Thursday, December 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyo da Hotuna: Yanda mutanen jihar Anambra suka rika shewar cewa shugaba Tinubu kai ne babanmu bamu da baban da ya wuce ka

Kalli Bidiyo da Hotuna: Yanda mutanen jihar Anambra suka rika shewar cewa shugaba Tinubu kai ne babanmu bamu da baban da ya wuce ka

Duk Labarai
Bidiyon shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana inda aka ganshi mutanen jihar Anambra suna masa wakar cewa shi kadaine babansu, basu da baban da ya wuceshi. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kai ziyara jihar Anambra inda aka masa tarba me kyau. Cikin Barkwanci, Shugaba Tinubu ya bayyanawa Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo cewa, a bashi fili zai gina gidan da zai yi ritaya a ciki a jihar Anambra.
Ka bude iyakoki a kaiwa Falasdiynawa Tallafin kayan Abinci>>Donald Trump ya gayawa Benjamin Netanyahu

Ka bude iyakoki a kaiwa Falasdiynawa Tallafin kayan Abinci>>Donald Trump ya gayawa Benjamin Netanyahu

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyanawa shugaban kasar Israela, Benjamin Netanyahu cewa a bide iyakokin kasar Falasdinawa a kai musu agajin kayan abinci da sauran kayan Masarufi. Ya bayyana hakanne a wata ganawa da suka yi ta wayar salula. Trump yace Falasdinawa na cikin halin matsin rayuwa kuma ya kamata a kyautata musu. Masu sharhi akan al'amuran yau da kullun sun bayyana cewa, wannan magana ba lallai tawa Benjamin Netanyahu dadi bane. Hakanan a wani yanayi da ake kallon na mayar da Benjamin Netanyahu gefe, Trump yayi sulhu da mayakan kasar Yemen, sannan ya ci gaba da tattaunawa da kasar Iran kan makamashin kare danginta. Hakanan Wani rahoto yace Trump ya nuna cewa baya bukatar Netanyahu wajan mu'amala da Gabas ta tsakiya.
Nasarar Rayuwa bata dogara akan karatun Bòkò ba>>Inji Gwamnan Jihar Bauchi

Nasarar Rayuwa bata dogara akan karatun Bòkò ba>>Inji Gwamnan Jihar Bauchi

Duk Labarai
Gwamnan jihar Bauchi, Dr. Bala Mohammed ya bayyana cewa, Nasarar Rayuwa bata dogara akan karantun Boko ba. Gwamnan ya bayyana hakane a yayin ganawa da masu sana'o'in hannu a jiharsa inda yace musu su mayar da hankali kan sana'o'insu sannan su kaucewa shiga dabi'un da zasu wargaza rayuwarsu. Yace mutane da yawa da suka yi nasara a rayuwa sun fara ne da sana'o'i kanana kuma basu dogara da karatun boko ba. Yace karatun Boko kawai ana yi ne dai amma karatun Qur'ani shine abin yi. Yace musamman direbobi suna zama masu kudi sosai.
Yau za a fara jigilar maniyata a Najeriya

Yau za a fara jigilar maniyata a Najeriya

Duk Labarai
A Najeriya a yau Juma'a ne ake sa ran jirgin farko na maniyatan aikin hajjin bana na ƙasar zai tashi zuwa ƙasar Saudiyya. Hukumar alhazan ƙasar ta ce jirgin farko zai fara jigilar maniyyata 315 na jihohin Imo da Abia da kuma Bayelsa zuwa ƙasar Saudiyya. Za a ci gaba da jigilar maniyatan daga Bauchi da Kebbi da jihohin Osun da kuma Legas.
Duk wanda ya zagi ubanka ka zagi uwassa>>Sheikh Salihu Zaria

Duk wanda ya zagi ubanka ka zagi uwassa>>Sheikh Salihu Zaria

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Salihu Zaria ya baiwa mutane shawarar su daina nuna ragowa. Ya bayyana hakane a wani faifan Bidiyonsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda aka jishi yana cewa duk wanda ya zageka ka rama. Wasu dai sun ji dadin wannan wa'azi amma wasu na ganin kamar kan malam ya dau zafi ne a yayin wannan magana. https://twitter.com/abu_twinss/status/1920596150412890552?t=9tqWxroB2SKk2cpm5BPERg&s=19 Malam dai kan yi wa'azi da kan dauki hankulan mutane sosai a kafafen sadarwa.
Shugaba Tinubu ya nemi Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya samo masa fili ya gina gidan da zai yi ritaya a jihe Anambra

Shugaba Tinubu ya nemi Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya samo masa fili ya gina gidan da zai yi ritaya a jihe Anambra

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nemi gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya nemo masa filin da zai gina gidan da zai yi ritaya a jihar Anambra. Shugaban ya bayyana hakane a yayin ziyarar sa ta farko a matsayin shugaban kasa a jihar ta Anambra inda ya kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar ta yi daban-daban. Ya jinjinawa Gwamnan kan kokarin gyaran jihar da yake yi inda yace masa shima ya zama dan jihar Anambra a sama masa fili ya gina gidan da zai yi ritaya. Shugaban dai ya fadi hakanne cikin raha.
Idan Baku Daukar shawarwarin da muke bayarwa ba za’a kawo karshen matsalar tsaro ba a kasarnan>>Akpabio ya Gargadi Tinubu

Idan Baku Daukar shawarwarin da muke bayarwa ba za’a kawo karshen matsalar tsaro ba a kasarnan>>Akpabio ya Gargadi Tinubu

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Kakakin majalisar Dattijai ya gargadi bangaren zartaswa akan su daina sukar shawarar da majalisar ke bayarwa kan yanda za'a magance matsalar tsaron kasarnan. Majalisar Dattijai dai ta bayar da shawarar a yi taron karawa juna sani na kwanaki 2 dan samo hanyar da za'a magance matsalar tsaron Najeriya. Saidai Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana cewa ba ta irin hakane za'a kawo karshen matsalar tsaro ba inda yace kwamandojin sojoji ne ke bayar da odar yanda za'a kai ...
Labari Me Dadi: Bankin Duniya ya bayar da Dala Miliyan $215 a rabawa Talakawa kyauta saboda halin matsin da ake ciki

Labari Me Dadi: Bankin Duniya ya bayar da Dala Miliyan $215 a rabawa Talakawa kyauta saboda halin matsin da ake ciki

Duk Labarai
Najeriya ta samu karin bashin dala Miliyan $215 daga bankin Duniya wanda ta nema dan rabawa talakawa tallafi kyauta. Gaba dayan bashin da Gwamnatin Najeriya ta nema dala Miliyan $800 ne wanda tace zata yi amfani dashi wajan rabawa Talakawa kudin kyauta, musamman tsofaffi da masu nakasa da saran masu rauni cikin al'umma. Tun a shekarar 2021 ne Gwamnatin ta nemi bashin saidai saidai bankin Duniyar be bayar da kudin gaba daya ba. Yana bayar dasu da kadan kadanne, zuwa yanzu Bankin ya bayar da Jimullar dala Miliyan $530 kenan. Wannan tallafi dai za'a bayar dashi ne saboda ragewa mutane radadin cire tallafin man fetur dana dala da sauran tsare-tsaren gwamnati da suka jefa mutane cikin halin kaka nika yi.