Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Sanata Natasha ta bayyana gaban Kotu a wajan shari’ar kalubalantar dakatar da ita daga majalisa

Sanata Natasha ta bayyana gaban Kotu a wajan shari’ar kalubalantar dakatar da ita daga majalisa

Duk Labarai
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya ta isa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a yau Talata don sauraron karar da aka shigar a kanta. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Mai Shari’a Binta Nyako ta sanya ranar yau talata domin sauraron karar raina kotu da shugaban majalisar dattawa ya shigar kan Akpoti-Uduaghan. Mai Shari’a Nyako ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar Litinin mai zuwa domin ci gaba da sauraron karar gaba ɗaya. Jaridar Arewa
Kalli Bidiyo: ‘Yansanda sun kama Jarumin Tiktok, Hassan Make-Up, Sannan an ci zarafinsa ta hanyar zagi da mari, duk da dokar ‘yansanda ta hana hakan

Kalli Bidiyo: ‘Yansanda sun kama Jarumin Tiktok, Hassan Make-Up, Sannan an ci zarafinsa ta hanyar zagi da mari, duk da dokar ‘yansanda ta hana hakan

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, 'yansanda sun kama Jarumin Tiktok, Hassan Make-Up. A wani Bidiyo da aka ganshi a ofishin 'yansanda, An ga Dansandan dake masa tambayoyi ya mareshi tare da zagi wanda hakan ya sabawa dokar aikin dansanda. Ko da a jiya, saida Kwamishinan 'yansanda na birnin tarayya, Abuja ya ja kunnen jami'ansa cewa, zagi da marin wanda ake zargi ko me laifi baya cikin aikin dansanda. https://twitter.com/Sadeeq_Malo/status/1922182213228978353?t=IuFMmAMvMSZV4WyxBsU_2g&s=19 Rahoton da muke samu shine Hassan Make-Up ya zo bikin Rarara ne aka kamashi.
ABIN ALFAHARI: Matasa Uku Daga Jihar Gombe Sun Kammala Karatun Jami’a A Garin Madina Dake Kasar Saudiyya

ABIN ALFAHARI: Matasa Uku Daga Jihar Gombe Sun Kammala Karatun Jami’a A Garin Madina Dake Kasar Saudiyya

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Matasa Uku Daga Jihar Gombe Sun Kammala Karatun Jami'a A Garin Madina Dake Kasar Saudiyya Daliban sune; Khuzaifa Usman Muhammad daga Pantami Abubakar Waziri Daga Kumo Yahaya Ibrahim Daga Kasuwar Mata Allah Ya sanyawa karatunsu albarka.
Matashiya ta Kàshè kanta saboda bata ci maki me yawa a jarabawar JAMB ba

Matashiya ta Kàshè kanta saboda bata ci maki me yawa a jarabawar JAMB ba

Duk Labarai
Matashiya me suna Opesusi Faith Timilehin 'yar Kimanin shekaru 19 ta sha guba ta kashe kanta ranar Litinin saboda ta ci maki 190 a jarabawar JAMB. Faith na zaunene da yayarta a Legas amma 'yar asalin Abeokuta ce, makwabtansu sun bayyana ta a matsayin mutuniyar kirki wadda bata son hayaniya. Danginta sun ce ko a shekarar data gabata ta rubuta jarabawar JAMB amma makinta na shekarar data gabata ya fi na yanzu. Saidai wani abin tashin hankali shine an bata Admission bayan mutuwarta.
‘Yar Shekaru 16 ta yi Gàrkùwà da kanta inda ta nemi iyayenta su biya kudin fansa Naira Miliyan 2

‘Yar Shekaru 16 ta yi Gàrkùwà da kanta inda ta nemi iyayenta su biya kudin fansa Naira Miliyan 2

Duk Labarai
Matashiya 'yar kimanin shekaru 16 wadda ke ajin SS2 a makarantar Sakandare ta yi garkuwa da kanta inda ta nemi a biya kudin fansa Naira Miliyan 2. Lamarin ya faru ne a Abakaliki, Jihar Ebonyi. Matashiyar ta kira dan uwanta inda ta sanar dashi cewa an yi garkuwa da ita. Wani dake da alaka da iyayenta ne ya taimaka mata wajan shirya wannan lamarin. Kakakin 'Yansandan jihar, Joshua Ukandu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kama wadanda ake zargi kuma sa'a tabbatar an hukuntasu.
An kama mahaifi da zargin yiwa ‘ya’yansa mata Fyàde

An kama mahaifi da zargin yiwa ‘ya’yansa mata Fyàde

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Legas na cewa, 'yansanda a jihar sun kama wani uba me suna Best Orji dan kimanin shekaru 39 da zargin yiwa 'ya'yansa fyade. Mahaifiyar yaran ce ta kai korafi wajan 'yansandan inda tace ya aikata lamarin a yayin da yaran ke da shekaru 12 da 14. Kakakin 'yansandan jihar, (PPRO),CSP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya bayar ga manema labarai. Yace sun kama Best Orji zasu gurfanar dashi a gaban kuliya.
Bidiyon tsiraici na Diyar Fasto dake shirin gadonshi, kuma har ta fara wakitarsa a coci tana wa’azi ya bayyana, an ganta turmi da tabarya ita da wani

Bidiyon tsiraici na Diyar Fasto dake shirin gadonshi, kuma har ta fara wakitarsa a coci tana wa’azi ya bayyana, an ganta turmi da tabarya ita da wani

Duk Labarai
Wata diyar fasto ta dauki hankula a kafafen sadarwa bayan da Bidiyon tsiraicinta ya bayyana. An ga Bidiyon nata ita da wani turmi da tabarya suna aikata Alfasha. Diyar Faston dai wadda take shirin gadon babanta, Tuni har ta fara wa'azi a cocinsa. Saboda tsiraicin dake cikin Bidiyon ba zamu iya kawo muku shi ba anan.
Zaki ya kàshè me gidansa balarabe ya kuma cinye gawar kwanaki kadan bayan da ya siyoshi ya rika wasa dashi a gida

Zaki ya kàshè me gidansa balarabe ya kuma cinye gawar kwanaki kadan bayan da ya siyoshi ya rika wasa dashi a gida

Duk Labarai
Wani zaki da Balarabe a garin Najaf dake kudancin kasar Iraqi ya siyo dan ya rika wasa dashi, ya kashe me gidan nasa kwanki kadan bayan siyoshi. Bayan ya kasheshi, ya kuma cinye kusan duka gawar me gidan nasa. Lamarin ya faru ranar 8 ga watan Mayu. Kakakin 'yansandan yankin Najab, Mufid Tahir, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sai da aka kashe zakin saboda yaki yadda ya daina cin gawar me gidan nasa. Me gidan Aqil Fakhr al-Din na da shekaru 50 kuma an bayyana cewa ya dade yana ajiye zaki a gidansa.
Yadda ‘yan tà’àddà suka kàshè sojoji suka kwashe màkàmài a sansanin soji a Borno, Sojojin dai sun tsere yayin da màhàràn suka afkawa sansanin nasu, saidai da gari ya waye sun koma, Kalli bidiyon Yanda sojojij ke kuka, da hotunan gawarwakin wadanda aka kashe birjik a kasa

Yadda ‘yan tà’àddà suka kàshè sojoji suka kwashe màkàmài a sansanin soji a Borno, Sojojin dai sun tsere yayin da màhàràn suka afkawa sansanin nasu, saidai da gari ya waye sun koma, Kalli bidiyon Yanda sojojij ke kuka, da hotunan gawarwakin wadanda aka kashe birjik a kasa

Duk Labarai
Mayaƙan Boko Haram sun kashe sojoji da ba a san adadinsu ba tare da yin awon gaba da wasu da dama bayan wani ƙazamin hari da suka kai a sansanin soji da ke yankin Marte a Jihar Borno. Majiyoyin soji sun ce mayaƙan ƙungiyar sun fi karfin sojojin, inda suka kwashi makamai masu tarin yawa sa’annan suka cinna wa ma’ajiyar makamai da ke sansanin sojin wuta. Mazauna yankin sun bayyana cewa da misalin ƙarfe 3 na asuba, kafin wayewar garin ranar Asabar ne Boko Haram ta ƙaddamar da harin. https://twitter.com/SaharaReporters/status/1922035239003562473?t=NnNR7DazlyCWs6i2qrXRdA&s=19 Wani soja da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, “ISWÀP ta ƙwace Marte, an kashe sojoji da dama, an kama wasu, amma wasu sun samu sun tsere zuwa Dikwa, inda runduna ta 24 take. “’Yan ta’addan sun ƙona tankok...
DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban Amurka Donald Trump ya isa Saudiyya domin fara zagayen kwanaki hudu a yankin Gulf

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban Amurka Donald Trump ya isa Saudiyya domin fara zagayen kwanaki hudu a yankin Gulf

Duk Labarai
Shugaban Amurka Donald Trump ya isa Saudiyya domin fara zagayen kwanaki hudu a yankin Gulf. Duk yankin da shugaban Amurka ya zaɓa a matsayin wurin da zai fara kai ziyara na nufin yankin na da matuƙar muhimmanci inda ake yi wa ziyarar kallon wani ɓangare. A watan Mayun 2027, Donald Trump ya sauya abin da aka saba a al'adance inda shugabannin Amurka kan fara ziyara da wurare kamar Canada da Mexico da kuma Turai. To sai dai kuma maimakon hakan, sai ya fara da ƙasar Saudiyya mai tarin albarkatun manfetur, a zangon mulkinsa na farko, kuma yanzu bayan ya yi kome sai ya zaɓi fara ziyarar da yankin na Gulf daga ranar Talata 13 zuwa Juma'a 16 ga watan Mayu. Zuwa ƙasashen Saudiyya da Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, ka iya zama ziyarar Trump ta farko a zangon mulkinsa na farko duk da...