Yadda Ta Kaya Tsakanina Da Shugaban Hukumar EFCC A Yayin Bada Belina -Aminu Tambuwal.
"A Lokacin Da Lauyoyina Suka Je Wajen Shugaban EFCC Domin Neman A Bada Ni Beli, Ya Ce Sai Na Kawo Wadanda Za Su Taaya Min. Na Ce Su Koma Su Gaya Masa Na Taɓa Zama Kakakin Majalisa, Na Yi Wa’adin Gwamna Har Sau Biyu, Kuma Yanzu Ina Majalisar Dattawa. Don Haka Ina Iya Tsayawa Kaina Domin Belin Kaina", Cewar Aminu Waziri Tambuwal
Daga Jamilu Sani RarahSokoto
Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu ta bayyana cewa, shi dai wanda tace bata taba haduwa dashi ba ya sai mata Motar GLK da bude mata babban shago, haka yace ta tashi daga Otal ta nemo gida kalar wanda take so ya siya mata.
Rahama tace bata jin dadin irin yanda ake cewa wai kanta ta bayar aka bata morlta.
https://www.tiktok.com/@juicylifestyle7/video/7538206815054597382?_t=ZS-8yscCkazHbl&_r=1
Malamin Addinin Islama, Baffa Hotoro yace yawanci 'yan mata da basu jin magana da kuma karuwai da muryar Sheikh Salihu Zaria suke amfani a Tiktok.
Malamin yace da Sheikh Salihu Zaria zai daina wa'azi da matsalar Tiktok ta kau.
Yace kuma irin su Sheikh Salihu Zaria ne wai ke kare Izalar Jos.
Kalli Bidiyonsa a kasa:
https://www.tiktok.com/@jrbunza/video/7537643442587864325?_t=ZS-8ysb98Oa6r2&_r=1
Kungiyar Kwadago NLC ta bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta gaggauta biya mata bukatunta nan da kwanaki 7 ko kuma ta tsunduma yajin aiki.
Kungiyar ta bukaci gyaran Fansho ne da kuma zargin karkatar da wasu kudaden ma'aikata.
Hakan na kunshene a cikin sanarwar da shugaban kungiyar Joe Ajaero ya sakawa hannu.
Yace idan gwamnati bata biya musu bukata ba nan da kwanaki 7 akwai yiyuwar su shiga yajin aiki
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya bayyana cewa, da Najeriya zata samu shuwagabanni 2 kamar Bola Ahmad Tinubu da ta zama kasar Amurka wajan ci gaba.
Ya bayyana hakane ranar Laraba a wajan wani taron yakin zaben cike gurbi.
Ya kawo canje-canje irin su gyaran haraji da sauransu wanda yace tsari ne wanda ya kawowa kasarnan Ci gaba
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya sanar da tafiya hutun mako uku don kula da lafiyarsa.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Salisu Zango ya fitar, ya ce gwamnan zai fara hutun ne daga ranar Litinin, 18 ga watan Agustan 2025.
“Cikin matakan da nake ɗauka don kula da lafiyata da kuma ganin na yi aiki cikin yanayi mai kyau, na ɗauki wannan matakin tafiya hutu, kuma zan dawo da zarar likitoci sun gama duba ni,'' in ji Gwamna Radda.
Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Malam Faruk Jobe.
A watan Yuli ne gwamna Radda ya yi hatsarin mota a kan hanyar Katsina zuwa Daura.
Yanzu tattalin arzikin Najeriya ya dai-dai ta ƙarkashin Tinubu - Okonjo-Iweala.
Darakta-Janar ta Hukumar kula da kasuwanci ta duniya WTO Dakta Ngozi Okonjo-Iweala a ranar Alhamis ta gana da shugaban ƙasa Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa, inda ta yabawa gwamnatin Tinubu kan canje-canje da tayi domin dai-dai ta tattalin arzikin Najeriya.
Okonjo-Iweala wadda ta bayyana ganawar da tayi a matsayin abinda taji daɗi, tace Shugaban Ƙasa ya nuna ya na son zantawa da'ita bayan tabi Uwargidan sa wajen ƙaddamar da kuɗaɗe ga mata.
Kuɗaɗen wanda Hukumar kula da kasuwanci WTO da cibiyar kula da kasuwanci ta duniya ITC da ke Geneva suka samar, nada nufin haɓɓaka kasuwanci da samar da ayyukan yi da samar da kuɗaɗen shiga ga mata.
Daga Usman Salisu
Rahotanni sun bayyana cewa, jam'iyyar ADC na shirin ja da baya kan shirinta na kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 me zuwa.
Hakan na zuwane bayan da jam'iyyar ta gano cewa, Gwamnatin tarayya ta tura mata munafukai a cikinta da su rika kai mata bayanan sirri.
Hakannan wannan na zuwane jim kadan bayan binciken da EFCC tawa Sanata Aminu Waziri Tambuwal wnda ake rade-radin zai wa wani da zai fito takarar shugaban kasa daga kudu mataimakin shugaban kasa .
Dan majalisar tarayya daga jihar Jigawa, Hon. Ibrahim Usman Auyo ya yi zargin cewa sai sun biya tsakanin Naira Miliyan 1 zuwa 3 sannan ake yadda su gabatar da kudirin doka a majalisar tarayya har a karantashi a zauren majalisar.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta.
Ya kara da cewa, bayan haka sai mutum ya bi 'yan majalisar yana rokonsu akan su goyi bayan kudirin nasa.
Yace dan haka maganar gabatar da kudirin doka a majalisar ya zama hanyar samun kudi.