Monday, December 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Sanata Natasha Akpoti na shirin komawa jam’iyyar APC

Sanata Natasha Akpoti na shirin komawa jam’iyyar APC

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Sanata Natasha Akpoti na shirin komawa jam'iyyar APC. Hakan ya fito ne a yayin da aka ganta tana bin wakar Rarara wadda yawa Tinubu a ziyarar da ya kai Katsina. https://www.tiktok.com/@senatornatasha/video/7501822342620810502?_t=ZM-8wGc5cquf6V&_r=1 Ana tunanin Sanata Natasha Akpoti na shirin komawa APC ne dan ta binne fadanta da Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio.
HASBUNALLAHU WA NI’IMAL WAKIL: Bèĺlò Țùŕjì Ya Kori Mutàñèn Gàriñ Bafàrawa

HASBUNALLAHU WA NI’IMAL WAKIL: Bèĺlò Țùŕjì Ya Kori Mutàñèn Gàriñ Bafàrawa

Duk Labarai
HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL: Bèĺlò Țùŕjì Ya Kori Mutàñèn Gàriñ Bafàrawa. Daga Datti Assalafiý Shugaban barayin daji Be||0 Turj! ya kori mutanen dake zama a garin Bafarawa, kusan gaba daya mutanen garin sun watse zuwa neman mafaka a halin da ake ciki Sannan Be||0 Turj! ya aika takarda zuwa ga mutanen garuruwan Kamarawa, Arume da Kagara, ya ce baya son ganin wani mutum a cikin garuruwan daga yau Lahadi zuwa misalin karfe 4 na yammaci Akwai labarin da na gani, ance a daren jiya kadai kusan garuruwa 5 barayin daji suka yiwa hari a tsakanin jihar Katsina da Zamfara Sannan jiya 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci makarantar Sakandare (GSS) dake garin Raka a karamar hukumar Tsafe jihar Zamfara inda suka kashe Malami sannan sukayi garkuwa da mutane da yawa Abubuwan da suk...
‘Yan kasar waje guda dubu daya da shida sun karbi shaidar zama ‘yan Najeriya

‘Yan kasar waje guda dubu daya da shida sun karbi shaidar zama ‘yan Najeriya

Duk Labarai
'Yan kasar waje guda dubu da shida ne suka karbi shaidar zama 'yan Najeriya a cikin shekaru 8 da suka gabata. Lamarin ya farune daga shekarar 2017 zuwa shekarar 2023. Saidai wannan lamba an kirgata ne kawai akan wanda shugaban kasa ya baiwa takardar zama 'yan kasar, ba'a saka wanda suka je ofishin hukumomi ba suka An fara lissafinne daga Gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wani Kantin Siyar Da Kayan Alatu A Kano Sun Baiwa Fauziyya D. Sulaiman Kyautar Mota

Wani Kantin Siyar Da Kayan Alatu A Kano Sun Baiwa Fauziyya D. Sulaiman Kyautar Mota

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani Kantin Siyar Da Kayan Alatu A Kano Sun Baiwa Fauziyya D. Sulaiman Kyautar Mota
An daure wannan malamar makarantar tsawon shekaru 30 saboda yiwa dalibanta maza Fyàdà

An daure wannan malamar makarantar tsawon shekaru 30 saboda yiwa dalibanta maza Fyàdà

Duk Labarai
Hukumomi a kasar Amurka sun daure malamar makaranta me suna Jacqueline Ma 'yar kimanin shekaru 36 tsawon shekaru 30 a gidan yari saboda samunta da laifin yiwa dalibinta maza fyade. A baya dai an bata kyautar karramawa a matsayin gwarzuwar malama a yankin San Diego County na kasar. Saidai daga baya an kamata da laifin yiwa yara dalibanta fyade, kuma ranar Juma'ar data gabata ne aka yanke mata hukuncin shekaru 30 a gidan yarin. Bayan yanke mata hukuncin, ta ashe da kuka inda tace tana fatan za'a yafe mata kuma tana danasanin bin son zuciya wajan batawa wadannan kananan yara Tarbiyya.
Shirin su El-Rufai na kokarin hada kan ‘yan Jam’iyyar Adawa da kayar a Tinubu a shekara 2027 na samun Tangarda saboda manyan ‘yan Adawar sai komawa APC suke

Shirin su El-Rufai na kokarin hada kan ‘yan Jam’iyyar Adawa da kayar a Tinubu a shekara 2027 na samun Tangarda saboda manyan ‘yan Adawar sai komawa APC suke

Duk Labarai
Shirin jam'iyyun Adawa na hadewa waje daya dan yin galaba akan jam'iyyar APC a zaben shekarar 2027 ya fara saun tangarda saboda komawa jam'iyyar APC me mulki da 'yan Adawa dayawa ke yi. Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne ke jagorantar wannan tafiya ta 'yan adawa. Duk da kokawar da 'yan Najeriya ke yi na tsadar rayuwa amma jam'iyyar APC me mulki sai kara samun manyan 'yan Adawa take suna komawa cikin ta. A baya dai an yi tsamanin Shugaba Tinubu da jam'iyyar APC zasu sha wahala wajan cin zabe Wanda su kansu 'yan Adawar abinda suka yi amfani dashi kenan wajv fara wannan tafiya tasu amma gashi lamarin na son dagule musu.
Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa dan magance matsalar barin Jam’iyyar da ake ta yi

Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa dan magance matsalar barin Jam’iyyar da ake ta yi

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnonin Jam'iyyar PDP sun kira wani taro na musamman da zai tattauna rikicin dake cikin jam'iyyar da yasa mutane ke ta fita daga cikinta. Gwamnonin sun kira tsaffin Gwamnonin Jam'iyyar da tsaffin shuwagabannin majalisun tarayya da sauran masu ruwa da tsaki a jam'iyyar dan tattaunawa kan yanda za'a shawo kan wannan matsala. Jam'iyyar PDP na fama da matsalar ficewar da yawa daga cikin membobinta zuwa jam'iyyar APC me mulki. Na baya-bayannan sune komawar Gwamnan Jihar Delta,b Sheriff Oborevwori da Tsohon Gwamnan jihar kuma tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Ifeanyi Okowa zuwa jam'iyyar APC. Hakanan duka sanatocin jihar Kebbi su 3 suma sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC da sauransu.