Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Hukumar ‘yansandan farin kaya DSS ta bukaci kafar X ta goge shafin Sowore saboda zarginsa da batawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu suna

Hukumar ‘yansandan farin kaya DSS ta bukaci kafar X ta goge shafin Sowore saboda zarginsa da batawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu suna

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan farin kaya, DSS ta bukaci kafar sada zumunta ta X wadda aka fi sani da Twitter data goge shafin mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore. Hukumar ta wallafa bukatar hakanne a shafinta na X din inda take zargin Sowore da yada labaran karya da kuma kawo barazanar tsaro saboda wallafa cewa shugaba Tinubu yace ya magance matsalar rashawa da cin hanci a Najeriya amma kuma ba haka bane. DSS sun ce sun baiwa kafar ta X awanni 24 su goge shafin na Sowore ko kuma su dauki matakin da ya dace akan kafar. DSS sun ce wannan ikirari na Sowore ya jawo har zanga-zanga an yi wanda hakan yake barazana ga zaman lafiya a Najeriya. Dan haka sukace Sowore da kafar data bashi dama ya wallafa irin wannan labari na iya fuskantar hukunci.
Kalli Bidiyon yanda dan majalisar tarayya, Abdulmumin Jibrin yayi murna bayan da jam’iyyar NNPP ta dakatar dashi

Kalli Bidiyon yanda dan majalisar tarayya, Abdulmumin Jibrin yayi murna bayan da jam’iyyar NNPP ta dakatar dashi

Duk Labarai
Dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin, Kofa kenan a wannan Bidiyon inda yake murna hadda yadda hula bayan da jam'iyyar NNPP ta dakatar dashi. Dan majalisar yayi hakanne bayan karbar takardar dakatar dashi da jam'iyyar ta NNPP ta yi. https://twitter.com/tudunwada__mi/status/1964437184141992043?t=c6EAKvwTSZ2DZvozphs8Ew&s=19
Na fita daga Jam’iyyar NNPP>>Inji Abdulmumi Jibrin bayan da NNPP din ta koreshi

Na fita daga Jam’iyyar NNPP>>Inji Abdulmumi Jibrin bayan da NNPP din ta koreshi

Duk Labarai
Dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji a majalisar wakilai, Abdulmumi Jibrin ya sanar da ficewarsa daga Jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano, inda ya ce ya amince da matakin korarsa da jam'iyyar ta yi. Jibrin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar, inda a ciki ya bayyana cewa bai cancanci kora daga jam'iyyar ba, ba tare an ba shi damar kare kansa ba. Tun da farko, jam'iyyar ce ta sanar da cewa ta kore shi bisa zarginsa da karya dokokinta. Ya ce, "na yi mamakin ganin an kore ni daga NNPP. Na yi amannar cewa tattaunar da na yi ba su yi nauyin da za su ja min kora ba," in shi, inda ya "ban janye komai ba a cikin abin da na fada." Ya ce ba a gayyace shi ba domin ya kare kansa kan abin da ake zarginsa da aikatawa, "ko a mulkin soja, ana ba wanda ake zargi dama ya kar...
Kalli Bidiyo: Ni Har Ka’aba an je an tsine min Albarka kuma babu abinda ya sameni, dan haka masu kusheni saboda an daukeni hoto da Wayar dubu 13 babu abinda zai sameni>>Inii Gfresh Al-amin

Kalli Bidiyo: Ni Har Ka’aba an je an tsine min Albarka kuma babu abinda ya sameni, dan haka masu kusheni saboda an daukeni hoto da Wayar dubu 13 babu abinda zai sameni>>Inii Gfresh Al-amin

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa, har Dakin Allah, Ka'aba an je an tsine masa dan haka babu abinda zai sameshi. Ya bayyana hakane a sabon Bidiyon da ya saki inda yake mayar da martani game da hotunanda da aka dauka a wajan wani biki daya halarta. An ga Gfresh da kuraje cike da fuskarsa, ba kamar yanda aka saba ganinsa fuska fresh ba kamar ta jarirai a Bidiyonsa. Gfresh yace an mamayesu shi da Murja Kunya an yi amfani da wayoyi masu arha aka daukesu hotuna, yace dan haka shi ya fara tunanin kara tsaro a kusa dashi. Yace kuma babu abinda zai sameshi dan mai abinda yafi haka bai kunyata ba. https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7545934313934605575?_t=ZS-8zWMycKyQbJ&_r=1 https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7546308686071745799?_t=ZS-8zWNVcH6...
Ƴansanda a Kano sun kama mutane 9 bayan rykycyn

Ƴansanda a Kano sun kama mutane 9 bayan rykycyn

Duk Labarai
Ƴansanda a Kano sun kama mutane 9 bayan rikicin da ya faru kan zargin kisan kai a Garko. Rundunar ’Yansanda ta Jihar Kano ta ce ta kama mutane tara da ake zargi da hannu a tashin hankali da ya faru a karamar hukumar Garko bayan wani lamari na kisan kai. A cewar sanarwar da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, lamarin ya faru ne a ranar 4 ga Satumba, 2025, lokacin da jami’an 'yansandan, shiyyar Wudil su ka kama wasu mutane uku da ake zargi da kisan kai, sannan aka kai su caji-ofis na Garko domin bincike. Sai dai a ranar 5 ga Satumba, jama’a dauke da sanduna da duwatsu suka farmaki ofishin, suna zanga-zangar mutuwar wanda aka kashe, tare da kokarin kashe wadanda ake tsare da su. Harin ya jawo konewar motar sintirin ’yansanda, lalata motoci uku na...
Gwamna Zulum zai bai wa ɗalibai da iyayensu kuɗaɗe don ƙarfafa gwiwa

Gwamna Zulum zai bai wa ɗalibai da iyayensu kuɗaɗe don ƙarfafa gwiwa

Duk Labarai
Gwamnan jihar Borno a arewacin Najeriya, Babagana Zulum, ya amince da bai wa iyaye maza N250,000 da iyaye mata N50,000 na ɗalibai 90 a garin Gajiganna da ke jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin da yake ƙaddamar da makarantar Islamiyya ta Higher Islamic College Gajiganna, inda ya yi alƙawarin ciyar da ɗaliban kyauta a kullum. "Za mu bai wa kowane uba N250,000, da kowace uwa N50,000. Kowane ɗalibi kuma zai samu N50,000 domin biyan buƙatunsa," in ji wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar. Ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakin ne domin ƙarfafa wa iyaye gwiwa wajen kai yaransu makarantar da ke arewacin Borno, yankin da yaƙin Boko Haram ya ɗaiɗaita. Gajiganna mai mutane kimanin 50,000, ɗalibai 90 ne kacal ke zuwa makaranta a garin, a cewar Gwamna Zulum. "Dole ne mu...
NNPP ta kori Abdulmumin Kofa daga jam’iyyar

NNPP ta kori Abdulmumin Kofa daga jam’iyyar

Duk Labarai
Jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano ta kori ɗanmajalisar tarayya Abdulmumin Jibrin Kofa daga jam'iyyar tana mai zargin sa da cin amanarta. Shugaban jam'iyyar na Kano, Hashim Dungurawa ya faɗa wa BBC cewa sun kori ɗanmajalisar mai wailtar mazaɓar Kiru da Bebeji saboda dalilai na cin amana da kuma tallan wani ɗantakara. "Mun same shi da cin amanar jam'iyya a matakai daban-daban," in ji Dungurawa. "Na farko, mun same shi da tallata ɗantakarar shugaban ƙasa na wata jam'iya da ba namu ba. "Na biyu, ya ce zai iya fita daga jam'iyyar. Wannan ba ƙaramin cin amana ba ne. Na uku, ba ya biyan kuɗin haraji na jam'iyya, duk da cewa akwai doka cewa duk wata akwai abin da zai bayar domin cigaban jam'iyyar. "Na huɗu, ba ya zuwa mazaɓarsa. 'Yan mazaɓarsa kan yi kusan wata biyar ba su ji ɗuriya...