Rundunar yansandan Kano ta kama masu yi mata sojan gona
Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama ƴansandan bogi uku da ake zargi da yin damfara ta hanyar shigar burtu a matsayin ƴansanda a jihar Kano, bayan sun damfari wani mutum naira miliyan ɗaya da dubu talatin.
Mutanen da aka kama sun fito ne daga ƙaramar hukumar Daura ta jihar Katsina inda aka kama su a ranar 2 ga Satumba, 2025, a Danagundi Quarters.
Rundunar ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da Jama’a na ƴansanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.
Sanarwar ta ce "Kamar yadda bincike ya nuna, an kama su ne bayan wanda suka damfara ya nemi ɗauki, inda ya yi bayanin yadda abin ya faru.
"Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargi sun yi shigar burtu a matsayin ƴansanda inda suka yi iƙirarin cewa suna da wasu ƙwarewa na musamman da za su t...








