Saturday, December 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Shugaban bankin Access Bank ya sayi gidan Dala Miliyan $20 a Landan

Shugaban bankin Access Bank ya sayi gidan Dala Miliyan $20 a Landan

Duk Labarai
Shugaban bankin Access Bank, Roosevelt Ogbonna ya sayi gidan dala Miliyan $20 a Landan. !Ya sayi gidanne a unguwar masu kudi da ake cewa, Billionaires’ Row kamar yanda kafar Bloomberg ta ruwaito. Rahotan yace da farko kudin gidan sun fi haka amma daga baya aka masa sauki ya kuma saya. Wannan gida da ya siya yana daga cikin ciniki masu tsada da aka yi a Landan wanda ya dauki hankula.
‘Yan darika Taron Yuyu ne, Duk Kano, babu Majalisin da ya kai na Gadon kaya cika, Dan haka Me Girma Gwamnan Kano kada ka yadda su ce maka bamu da yawa>>Inji Malam Kan neman da ake Gwamnatin Kano ta dauki mataki kan Malam Lawal Triumph

Malam yace ba gaskiya bane Abinda ake gayawa Gwamnan Kano cewa 'yan Izala basu da yawa a jihar. Yace sun sha hawa mumbari suna neman a baiwa Gwamna Abba Kujerarsa saboda shine yaci zabe. Yace kuma duk Kano babu majalisin dake cika kamar na gadon Kaya. Dan haka ya yi kira ga gwamna cewa, ya sa ma ransa mulki Allah ne ke bayarwa. https://www.tiktok.com/@ali_d_abba/video/7555267558375492886?_t=ZS-90BvDpfxs0X&_r=1
Kalli Bidiyo: Idan dai kai Kirista ne na gaskiya, Bai kamata a ganka da Guru ko laya ba, sannan bai kamata kana zuwa gurin Boka ba>>Inji Wannan Faston

Kalli Bidiyo: Idan dai kai Kirista ne na gaskiya, Bai kamata a ganka da Guru ko laya ba, sannan bai kamata kana zuwa gurin Boka ba>>Inji Wannan Faston

Duk Labarai
Wannan Wani Fasto ne da ya dauki hankula sosai bayan da yayi wa'azin cewa Kirista na Gari baya zuwa wajan Boka ko daura laya ko Guru. Wasu sun rika ce masa Fasto dan Izala inda wasu suka rika ce masa, Allah yasa ya musulunta. https://www.tiktok.com/@ndbcvihausa/video/7555449846900116743?_t=ZS-90BuSukkwiH&_r=1
Kalli Bidiyon yanda Hassan Make-Up ya kama Otal din Miliyan 3 da rabi a Makkah inda yaje aikin Umrah

Kalli Bidiyon yanda Hassan Make-Up ya kama Otal din Miliyan 3 da rabi a Makkah inda yaje aikin Umrah

Duk Labarai
Tauraron Tiktok Hassan Make-Up yana kasar Saudiyya inda yake aikin Umrah. An ga yanda ya kamata otal dake kusa da dakin Ka'aba wanda aka bayyana da cewa ana biyan Naira Miliyan 3.5 kudin Najeriya. Wata kawarsa data kai masa ziyara ce ta bayyana hakan. https://www.tiktok.com/@fanneshuwa15/video/7555282877152283922?_t=ZS-90BtjuQylBh&_r=1
Da Duminsa: Gwamnatin Jihar Kano ta dauki mataki akan Malam Lawal Triumph, saidai bai yiwa dalibansa dadi ba

Da Duminsa: Gwamnatin Jihar Kano ta dauki mataki akan Malam Lawal Triumph, saidai bai yiwa dalibansa dadi ba

Duk Labarai
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga yon wa'azi Majalisar Shura da gwamnatin Kano ta kafa ta sanar da dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa'azi. A wani taron manema labarai da Sakataren majalisar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi a yau Laraba, ya ce an dakatar da Malam Lawan ne domin bashi damar ya zo gaban majalisar ya kare kan sa daga zarge-zargen da ake yi masa na yin kalaman ɓatanci ga Ma'aiki. A cewar Sagagi, an dakatar da Malam Lawan har sai an kammala bincike da jin ta bakin sa a matakin Majalisar ta shura. Ya kuma yi kira ga ƴan siyasa da su guji tsoma baki a batun, inda ya bukaci da a kyale kwamitin ya kammala aikin sa. Sagagi ya tabbatar da cewa Majalisar za ta yi aiki tsakani da Allah ba tare da son rai ko rashin adalci ba...
Kalli Bidiyo:Jama’ar Katsina ku yi Hakuri, kamin in hau mulki na yi Alkawarin duk wata zan rika bada bayanin yawan kudaden da muka samu da yawan wanda muka kashe, amma yanzu da na zama Gwamnan naga abin ba zai yiyu ba>>Inji Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya baiwa al'ummar Jihar Hakuri inda yace kamin ya hau mulki yayi Alkawarin rika bayar da ba'asi kan yawan kudaden da aka samu da wanda aka kashe. Yace amma bayan da ya hau yaga abin ba mai yiyuwa bane. Gwamnan yace dalili kuwa shine Wasu kudaden idan aka karbosu kudin aikin gwamnatin data wucene za'a biya, hakanan wasu kudaden kuma aikin da aka yi shekarar data wucene za'a biya dasu. A karshe dai yace shima dan Adam ne dan haka yana neman Afuwa. Kalli Bidiyon jawabinsa a kasa; https://www.tiktok.com/@mps_mediang/video/7553746884012035346?_t=ZS-90BqPMn9FZ3&_r=1
Mun samar da tsaro sosai a Yankin Arewa, yanzu mutanen da a baya suka tsere daga gidajensu, sun koma garuruwansu>>Inji Shugaba Tinubu

Mun samar da tsaro sosai a Yankin Arewa, yanzu mutanen da a baya suka tsere daga gidajensu, sun koma garuruwansu>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, jami'an tsaro sun samar da tsaro sosai a yankin Arewa maso gabas da Arewa maso yamma. Yace Mutanen da a baya suka tsere daga gidajensu saboda matsalolin tsaro a yanzu sun koma gidajen nasu. Shugaban yace an samu nasarori sosai a yaki da masu dauke da makamai a sassa daban-daban na kasarnan. Shugaban ya bayyana hakane yayin da yake jawabin ranar cikar Najeriya shekaru 65 da samun 'yanci. https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1973276459851718762?t=kes68RdXaxTNIpxXB9Z7OQ&s=19
Kalli Bidiyo: Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce Kwamishinan ‘yansandan Kanon ya basu kunya kuma suna Allah wadai da abinda yayi na kin Halartar Bikin ‘yancin Najeriya

Kalli Bidiyo: Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce Kwamishinan ‘yansandan Kanon ya basu kunya kuma suna Allah wadai da abinda yayi na kin Halartar Bikin ‘yancin Najeriya

Duk Labarai
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi Allah wadai da kwamishinan 'yansandan jihar, Inda yace ya basu kunya saboda kin halartar bikin ranar 'yancin Najeriya. Gwamna Abba yace Kwamishinan ya dauki matakai da suka nuna cewa yana goyon bayan wata jam'iyya. Gwamnan yace shine Gwamna sannan shugaban tsaro na jihar Kano kuma Allah ne ya bashi, dan haka babu wanda ya isa ya kwace mai. Gwamnan yayi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya cire Kwamishinan 'yansandan daga jihar Kano na kawo musu wani. Kalli Jawabin Gwamnan a kasa: https://www.tiktok.com/@sardauna_shoot.ng/video/7556210141406711048?_t=ZS-90BmkqFaY76&_r=1
Daga yau, 1 ga watan Oktoba, hukumar shige da fici ta Najeriya zata fara kama ‘yan kasar waje dake zaune a Najeriya ba bisa ka’ida ba, ko wadanda suka shigo Najeriya ba tare da takardu ba

Daga yau, 1 ga watan Oktoba, hukumar shige da fici ta Najeriya zata fara kama ‘yan kasar waje dake zaune a Najeriya ba bisa ka’ida ba, ko wadanda suka shigo Najeriya ba tare da takardu ba

Duk Labarai
Rahotanni sun ce daga yau, 1 ga watan Oktoba, Hukumar kula da shige da fici ta Najeriya zasu fara kame da hukunta wadanda suka shigo Najeriya bizarsu ta kare basu fita ba da wadanda kuma suna shigo ba tare da takardu ba. Wadanda aka kama da laifi, zasu iya fuskantar hukuncin mayar dasu kasashensu ko kuma cinsu tara. Wanda aka kama ya dade a Najeriya tsawon watanni 3 bayan shigowa kuma takardunsa sun kare, zai biya tarar Dala $15 kullun. Ko kuma a bashi zabin hanashi shigowa Najeriya na tsawon shekaru 2. Sai kuma wadanda suka tsaya a Najeriya na tsawon watanni 3 zuwa shekara 1, su kuma za'a musu hukuncin biyan tarar dala $15 kullun ko kuma hanasu shigowa Najeriya na tsawon shekaru 5.