Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya dawo Najeriya daga Landan a jiya Laraba.
Tsohon gwamnan jihar Kanon ya tafi ƙasar Birtaniya domin neman magani jim kaɗan bayan murabus ɗinsa daga shuagabancin jam'iyya mai mulki a ƙasar.
Da ya ke tabbatar da wannan batu ga jaridar The PUNCH, tsohon shugaban ma’aikatansa, Mohammed Garba, ya ce Ganduje ya sauka a Nijeriya ne a safiyar jiya Laraba bayan shafe kusan wata guda a waje.
“Eh, ya dawo Najeriya yau. Ya dawo cikin koshin lafiya, kuma ya ƙarasa gidansa,” in ji Garba, yayin da ya ke tabbatar wa da jaridar PUNCH.
Ya ƙara da cewa Ganduje ya bar Najeriya zuwa Landan ne kwana biyar bayan ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar domin neman lafiya.
Shugaban APC na farko, Bisi Akande ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan Buhari a Kaduna
Shugaban jam'iyyar APC na farko kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Cif Bisi Akande ya jagoranci tawagar ƴansiyasa zuwa ta'aziyyar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Shafin Z na BBC ya rawaito cewa tawogar ta kai ziyarar ce gidan marigayin a jihar Kaduna ranar Laraba, inda Akande ya kwatanta shi da shugaba na gari wanda tarihi ba zai taɓa mantawa da shi ba saboda kyayawan ayyuka da ya yi a ƙasar.
Matar marigayin ne Aisha Buhari da kuma ɗansa Yusuf Buhari ne suka tarbi tawagar ƴansiyasar.
Akande ya nuna kaɗuwarsa kan mutuwar tsohon shugaban ƙasar, inda ya ce lokaci na karshe da suka haɗu shi ne lokacin da ya kai masa ziyara a Daura.
DA ƊUMI-ƊUMI: Asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya ya ƙaru a karo na farko tun 2021.
A wani rahoto da Babban Bankin Ƙasa, CBN, ya fitar a ranar 19 ga watan Agusta, asusun na ƙasar wajen ya ƙaru zuwa Dalar Amurka Biliyan 41.
A cewar CBN, rabon da asusun ya ƙaru irin haka, tun ranar 3 ga watan Disamba, 2021.
Sanata Ahmed Wadada, mai wakiltar Nasarawa ta Yamma, ya fice daga jam’iyyar SDP.
Murabus ɗin nasa ya fito ne a cikin wata wasika da ya aika wa shugaban jam’iyyar na gundumar Tudun Kofa, ƙaramar hukumar Keffi, Jihar Nasarawa.
"Ina mai rubuta wannan wasiƙa ne don sanar da ku shawarar da na ɗauka ta ficewa daga kasancewa ɗan jam’iyyar SDP, daga yau nan take. Wannan shawara ba a ɗauke ta da sauƙi ba, amma na ji tilas in ɗauki wannan mataki saboda rikice-rikicen cikin gida da suka dade suna addabar jam’iyyarmu,” in ji shi.
Ya ce rikice-rikicen cikin gida sun jawo rabuwar kai sosai da kuma shari’o’i a tsakanin jam’iyyar.
Wadada ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi a lokacin da yake memba, tare da bayyana farin cikinsa kan gogewa da alaƙar da ya samu.
Sai dai, sanatan bai b...
INDA RANKA: Matashi Ya Sadaukar Da Soyayyar Budurwarsa ta Shekaru 8 Akan Sabon LIFAN Da 200k
Kamar Yadda Muka Samu Rahoto Wani Attajiri ne ya nuna bukatar matashin Yabar masa budurwarsa da suke soyayya domin ya aure ta, inda yanajin tayin attajirin matashin baiyi wata-wata ba ya karba, yayi bakwana da Ita nan take.
Shin kuma zaku iya Hakan?
Malamin Dariqa, Abdulfathi Sani ya bayyana cewa, har yanzu ana wahayi.
Malamin ya bayyana hakane a Bidiyon martanin da yawa Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Malam yace Ko gobe za'a iya yin Wahayi.
Gwamnan Jihar Naija, Umar Bago ya bayyana cewa, Babu Wahala a jihar Naija.
Yace farashin kayan abinci sun saika, Ana noma sosai sannan yana gina tituna.
Da aka tambayeshi kan Sauran jihohin Arewa dake kuka da tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu, sai yace babu jihar da Tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu ba su kai ci gaba ba.
https://www.tiktok.com/@madubitv2790/video/7540384826646334725?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7540384826646334725&source=h5_m×tamp=1755785973&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7510...
Gidajen man fetur din Najeriya irin su AA Rano, Total, Mobil, NIPCO duk sun rage farashin man fetur dinsu dan yin gasa da kamfanin man fetur na kasa, NNPCL da sauransu.
Saidai ragin ya farune a Abuja da kewaye kadai.
Gidajen man fetur din AA Rano, Ranoil, Mobil, da NIPCO sun rage farashin man su zuwa Naira 890 akan kowace lita maimakon Naira 945.
Suma gidajen man fetur din Empire Energy, Emadab, da Total duk sun rage farashin man fetur dinsu inda wasu ke sayarwa akan naira 899 wasu kuma 910 akan kowace lita a Abuja.
Shugaban kungiyar 'yan kasuwar, Abubakar Maigandi ya bayyana cewa sun rage farashinne saboda faduwar farashin danyen man fetur da kuma raguwar farashin man a inda suke sarowa.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, Najeriya zata fara fitar da man fetur zuwa kasashen waje.
Karamin ministan man fetur, Dr Heineken Lokpobiri ne ya bayyana hakan a wajan taron ma'aikatan man fetur da aka gudanar.
Yace duk da kalubalen da Najeriya ke fuskanta wajan wadata cikin gida da Man fetur, kasar zata kuma kaiwa kasashen Afrika ta yamma man fetur din.