Thursday, December 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyo: Matashi Garba Maiwada ya zargi Gwamna Zulum da yin dama-dama da Maiduguri ta yanda matasa sai tafiya ci rani suke saboda ba aikin yi a garin

Kalli Bidiyo: Matashi Garba Maiwada ya zargi Gwamna Zulum da yin dama-dama da Maiduguri ta yanda matasa sai tafiya ci rani suke saboda ba aikin yi a garin

Duk Labarai
Matashi Garba Maiwada ya gayawa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum cewa, sun yi dama-dama da garin Maiduguri ta yanda garin a yanzu babu aikin yi. Matashin yace amma na kusa da gwamnan basa gaya masa gaskiya Matashin yace ba zasu zabi wani ba wai dan Gwamna Zulum yace a zabeshi, yace ko da kuwa Gwamna Zulum dinne a yanzu ya dawo ba zasu sake zabenshi ba. https://www.tiktok.com/@garbamaidawa/video/7536889948037795128?_t=ZS-8yq7YYqADTN&_r=1
Kalli Bidiyo: Mutane basa yawo shiyasa suke mamaki dan nace an bani kwangilar Biliyan 4 suna ganin karyane, Ni kuma ina yawo, ba kasuwancin da bana yi kuma yanzu haka an sake bani gidajen Naira Biliyan 5 in sayar>>Mansurah Isa

Kalli Bidiyo: Mutane basa yawo shiyasa suke mamaki dan nace an bani kwangilar Biliyan 4 suna ganin karyane, Ni kuma ina yawo, ba kasuwancin da bana yi kuma yanzu haka an sake bani gidajen Naira Biliyan 5 in sayar>>Mansurah Isa

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta bayyana cewa, mutane na mamakin tace an bata kwangilar Naira Biliyan 4. Tace abinda da yawa basu fahimta ba shine, ba wai Biliyan 4 tsabar kudi ake magana ba, ana maganar a rubucene. Tace idan tsabar kudi ake magana, ko Dangote da me kudin Duniya, Elon Musk basu taba ganin Biliyan 4 a zahiri ba duk yawanci a takarda ne. Tace kuma matsalar mutane basa yawo ne shiyasa, tace amma ita tana yawo kuma ita 'yar kasuwa ce dan haka ko a yanzu ma an bata gidajen Naira Biliyan 5 ta sayar a Abuja. https://www.tiktok.com/@nassxee_hausa_tv/video/7536705865944993080?_t=ZS-8ypznj1pQCf&_r=1
Kotu ta cewa Gwamnatin tarayya ta kawo karshen Shari’ar Dasuki

Kotu ta cewa Gwamnatin tarayya ta kawo karshen Shari’ar Dasuki

Duk Labarai
Kotu ta ba gwamnatin tarayya wa’adin Satumba kan shari’ar Dasuki. Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin zuwa ranakun 24, 25 da 26 ga watan Satumba domin kammala shari’ar tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro , Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya), kan zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da badakalar kudi. Mai shari’a Peter Lifu ya umurci gwamnati ta kammala kiran shaidu da gabatar da dukkan shaidun da za ta dogara da su a shari’ar da ta fara tun 2015. A zaman baya, kotu ta karbi kayayyakin da aka samo daga gidajen Dasuki a Abuja da Sokoto a matsayin shaida, ciki har da kwamfuta, wayoyi, kudi da takardun banki. An dage shari’ar zuwa Satumba domin gwamnati ta rufe gabatar da shaidu sannan Dasuki ya fara kare kansa....
Kalli Bidiyo: Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) baya cutarwa baya amfanarwa, yana Kabari, Kuma duk me neman ya bashi wani abu ba zai samu ba, ka nema a wajan Allah>>Inji Malam Abdurrahman Umar

Kalli Bidiyo: Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) baya cutarwa baya amfanarwa, yana Kabari, Kuma duk me neman ya bashi wani abu ba zai samu ba, ka nema a wajan Allah>>Inji Malam Abdurrahman Umar

Duk Labarai
Malam Abdurrahman Umar ya gargadi masu neman wani abu a wajan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa, zasu mutu basu samu ba dan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yana kabari, baya cutarwa baya amfanarwa. Ya bayyana hakane a wani wa'azinsa daya yadu sosai. Yace Suffar Allah ce ake jinginawa ga Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) https://www.tiktok.com/@abdurrahmanumarr/video/7537055471803403576?_t=ZS-8ypuAvQiki1&_r=1
Wata Sabuwa: Bayan Sakin Tambuwal EFCC na shirin kama shugaban ADC, David Mark

Wata Sabuwa: Bayan Sakin Tambuwal EFCC na shirin kama shugaban ADC, David Mark

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar EFCC na shirin kama shugaban jam'iyyar ADC, David Marka da kuma tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha. Jam'iyyar ADC ce ta bayyana hakan ta bakin kakakinta, Bolaji Abdullahi. Jam'iyyar tace me yasa sai 'yan ADC ne kadai ake wa irin wannan bincike kuma me yasa Misali David Marka da ya bar shugabancin majalisar dattijai kusan shekaru 10 da suka gabata, sai yanzu ne za'a fara bincikensa? ADC ta zargi EFCC da kawar da kai akan 'yan jam'iyyar APC bata bincikensu. Hakan na zuwane bayan sakin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da EFCC din ta yi bayan kamashi.
Matatar man fetur ta Dangote ta rage farashin man fetur dinta da Naira 30

Matatar man fetur ta Dangote ta rage farashin man fetur dinta da Naira 30

Duk Labarai
Matatar man fetur din Dangote ta sanar da rage farashin man fetur dinta da Naira 30.. Me kula da harkar sadarwa na matatar, Anthony Chiejina ne ya bayyana hakan inda yace ragin farashin zai fara aiki ne nan take. Yanzu za'a rika sayen man fetur din akan naira 820 maimakon 850 da ake sayarwa a baua. Matatar tace zata ci gaba da samar da wadataccen man a duka fadin Najeriya
Kalli Bidiyo: Ban yadda ba, Kyamarar BBCHausa ta mayar min da matata tsohuwa>>Inji Gfresh Al-amin

Kalli Bidiyo: Ban yadda ba, Kyamarar BBCHausa ta mayar min da matata tsohuwa>>Inji Gfresh Al-amin

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa bai amince da irin daukar da akawa matarshi ba a yayin hirarsu da BBChausa. Gfresh yace kyamarar BBChausa ta mayar da matarsa tsohuwa. Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Tiktok. Gfresh yace matarsa matashiya ce kuma kyakkyawa kuma bai taba auren mata ko yin Budurwa data kai ta kyau da kuruciya ba
Yan sanda sun gargaɗi yara lanana masu tuƙa Adaidaita Sahu a Kano

Yan sanda sun gargaɗi yara lanana masu tuƙa Adaidaita Sahu a Kano

Duk Labarai
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi gargaɗi game da yadda yara ƙanana ke tuƙa babur mai ƙafa uku da aka fi sani da Adaidaita Sahu a birnin Kano. Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Litinin ta bayyana damuwa kan yadda ƙaruwar yara ƙananan da ke tuƙa babur mai kafa ukun ke jefa rayukan mutanen jihar cikin haɗari. Sanarwar ta ce a cikin watan Agustan nan kaɗai, an samu manyan haɗurra 16 sanadiyyar tuƙin da yaran suke yi, lamarin da yayi sanadin jikkatar mutane da dama da kuma asarar dukiya mai yawa. ‘Yan sandan sun gargaɗi jama’a da su riƙa bin ƙa’idojin tuƙi tare yin biyayya a duk lokacin da fitilar kan hanya ta nuna a tsaya ko a tafi. Rundunar ƴan sandan ta kuma ce ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kamawa da hukunta duk wanda aka samu da karya dokokin don tabbatar da ...
EFCC ta saki Tambuwal bayan tsare shi na kwana guda

EFCC ta saki Tambuwal bayan tsare shi na kwana guda

Duk Labarai
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC ta saki tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal. Wasu makusantan Sanatan ne suka tabbatar wa BBC sakin nasa, kuma yanzu haka yana gidansa na Abuja. A ranar Litinin ne hukumar ta tsare shi a Abuja, bayan amsa gayyata kan zarge-zargen fitar da maƙudan kuɗaɗe da suka kai Naira biliyan 189. Kamun da aka yi masa ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar, musamman tsakanin ƴan hamayya, waɗanda ke zargin hakan na da alaƙa da rawar da yake takawa a tafiyar ƴan jama'iyyar haɗaka ta ADC.