafoundation123/video/7647473633614482708?_r=1&_t=ZS-96vkOkX1Bm1
Malamin Addinin Islama, Sheikh Abdulrazaq Yahya Haifan ya bayyana cewa indai mutum na da tumbi to basirarsa bata da yawa, inji ibn Hajar.
Hakanan yace Imamushshafi'i ya bayyana cewa bai taba ganin mutum kato me hankali ba.
Saidai ya bayyana wasu kalilan inda yace akan samu jefi-jefi.
https://www.tiktok.com/@sheikh_haifan1/video/7646926880167283976?_r=1&_t=ZS-96vjEYmZl6y
Bidiyon Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf yana raba kwanuka ya karade kafafen sada zumunta.
An yi zargin yana raba kwanukanne a matsayin tallafi ga wadanda yake baiwa wanda hakan ya jawo cece-kuce sosai ake cewa akwai rashin kyautawa game da hakan.
Saidai cikakken Bidiyon ya bayyana inda aka ganshi ashe yana basu kwanukanne su je a zuba musu Abinci.
https://twitter.com/i/status/2062102904178098580
Matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta rabawa mata shuwagabannin jam'iyyar APC na jihohi sabbin Motoci.
Lamarin ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta inda da yawa ke cewa hakan bai dace ba.
https://twitter.com/i/status/2062415104616861876
Gwamnatin jihar Lagos ta sanar da kama mabarata 144 zata mayar dasu zuwa Kano.
Wasu sun jinjinawa wannan mataki inda wasu ke Allah wadai.
https://twitter.com/i/status/2062235006005576136
'
Yar Gwagwarmaya, Aisha Yesufu ta dauki hankula bayan da aka ga wani Bidiyon ta da ta je ofishin jam'iyyar NDC tana musu masifa.
Ta yi hakanne saboda an hanata tikitin tsayawa takarar sanata a Abuja.
A cikin wadanda takewa jarabar, Hadda shugaban jam'iyyar, Seriake Dickson.
https://twitter.com/i/status/2062235953578520695
An hangi Gwamnan jihar Naija, Umar Bago yana wake-wake irin na Kiristoci a coci wanda ya jawo cece-kuce.
Da yawa dai sun yi Allah wadai da lamarin musamman ganin cewa Gwamnan Musulmi ne.
https://www.tiktok.com/@gospelgurus/video/7646883525374856455?_r=1&_t=ZS-96uVxRB8MtR
Bidiyon update na tsohuwar Tauraruwar BBNaija, Angel ya bayyana.
An ga Bidiyon nata a kafafen sada zumunta yana yawo inda da yawa suka bayyana rashin jin dadi musamman masoyanta na gaskiya.
Ba zamu iya nuna Bidiyon anan ba saboda muninsa.