Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur a Abuja da Legas kadai

Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur a Abuja da Legas kadai

Duk Labarai
Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur dinsa a Abuja da Legas zuwa Naira 875 da kuma Naira 900. Hakan na zuwane kwanaki bayan da NNPCL din ya kara farashin zuwa Naira N915 da kuma Naira N955. Saidai a ranar Laraba, kafar TheCable ta ruwaito cewa, ta lura kamfanin ya rage farashin zuwa Naira 40 akan kowacce lita. A legas, Farashin ya ragu zuwa N875, sannan a Abuja farashin aguwa yayi zuwa N900. Saidai rahoton yace Dangote da Mobil da AP duka basu rage farashinsu ba yana nan a Naira 915 kan kowace lita.
Ba zamu zabi Peter Obi a matsayin shugaban kasa ba saboda giya zai ta kawowa Arewa>>Inji wani Jigo a APC

Ba zamu zabi Peter Obi a matsayin shugaban kasa ba saboda giya zai ta kawowa Arewa>>Inji wani Jigo a APC

Duk Labarai
Saboda Zai Sa A Shigo Da Giya Arewa, Don Haka Ba Za Mu Zabi Peter Obi Ba — Jigo a Jam’iyyar APC Wani jigo daga yankin Arewa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Alwan Hassan, ya bayyana cewa Arewa ba za ta kada kuri’a ga Peter Obi a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 ba, saboda yadda ake alakanta shi da kasuwancin shigo da giya. Yayin da yake jawabi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Talata, Hassan ya caccaki Obi bisa yadda ya yaba da kamfanin giya a jihar Anambra da kuma rawar da yake takawa a harkar shigo da barasa. "Wa kuke tsammani zai kayar da Asiwaju a 2027? Obi wanda a shirin nan yana rokon goyon bayan Arewa, amma a lokaci guda yana murnar girman kamfanin giya a jiharsa kuma yana da hannu a shigo da barasa mafi yawa," in ji shi. "Yanzu ...
Kalli Hoto: Ganin Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai tsaye shi kadai a filin jirgi, babu ‘yan rakiya babu jami’an tsaro yasa wasu suke cewa, mulki baya dawwama

Kalli Hoto: Ganin Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai tsaye shi kadai a filin jirgi, babu ‘yan rakiya babu jami’an tsaro yasa wasu suke cewa, mulki baya dawwama

Duk Labarai
Wani Hoton Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a tsaye a filin jirgin sama ya dauki hankula. An ga El-Rufai tsaye shi kadai babu 'yan rakiya babu jami'an tsaro. Hakan yasa wasu ke cewa, Mulki baya dawwama. https://twitter.com/AbbaM_Abiyos/status/1953032421042987076?t=hvboBBvl1YCPed_ZYvgpug&s=19
Gwamnatin tarayya ta ciwo bashin dala Miliyan 23.35 daga Kuwait dan ta yi maganin matsalar rashin zuwan yara makaranta a jihar Kaduna

Gwamnatin tarayya ta ciwo bashin dala Miliyan 23.35 daga Kuwait dan ta yi maganin matsalar rashin zuwan yara makaranta a jihar Kaduna

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta ciwo bashin Dala Miliyan 23.35 dan magance matsalar rashin zuwan yara makaranta a jihar Kaduna. Gwamnatin ta saka hannu ta karbo bashin a madadin gwamnatin jihar Kaduna wanda wannan na daga shirin ciwo bashin Dala Miliyan  $62.8m dan magance matsalar rashin zuwan yara makaranta a jihar. Daraktan yada labarai na ma'aikatar kudi ta tarayya, Mohammed Manga ya tabbatar da hakan inda yace za'a yi amfani da wannan kudi dan inganta karatun akalla yara 100,000. Sannan za'a yi amfani da kudin wajan gyaran makarantu da sauran abubuwan da suka shafi harkar ilimi a jihar.
Ji irin rawar da mahaifiyar RUKAYYA MUHAMMAD FEMA ta taka wajan nasarar data samu a wajan Muqabala ta Duniya

Ji irin rawar da mahaifiyar RUKAYYA MUHAMMAD FEMA ta taka wajan nasarar data samu a wajan Muqabala ta Duniya

Duk Labarai
Yadda Mahaifiyar Gwarzuwar Muƙabala Ta Duniya Ta Shiga Cikin Tarihi. Hajiya Fatima Umar Mairiga, mahaifiyar gwarzuwar muƙabala ta duniya, RUKAYYA MUHAMMAD FEMA, ta taka gagarumar rawa wajen tabbatar da nasarar diyar ta tun tana ƙarama. Hajiya Fatima ba wai kawai ta tsayu wajen tarbiyya da karfafa gwiwa ba, har ma ta rungumi addu’a a matsayin hanya mafi muhimmanci wajen ganin ɗiyarta ta cimma nasara a rayuwa. Tun tana ƙarama, Rukayya da mahaifiyarta ke tashi cikin dare domin gabatar da Sallar Tahajjud, suna roƙon Allah ya azurta ta da ilimi mai amfani, hikima, da fasaha. Wannan kyakkyawar alaka da Allah da kuma tsantsar jajircewa ya kasance ginshikin nasarar da ta samu. A cikin gagarumar gasa ta duniya – TeenEagle Global Finals 2025 da aka gudanar a birnin London, ƙasar Ingila,...
Shugaba Tinubu Ya Taya Dalibai Uku ‘Yan Arewa Murna Bisa Nasarar Da Suka Samu A Gasar Turanci Ta Duniya (TeenEagle)

Shugaba Tinubu Ya Taya Dalibai Uku ‘Yan Arewa Murna Bisa Nasarar Da Suka Samu A Gasar Turanci Ta Duniya (TeenEagle)

Duk Labarai
Shugaba Tinubu Ya Taya Dalibai Uku ‘Yan Arewa Murna Bisa Nasarar Da Suka Samu A Gasar Turanci Ta Duniya (TeenEagle). Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Nafisa Abdullahi Aminu mai shekaru 17, Rukayya Muhammad Fema mai shekaru 15, da Hadiza Kashim Kalli murna bisa nasarar da suka samu a gasar TeenEagle ta duniya da aka gudanar a birnin London, Ƙasar Ingila. Nafisa ce ta lashe kyautar gwarzon daliba a fannin ƙwarewar harshen Turanci, yayin da Rukayya ta zama ta farko a muhawara, Hadiza kuma ta samu kyautar zinariya a matsayin mai hazaka. Shugaba Tinubu ya jinjinawa waɗannan matasa na Najeriya da suka ɗaga tutar ƙasa a idon duniya, yana mai cewa wannan nasara alama ce ta hasken makomar ƙasar. Ya kuma yaba da irin gudunmawar cibiyoyin ilimi da gwamnatocin jihohi wajen haɓaka ƙwar...
Wannan Bidiyon na Rayya da aka ganta a wani yanayi ya dauki hankula

Wannan Bidiyon na Rayya da aka ganta a wani yanayi ya dauki hankula

Duk Labarai
Bidiyon tauraruwar fina-finan Hausa, Rayya da ya bayyana inda aka ganta sanye da kaya ba dankwali ya dauki hankula a kafafen sadarwa. Wasu dai saboda irin yanda ta bayyana a Bidiyon suna cewa ba ita bace. https://www.tiktok.com/@rayya.official4/video/7533739372231871750?_t=ZS-8yeEUFc4Nur&_r=1 Menene ra'ayinku akai? https://www.tiktok.com/@danmutum.1/video/7535128825768824070?_t=ZS-8yeGBLnRof3&_r=1
Masu son zama shugaban kasa sun yi yawa a ADC>>Inji Sule Lamido

Masu son zama shugaban kasa sun yi yawa a ADC>>Inji Sule Lamido

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Jigawa, Malam Sule Lamido yace masu son zama shugaban kasa, sun yi yawa a jam'iyyar ADC. Sule Lamido ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV. Sule Lamido wanda yana daga cikin wadanda suka halarci taron farko na hadakar 'yan Adawa da suka zabi APC a matsayin jam'iyyar su, yace ba zai bar PDP zuwa karamar jam'iyya ba. Yace yana baiwa masu son shugabanci a jam'iyyar ta ADC dasu natsu su zama cewa sun samu alkibla da hafin kai. Akwai Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi da duka suka bayyana son tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar ta ADC.