Gwamnatin Tarayya zata rage Harajin da take karba na shigo da kaya daga kasashen waje
Gwamnatin tarayya na shirin rage harajin da take karba na shigo da kaya daga kasashen waje da kaso 7.
Shugaban hukumar Kwastam, Bashir Adeniyi ne ya bayyana hakan a wajan wani taro da aka gudanar.
Yace hakan zai taimaka wajan jawo hankalin masu zuba jari zuwa Najeriya.








