Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Yawanci ‘ya’yan fari a Najeriya ‘ya’yan shegu ne, ba ‘ya’yan halas bane>>Inji Binciken Smart DNA Nigeria

Yawanci ‘ya’yan fari a Najeriya ‘ya’yan shegu ne, ba ‘ya’yan halas bane>>Inji Binciken Smart DNA Nigeria

Duk Labarai
Babbar cibiyar binciken kwayoyin halitta na DNA me sunan Smart DNA Nigeria ta bayyana cewa yawan ma'aurata masu neman a musu binciken kwayoyin halitta da 'ya'yansu na karuwa. Cibiyar tace a shekarar 2025 an samu karuwar yin binciken kwayoyin halittar DNA da kaso 13.1 cikin 100. Hakan na kunshene a cikin bayanin da kungiyar ta fitar wanda ya kunshi bayanan data tattara daga watan July 2024 zuwa June 2025. Kafar tace wani abin damuwa shine yawanci musaman 'ya'ya maza na fari da mata ke haifa ba mazajen ne iyayensu ba, daga waje suke shiga da cikin. Rahoton yace kaso 65 na maza 'yan fari 'ya'yan shegu ne a Najeriya yayin da suma mata 'ya'yan fari yawanci ba 'ya'yan halas bane kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito. Saidai rahoton yace yawanci masu yin g...
Albashin sanatocin Najeriya su 109 zai iya biyan Albashin Farfesoshi 4,708, Kowane sanata yana karbar Naira Miliyan 21.6 duk wata, yayin da kowane Farfesa kuma ke karbar Naira 500,000 duk wata

Albashin sanatocin Najeriya su 109 zai iya biyan Albashin Farfesoshi 4,708, Kowane sanata yana karbar Naira Miliyan 21.6 duk wata, yayin da kowane Farfesa kuma ke karbar Naira 500,000 duk wata

Duk Labarai
Rahoto yace Jimullar kudin da ake baiwa Sanatocin Najeriya 109 a duk wata da suka kai 2.354 sun isa a biya albashin farfesoshi 4,708. Kudin da ake biyan sanatocin ba albashine kadai ba, hadda kudin kula da ofisoshinsu da na kula da mazabunsu. An dade ana mahawara akan albashin 'yan majalisa da malaman makaranta, Musamman Farfesoshi. A kwanannan aka ga Professor Nasir Hassan-Wagini na jami'ar Umaru Musa Yar’adua University, Katsina yana sayar da kayan miya inda yace yana yi ne dan taimakon kansa. Matsakaicin Albashin Farfesa Naira 500,000 ne a yayin da Sanatoci ke karbar Naira Miliyan 21.6 duk wata. A shekarar data gabata, BBCHausa ta yi hira da Senator Kawu Sumaila wanda yace duk wata Naira Miliyan 21.6 ake biyansu. A hirarsa da Daily Trust, Farfesa Dr Niyi Sunmonu na jam...
Ɗan Majalisar Taraiya na Fagge, MB Shehu ya saya wa mabuƙacin tsoho injin facin da ya roƙa a wani faifen bidiyo

Ɗan Majalisar Taraiya na Fagge, MB Shehu ya saya wa mabuƙacin tsoho injin facin da ya roƙa a wani faifen bidiyo

Duk Labarai
Ɗan Majalisar Taraiya na Fagge, MB Shehu ya saya wa mabuƙacin tsoho injin facin da ya roƙa a wani faifen bidiyo. Ɗan Majalisar Wakilai, mai wakiltar mazaɓar ƙaramar hukumar Fagge, Muhammad Bello Shehu, ya sayi wa injin faci ga wani tsoho da ke buƙatar injin. DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito cewa a makon da ya gabata ne faifen bidiyon tsohon, mai suna Ali Abdulrahman, wanda aka fi sani da Ali Mai Faransawa, ya karade kafafen sadarwa, inda ya ke korafin cewa ya shafe shekaru ya na tafiyar Kwankwasiyya amma bai taɓa samun wani tagomashi ba. A cewar Ali Mai Faransawa, wani kansila a Fagge ya yi masa alƙawarin haɗa shi da shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge domin a saya masa injin faci, amma abun ya ci tura. Bidiyon ta sa, wacce gidan rediyon Express FM ya wallafa a shafin sa na fa...
Kalli: Zanen Tattoo da Rahama Saidu ta yi akan kirjinta ya jawo cece-kuce

Kalli: Zanen Tattoo da Rahama Saidu ta yi akan kirjinta ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
Zanen Tattoo da Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu ta yi akan Kirjinta ya jawo cece-kuce sosai. Tun a kwanakin baya aka ga Rahama Kwance ana mata zanen a kirjinta wanda ya jawo cece-kuce sosau. Saidai a yanzu bayan data saki wasu sabbin hotuna, an kuma ganin Tattoo din ya fito sosai fiye da da. Hakan yasa da yawa suka rika tambayar shin me zanen yake nufi dan kuwa da Yarbanci ta rubutashi. Wasu masu fassara dai sun bayyana cewa, zanen na kirjinta na nufin Allah Dukiya.
Kalli Bidiyon yanda aka kai Adam A. Zango dakin Amaryarsa

Kalli Bidiyon yanda aka kai Adam A. Zango dakin Amaryarsa

Duk Labarai
A jiyane aka daura auren Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango da Amaryarsa, Maimuna Musa. Bidiyo ya bayyana inda aka ga yanda aka kaishi dakin amaryarsa. Tuni 'yan Uwa da abokan Arziki suka rika taya Adam A. Zango murnar aurensa. Amarya Maimuna dai ta yi fatan Allah yasa mutuwa ce zata rabata da gidan mijinta. https://www.tiktok.com/@sagir_producer/video/7531874147463482630?_t=ZS-8yyOLukQRHs&_r=1
Da Duminsa: Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya kara aure, ‘Yar Kannywood ce ya aura, Ji bayani game da fina-finan da ta yi da sanda aka daura auren

Da Duminsa: Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya kara aure, ‘Yar Kannywood ce ya aura, Ji bayani game da fina-finan da ta yi da sanda aka daura auren

Duk Labarai
Rahotanni da Hutudole ke samu na cewa, Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya kara aure. Rahotannin sun ce Adam A. Zango ya auri Salamatu wadda aka fi sani da Maimuna Musa ta Garwashi. Sannan kuma itace ta fito Zaituna a Labarina. Hutudole ya samu labari cewa an daura aurenne a ranar Lahadi, 17 ga watan Augusta. Tuni dai 'yan Uwa da abokan arziki suka fara taya su Murna.
Kalli Bidiyo Da Duminsa: A karshe dai an bayyana ainahin Mijin Rahama Sadau, bama dan Najeriya bane

Kalli Bidiyo Da Duminsa: A karshe dai an bayyana ainahin Mijin Rahama Sadau, bama dan Najeriya bane

Duk Labarai
Daya daga cikin wadanda ake bayyana cewa sune suka auri Rahama Sadau me suna Abdullahi Aliyu ya fito ya bayyana cewa bashine mijin Rahama ba. Yace tabbas suna da alaka me kyau tsakaninsa da Rahama Sadau. Saidai yace bashine ya aureta ba dan hotunansu da ake yadawa sun kai kusan shekaru 6 da dauka ba sabbin hotuna bane. Ya kara da cewa, Mijin Rahama Sadau ba dan Najeriya bane, dan kasar Chinane. Kuma nan gaba kadan za'a ganshi. Kalli Bidiyon anan
Da Duminsa: Jam’iyyar NNPP ta Lashe zaben cike gurbi na Bagwai da Shanono

Da Duminsa: Jam’iyyar NNPP ta Lashe zaben cike gurbi na Bagwai da Shanono

Duk Labarai
Jam'iyyar NNPP ta Lashe zaben cike gurbi na Bagwai da Shanono da aka gudanar jiya, Asabar a Kano. Da yake bayyana sakamakon zaben da misalin karfe  12:36am na safe, Professor Hassan Shitu ya bayyana dan takarar NNPP, Dr Ali Kiyawa a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 16,198 inda ya kayar da dan takarar APC, Ahmad Kadamu, da ya samu kuri'u 5,347. 'Yan Jam'iyyar NNPP sun gudanar da zaman dirshan a ofishin INEC inda suka zargi cewa, ana shirin yin murdiyar zabe a sakamakon mazabar Ghari/Tsanyawa. Kakakin Gwamnatin jihar Kano, Sanusi Tofa yace ba zasu bar kofar INEC din ba sai an fadi sakamakon Ghari/Tsanyawa
EFCC ta kwato Naira Biliyan 5 da dala Miliyan $10 daga hannun barayin tsaffin ma’aikatan NNPCL

EFCC ta kwato Naira Biliyan 5 da dala Miliyan $10 daga hannun barayin tsaffin ma’aikatan NNPCL

Duk Labarai
Hukumar hana rashawa da cin hanci, EFCC ta kwato Naira Biliyan 5 da Dala Miliyan $10 daga hannun tsaffin ma'aikatan NNPCL da 'yan Kwangila. Wadannan kudade na da alaka da gyaran matatun man Kaduna, Fatakwal, da Warri. Hakanan kuma Punchng tace ta samu karin bayanin cewa, EFCC din na kokarin kara kwato wasu Naira Biliyan 10 da wasu dala Miliyan $13 da suma aka karkatar dasu. Rahoton yace shugaban EFCC, Ola Olukoyede da kansa ne ke jagorantar wannan bincike musamman ganin yanda aka kashe makudan kudade wajan gyaran matatun man Najeriya amma har yanzu basa aiki. Gwamnatoci da suka shude sun yi kokarin gyaran matatun man fetur din amma basu yi nasara ba.