Da yawa wanda zaka ga sun koma abin tausai a karshen rayuwarsu a lokacin suna tashe sun raina mutane sannan ko ibada basa yi>>Inji Rukayya Dawayya
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rukayya Dawayya ta bayyana cewa, da yawa wanda zaka ga sun koma abin tausai a karshen rayuwarsu lokacin suna tashe sun raina kowa.
Rukayya Dawayya ta bayyana hakane a wani Bidiyo data wallafa a shafinta na sada zumunta.
Ta fadi hakane bayan da Ummi Nuhu ta bayyana gwanin ban tausai inda yanzu haka an fara tara mata kudi dan ta kula da kanta.
Da yawa dai sun ce Rukayya Dawayya da Ummi Nuhu take.
https://vm.tiktok.com/ZMScu34tM








