Dattawan APC sun ce basu son Kwankwaso ya koma jam’iyyar
Raɗe-raɗin dawowar Kwankwaso jam'iyyar APC mai mulki, na cigaba da fitowa fili.
An samu rudani a sakateriyar jam’iyyar APC, a ranar Talata, bayan da Shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da Ministan Jiha na Harkokin Gidaje da Ci gaban Birane, Yusuf Ata, suka yi sabani kan daowawar Kwankwaso jam'iyyar APC.
Yayin da Minista Ata ke cewa Kwankwaso – wanda kuma tsohon Ministan Tsaro ne – ya rasa karbuwa a Kano kuma siyasar sa na dab da mutuwa, Ganduje ya ce APC ba lallai ta ki karbansa ba, yana mai cewa “aboki a lokacin bukata, aboki ne na gaskiya.”
Ata, yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da Ganduje a sakateriyar jam’iyyar da ke Abuja, ya bayyana cewa matsin lambar siyasar da Kwankwaso ke ciki ne ke sa shi kokarin dawowa APC, yana mai cewa har Kw...







