An ga wani Bidiyo na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a yayin da aka kawo gawar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari daga landan inda ya dakawa ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar tsawa.
Ministan dai yayi yunkurin shiga cikin jirgin saman da ya kawo tsohon shugaban kasar.
Saidai Tinubu ya daka mai tsawa yace dawo nan ina zaka?
Kalli Bidiyon a kasa:
https://twitter.com/emmaikumeh/status/1947326449163149437?t=ZubrSRrxXUUeHjQ9N6DKnw&s=19
Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta kama tare da lalata giya ta Naira Miliyan 5.8 a garin Kazaure.
Kwamandan Hisbah na jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN.
Yace shugaban karamar hukumar Kazaure, Alhaji Mansur Dabuwa ne ya jagiranci lalala giyar wadda ta kai kirate 400.
Yace shan giya a gaba dayan jihar haramunne kuma zasu ci gaba da yaki da hakan.
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false}
Diyar tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari, Noor Buhari ta bayyana cewa, kabarin Babanta, yafi kujerar mulkin da ya bari haske.
Noor ta bayyana hakane a shafinta na Instagram inda tace tun rasuwar babanta zuciyarta ta yi nauyi kuma ga kadaici
Noor ta kuma wallafa Bidiyon ta tare da mahaifin nata inda tace tana rokon 'yan Najeriya su saka mahaifinta a addu'a.
Ministan Matasa,Ayodele Olawande yace gyaran da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zaiwa Najeriya zai sa 'yan Najeriya dake zaune a kasashen waje su so dawowa gida.
Yace duka abinda shugaban kasa ke yi yana yi dan gobene, yace nan gaba kadan Najeriya zata gyaru sosai da zata rika baiwa 'yan Najeriya dake kasashen waje sha'awa su dawo gida.
Yace yanzu gwamnati na jawo matasa a jiki dan su san ana yi dasu.
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Dan gwagwarmayar kare hakkin ɗan'adam kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya zargi wani ɗansanda da sace masa gilashin da mai ɗauke da na'ura a wajen zanga-zangar da aka yi a hedikwatar ƴansanda a Abuja a yau Litinin.
Zanga-zangar, wacce Sowore tare da wasu masu fafutukar kare hakkin bil’adama da tsoffin jami’an ‘yan sanda suka jagoranta, ta nemi a inganta walwalar jami’ai da kuma cire tsoffin jami’an daga tsarin fansho na haɗaka.
Daily Trust ta rawaito cewa a ...
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben shekarar 2023, Datti Baba Ahmad ya bayyana cewa, ba zai koma jam'iyyar ADC ba.
Ya bayyana hakane a wani taron manema labarai inda yace tasu bata zo daya ba jam'iyyar ADC.
Dan haka yace zai ci gaba da zama a jam'iyyar sa ta Labour party.
Yace a zaben shekarar 2023 kuri'u Miliyan 10 suka samu dan haka ba zasu koma jam'iyyar ADC ba.
https://twitter.com/abdullahayofel/status/1947350555661382086?t=u1GOZi4DwMTrdyP-lYCRNQ&s=19
Babban malamin addinin Islama, Sheikh Musa Asadussunnah ya bayyana cewa ya kamata a karantar da mutane cewa, ba wai su kadai ne ke da hakki akan shuwagabanni ba.
Yace suma shuwagabannin na da hakki akan mutane da zasu nemi Allah ya saka musu.
Yace ko da mutum zaluntarka yayi ka mai Addu'ar da ta zarce ta zaluncin da ya maka to ka yi cuta.
https://www.tiktok.com/@sadiqaligana/video/7528907031089139000?_t=ZM-8yDbd0sV6hE&_r=1
A baya dai malam yace idan aka cuci mutum Allah zai iya yafewa koda me hakkin bai yafe ba.
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
rahotanni sun bayyana cewa, Kamfanin simintin BUA na shirin rage farashin simintinsa.
Hakan na zuwane daga bakin shugaban kamfanin, Abdulsamad BUA inda yacw hakan na da alaka da samun saukin canjin Naira da dala da kuma raguwar kudin samar da simintin.
Ya bayyana hakane a babban taron kamfanin na kasa AGM da aka yi a Abuja.
Yace a yanzu farashin dala ya doshi saukowa zuwa 1,500 akan kowace dala yace idan ya dawo zuwa 1,200 akan kowacw dala, za'a ga saukin farashin kaya sosai ...
A yau ne aka samu rahotannin dake cewa, tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da Tinubu ya kai ziyarar gaisuwar Aminu Dantata a Kano.
Da yawa dai nawa kallon ziyarar ta Kwankwaso a matsayin siyasa inda ake tsammanin zai iya komawa jam'iyyar APC.
https://twitter.com/SaifullahiHon/status/1947233776729305145?t=m7EG4FtmAnQ_fLm5bO0Iyw&s=19
Zuwa yanzu dai babu bayanai kan abinda suka tattauna.