Monday, May 12
Shadow

Author: Auwal Abubakar

‘Yansandan Kano sun kama waɗanda ake zargi da garkuwa da mutane

‘Yansandan Kano sun kama waɗanda ake zargi da garkuwa da mutane

Duk Labarai
Rundunar 'yansandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane da take zargi sun shiga jihar ne da nufin yin yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an kama mutanen a garin Kwanar Dangora, kuma yanzu suna hannun 'yansanda, bayan da ya ya ce sun shiga jihar da nufin yin garkuwa da mutane. Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce ''wannan kasuwancin fa na satar mutane ba zai yi tasiri a Jihar Kano ba Insha Allah''. Ya kuma gode wa al'ummar jihar bia addu'o'in da ya ce suna yi a koyause. Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, ba ta cikin jihohin yankin da ke fama da masu garkuwa da mutane, kodayake ana ɗan samu jifa-jifa, amma ba kamar sauran wasu jhohin yankin, da matsalar ta yi ƙa...
Na yi mamakin sauke ni daga muƙamin minista – T Gwarzo

Na yi mamakin sauke ni daga muƙamin minista – T Gwarzo

Duk Labarai
Tsohon ƙaramin ministan gidaje na Najeriya, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce ya yi mamakin sauke shi da a aka yi daga muƙaminsa. Yayin wata hira da BBC kwanaki bayan sauke shi , T Gwarzo ya ce babu wani laifi da ya yi, wanda ya janyo aka sauke shi daga muƙamin nasa, sabod a cewarsa ya yi iya baƙin ƙoƙarinsa a muƙamin da aka ba shi. ''Batun ya zo min da mamaki, domin ba na tunanin wani abu mai kama da wannan zai faru da ni'', in ji shi. Ya ƙara da cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi la'akari da tarayyarsu tun ta da can wajen naɗa shi muƙamin. Ya ce fiye da shekara 14 suna tare da Tinubu tun a jam'iyyar ACN, shi da Nuhu Ribadu da Sanata George Akuwam - da ke riƙe da muƙamin sakataren gwamnati a yanzu. Sai dai ya ce Allah ne ke ba da mulki, kuma ya karɓe a duk lokacin da ya so, ...
Shugaba Tinubu zai tafi Saudi Arabia gobe don taron rikicin Gabas ta Tsakiya

Shugaba Tinubu zai tafi Saudi Arabia gobe don taron rikicin Gabas ta Tsakiya

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, tare da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da wasu ministoci tare da wasu shugabannin hukumomi za su bar Abuja a gobe Lahadi domin halartar taron koli na hadin gwiwa na kasashen Larabawa da Musulmi wanda za a fara ranar Litinin 11 ga watan Nuwamba, 2024, a babban birnin Saudi Arabia, Riyadh. Za a yi taron ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, bayan makamancin taron da aka yi a birnin a bara. Taron zai mayar da hankali ne kan halin da ake ciki yanzu a Gabas ta Tsakiya. Mai bai wa shugaban Najeriya shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, shi ne ya sanar da tafiyar a wata sanarwa da ya sanya wa hannu a yau Asabar. Sanarwar ta ce shugaban zai samu rakiyar mini...
Maiɗakin Tinubu ta musanta cewa za ta jagoranci yi wa ƙasa addu’a

Maiɗakin Tinubu ta musanta cewa za ta jagoranci yi wa ƙasa addu’a

Duk Labarai
Matar shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta musanta rahoton da ke cewa za ta jagoranci taron yi wa ƙasa addu'a saboda tarin matsalolin da Najeriya ke fama da su. A ranar Lahadi da ta wuce wani rahoto da aka fitar ya bayyana cewa matar shugaban ƙasar tare da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu za su jagoranci taron kwana bakwai na yi wa ƙasar addu'a kan halin da take ciki. Rahoton ya bayyana cewa Darakta Janar na Taron yi wa kasa Addu'a, Segun Afolorunikan, shi ne ya yi sanarwar a wani taron manema labarai a Abuja, ranar Lahadi da ta wuce. A waccan sanarwar Afolorunikan ya ce taron wanda aka tsara tare da jagororin addinin Kirista da Musulmi, zai buƙaci Allah Ya shiga al'amarin ƙasar kan matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da kuma tsaro....
Kalli Bidiyo: Wata Sabuwa ana rade-radin wani babban dan siyasar Najeriya dan luwadi ne, ya mayar da martani

Kalli Bidiyo: Wata Sabuwa ana rade-radin wani babban dan siyasar Najeriya dan luwadi ne, ya mayar da martani

Duk Labarai
Shahararren dan din din kudu kuma dan siyasa a jihar Legas, Desmond Elliot wanda aka bayyana cewa dan luwadi ne ya fito ya karyata wannan zargi da akw masa. Shafin Gistlover ne ya wallafa sunayen wasu 'yan Fina-finan kudu inda yace duk 'yan luwadi ne wanda lamarin ya jawo hauragiya a kafafen sada zumunta. Saidai a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na TV, Desmond Elliot ya musanta wannan zargi inda yace wasu ne kawai ke son bata masa suna. Kalli Bidiyon jawabinsa anan Yace yana da abubuwa da yawa da yake mayar da hankali akai fiye da irin wadannan gulmace gulmacen da ake yadawa akansa.
Kasar Iràn na son ta tarwatsa Najeriya>>Inji Kasar Israela

Kasar Iràn na son ta tarwatsa Najeriya>>Inji Kasar Israela

Duk Labarai
Jakadan kasar Israela a Najeriya, Michael Freeman ya bayyana cewa, ba a gabas ta tsakiya ba kadai ayyukan ashsha na kasar Iran suka tsaya ba. Yace ayyukan na kasar Iran sun shigo yankin Africa musamman Najeriya. Ya kara da cewa, kasar ta Iran ce ke son ta tarwatsa Najeriya. Ya bayyana hakane ranar Talata a Abuja wajan hada rahoton cikar harin da kungiyar HAMAS ta kauwa kasar ta Israela na October 7. Mutane 396 ne dai kungiyar ta Hamas ta yi garkuwa dasu bayan hare-haren da suka kai inda daga baya suka saki wasu daga ciki bayan shiga tsakani da kasar Amurka da Majalisar dinkin Duniya suka yi. Saidai har yanzu akwai mutane 101 a hannun kungiyar ta Israela. Freeman ya bayyana kasar Iran a matsayin shedaniyar kasa wadda yace tana amfani da karnukan farautarta irin su Hamas...
A yayin da ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa, Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Biliyan 5 wajan gyaran gidan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

A yayin da ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa, Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Biliyan 5 wajan gyaran gidan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Biliyan 5 daga cikin kudin 'yan Najeriya wajan gyaran gidan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima dake Legas. Hakan ya bayyanane a shafin GovSpend wanda shafine dake saka ido kan yanda gwamnatin Najeriya ke kashe kudaden talakawa. Shafin ya nuna cewa gwamnatin ta kashe jimullar Naira N5,034,077,063 a watan Mayun da September dan gyara gidan mataimakin shugaban kasa dake Legas. Hakanan Ministan Abuja,Nyesome Wike shima ya bayyana cewa, zasu kashe Naira Biliyan 15 dan ginawa mataimakin shugaban kasar gida a Abuja.