Friday, December 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Mayar da Najeriya tsarin Jam’iyya daya na da hadari>>Goodluck Jonathan

Mayar da Najeriya tsarin Jam’iyya daya na da hadari>>Goodluck Jonathan

Duk Labarai
Bayan tsawon lokaci ba a ji ta bakinsa ba dangane da faruwar al'amuran siyasa, tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ɓara inda ya yi gargaɗin cewa "abu ne mai haɗari ɗora Najeriya a kan turbar jam'iyya guda ɗaya". Ba kasafai dai ake jin bakin Goodluck Jonathan ba a al'amura kasancewarsa mutum mai kawaici da rashin son yawan magana. To sai dai a ranar Larabar nan, tsohon shugaban na Najeriya yayin wata lacca da aka shirya a Abuja domin tuna wa da marigayi Edwin Clerk, dattijo ɗan ƙabilar Ijaw wanda ya rasu yana da shekara 97, Jonathan ya ja hankalin gwamnati da jam'iyya mai mulki ta APC da ake zargi da mayar da ƙasar ƙarƙashin tsarin jam'iyya guda. Kalaman Goodluck Jonathan Tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya ce duk wnai yunƙurin mayar da Najeriya kan tsarin jam'i...
Gwamnatin Kano ta dakatar da watsa shirye shiryen siyasa kai tsaye a kafafen yada labarai dake jihar. Hakan na zuwa ne domin tantance da kuma tsabtace kalamai da yan siyasa ke yi a kafar sadarwa na radiyo da talabijin

Gwamnatin Kano Ta Haramta Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye a Kafafen Watsa Labarai Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana dakatarwa nan take ga dukkan shirye-shiryen siyasa da ake yadawa kai tsaye a kafafen watsa labarai na jihar. An bayyana wannan mataki ne yayin taron tattaunawa na kowane lokaci da ake gudanarwa a Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, wanda Kwamishinan Yada Labarai, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jagoranta tare da shugabannin kafafen yada labarai. A cewar wata sanarwa da Daraktan Harkokin Musamman na ma’aikatar, Sani Abba Yola, ya sanyawa hannu, an dauki wannan mataki ne don dakile yada kalaman da za su iya haifar da fitina da barazana ga zaman lafiya da daidaiton al’adu da addini a jihar. “Ba mu dauki wannan mataki don murkushe ‘yan adawa ba,” in ji ...
Matata tace Na burgeta kuma zan yi kyau da Fafaroma shiyasa na watsawa Duniya ta gani>>Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayi karin bayanin dalilin da yasa ya wallafa hotonsa da kayan Fafaroma

Bayan da cece-kuce yayi yawa akan hoton da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya wallafa yana sanye da kayn Fafaroma, ya fito yayi karin bayani. Shugaba Trump yace Kamin ya dora hoton a shafinsa na Sada zumunta sai daya nunawa matarsa kuma ta amince dashi cewa yayi kya. Yace dan haka yayi amannar kasancewar matarsa 'yar Darikar Katolika, to yasa sauran ma 'yan darikar zasu so hoton. A baya dai da aka Tambayeshi wa yafi cancanta ya zama Fafaroma, sai yace shine.
Bayan da ta zargeni da nemanta da lalata Har Hotunan Selfie Sanata Natasha Akpoti ke daukar mu ni da ita idan mun tafi aiki, saboda tsabar jin dadin aiki dani kuma nace ta kawo hujjar zargin da take min amma taki

Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa, Abin mamaki bayan da sanata Natasha Akpoti ta zargeshi da cewa ya nemeta da lalata, sun yi tafiye-tafiye tare har zuwa kasashen waje aiki. Yace kuma har hotuna Selfie take daukarsu idan suna aiki saboda jin dadin aiki dashi. Yace amma kuma ya nemi ta gabatar da hujjar zargin da take masa amma taki. Sanata Natasha Akpoti dai tace ba zata bayar da hujjojin zargin da takewa, Sanata Godswill Akpabio ba sai an je kotu.
Kalli Bidiyo: Iyayen mu da suka rika haihuwar ‘ya’ya talatin akwai saukin rayuwa a lokacin amma yanzu Rayuwa ta canja dole mutum ya kula da yawan ‘ya’yan da zai haifa>>Sheikh Ibrahim Maqari

Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Ibrahim Maqari ya jawo hankalin mutane akan tara 'ya'ya. Yace a baya mutane na haihuwar 'ya'ya talatin saboda akwai wadatar gurin zama kuma a wancan lokacin ba sai an saka yaro a makaranta ba. Yace amma yanzu Rayuwa ta canja, irin wancan abin ba zai yiyu ba. https://www.tiktok.com/@prof.ibrahim.maqa92/video/7500248373430078725?_t=ZM-8wB1sZ5f0AZ&_r=1 Saidai malam yace irin mutanen mu na da wahalar canjawa akan wani abu da suka saba dashi.
Cikin Girmamawa Muna Jajantawa Atiku Abubakar, Dangote, Sanata Saraki Da Dino Melaye Kan Rashin Nasarar Da Arsenal Ta Yi Akan PSG A Daren jiya

Cikin Girmamawa Muna Jajantawa Atiku Abubakar, Dangote, Sanata Saraki Da Dino Melaye Kan Rashin Nasarar Da Arsenal Ta Yi Akan PSG A Daren jiya

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Cikin Girmamawa Muna Jajantawa Atiku Abubakar, Dangote, Sanata Saraki Da Dino Melaye Kan Rashin Nasarar Da Arsenal Ta Yi Akan PSG A Daren jiya Bayan su, wane Babba kuka sani dan Arsenal a kasar nan?
Gwammatin Tinubu tace zata gina makamin kare dangi, watau Nokiliya, Saidai Minista yace kul kada a fara

Gwammatin Tinubu tace zata gina makamin kare dangi, watau Nokiliya, Saidai Minista yace kul kada a fara

Duk Labarai
Ministan wutar Lantarkin Najeriya, Adebayo Adelabu ya gargadi yunkurin hukumar makamashin Najeriya na samar da tashoshin makamin Nokiliya dan samar da wutar lantarki. Hukumar dai tace tana son yin hakanne dan samar da wutar Lantarki me karfin 1,200 Megawatt da zata magance matsalat wutar Lantarkin Najeriya. Shugaban Hukumar Makamashin, Anthony Ekedewa ya kaiwa ministan wutar lantarkin ziyara a ofishinsa a Abuja ranar Talata ind ya bayyana cewa suna shirin samar da tashoshin makamin kare dangi guda 4 a Najeriya. Yace idan suka yi nasara hakan zai samar da ingantacciyar wutar Lantarki me karfi sosai a Najeriya Yace suna son kafa wadannan tashoshin wutar ne a jihohin Kogi da Akwa-Ibom. Saidai yace basu da kudi amma suna neman hada kai da ma'aikatar wutar Lantarkin. Mini...
Budurwa ta yi karyar An yi garkuwa da ita, ashe dakin saurayinta ta tafi suka buga soyayya

Budurwa ta yi karyar An yi garkuwa da ita, ashe dakin saurayinta ta tafi suka buga soyayya

Duk Labarai
Wata daliba dake ajin karshe na jam'ar Jihar Ekiti, EKSU me suna Helen Kayode ta yi karyar an yi garkuwa da ita amma ashe dakin saurayinta ta tafi suka sha soyayya. Ta aikawa kanwarta da sakon cewa, ta shiga motar da ba ta gane mata ba inda daga baya tace an kaita wani kango ana tsare da ita. Sakon nata ya watsu sosai a kafafen sada zumunta sannan hankalin mutanen Iworoko-Ekiti da Ado-Ekiti ya tashi sosai inda daga canne ta fito. Kakakin 'yansandan jihar, SP Sunday Abutu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun kama dalibar. Kuma ta amsa laifin data aikata na aika sakon garkuwa da ita amma na karya. Hukumar 'yansandan sun yi gargadin cewa kada a sake samun wanda yayi hakan in ba haka ba mutum zai fuskanci hukunci
Tabbas na bayar umarnin a ciro min kàn Wike sannan a kàshè Tinubu inda har nasa  ladar Naira Miliyan 100 ga wanda yayi hakan>>Nnamdi Kanu

Tabbas na bayar umarnin a ciro min kàn Wike sannan a kàshè Tinubu inda har nasa ladar Naira Miliyan 100 ga wanda yayi hakan>>Nnamdi Kanu

Duk Labarai
Shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB dake son lafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya aminta cewa ya sa a kashe masa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ta hanyar ciro kansa. Sannan kuma yasa a kashe shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kona kadarorinsa, inda har ya saka ladar Naira Miliyan 100 ga duk wanda yayi hakan. Wani shaida ne ya bayyana hakan a kotu inda yace Kani ya fadi hakanne a gidan Rediyon da ya bude. An kuma saurari maganar da Kanu yayi wadda aka nada a cikin Kotun inda aka jishi ana cewa, a kashe Wike saboda bai cancanci rayiwa ba sannan a kashe Tinubu a kona kadarorinsa sannan a kashe jami'an tsaro.