Ji yanda aka kama wani me shekaru 33 a jihar Yobe da ya zakkewa jaririya me watanni 9
'Yansanda a jihar Yobe sun kama wani mutum me shekaru 33 da ya zakkewa jaririya me watanni 9.
An kamashi ne a Damboa dake Potiskum.
Hukumar 'yansandan tace ta kama Ibrahim Shaibu Goni ne bayan samun bayanan sirri game da laifin nasa.
Kakakin 'yansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim yace wanda ake zargin ya dauki jaririyar daga hannun mahaifiyartane inda ya je ya aikata wannan aika-aika, sannan an samu wasu abubuwa a jikin jaririyar da suka tabbatar da zargin da ake masa.
Yace duka wanda ake zargi da wanda yayi aika-aikar an mikasu ga Asibiti dan gudanar da bincike inda yace kwamishinan 'yansandan jihar yayi Allah wadai da lamarin.








