Kalli bidiyon yanda sojoji suka je ofishin NEPA suka kwashe ma’aikatan zuwa barikinsu bayan da aka yanke musu wutar Lantarki
Rahotanni daga legas na cewa, hukumar sojojin sama sun kai farmaki ofishin hukumar wuta ta jihar, Ikeja Electric inda suka ci zarafin ma'aikatan hukumar ciki hadda shugabar ma'aikatar.
Lamarin ya farune bayan da Hukumar sojin sama dake barikin Sam Ethan Base aka dauke musu wuta saboda kasa biyan bashin sa ake binsu.
https://www.tiktok.com/@emmax.media/video/7478644385446415638?_t=ZM-8uTjgNbH846&_r=1
Bidiyo da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta ya nuna yanda sojojin suka ci zarafin wasu ma'aikatan hukumar.
Shugabar ma'aikatar, Folake Soeten tace sun kamata sun kulleta a cikin but din mota a yayin cin zarafin.
Saidai hukumar sojin saman na kokarin cewa bata san wane sojoji ne suka je suka aikata wannan lamari ba.
https://www.tiktok.com/@emmax.media/video/747864...








