Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma ya mayar da mafi karancin Albashi a jiharsa Naira ₦104,000.
Sannan malaman jami'a kuma ya mayar musu da mafi karancin albashinsu zuwa Naira ₦222,000.
Su kuwa Likitoci ya mayar musu da mafi karancin Albashi zuwa Naira 582,000
Tauraruwar Tiktok, me sayar da kayan Mata dana maza, Alpha Charles Borno ta dauki hankula bayan Bidiyon fata dora inda aka ganta zaune a cikin mota
Da yawa sun bayyana cewa bata sanye da wando wanda hakan ya jawo cece-kuce.
Saidai wasu sun ce sun tana da wando.
Lamarin dai ya jawo zazzafar muhawara.
https://www.tiktok.com/@alphacharlesborno/video/7541963311210892552?_t=ZS-8zD6GTs339l&_r=1
Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya, NRC ta sanar da dakatar da sufurin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, har sai abinda hali yayi.
Hukumar ta sanar da hakane jim kadan bayan hadarin da aka samu bayan tashin jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna bayan da ya kaucewa taragonsa.
Daraktan hukumar, Kayode Opeifa ne ya sanar da haka a Abuja ga manema labarai, Ya musanta rade-radin da ake yi cewa dama jirgin kasan yana da matsala.
Yace jami'an hukumar su dana hukumar bincike ta kasa, (NSIB) sun halarci wajan faruwar hadarin inda yace suna kan bincike kan lamarin.
Ya kuma kara da cewa, sun fara shirin mayarwa da fasinjojin fake cikin jirgin kudaden tikiti da suka saya.
Yace mutane 6 sun ji raunika ba masu muni ba kuma an basu kulawar data kamata.
Hukumar kula da magunguna da abinci ta kasa, NAFDAC ta yi gargadi cewa an shigo da maganin hana daukar ciki me suna Postinor na bogi Najeriya.
Hukumar tace ta tabbatar da hakan ne bayan da hukumar Society for Family Health (SFH) wadda itace aka yadda ta shigo da maganin ta bayyana cewa ba itace ta shigo da maganin boge din ba.
NAFDAC tace yanda za'a gane maganin na boge shine, rubutunsa kanana ne, sannan an yi kuskuren rubuta kalmar Verify inda aka rubuta Veify.
Sannan kuma akwai kuskuren rubutun Distnibuted in Nigeria maimakon a rubuta, distributed in Nigeria.
Hukumar tace wannan magani na jabu na nan yana yawo a Najeriya kuma akwai yiyuwar yana dauke da sinadarai masu cutarwa dan haka ta nemi a gujeshi.
Bishiyar Annabi Adamu A.S.
Tsarabar Mawloudin Bana a gidan Qadiriyya ita ce, reshen Bishiyar Itaciyar Annabi Adamu A.S.Bayan an yi bukin ɗaga tuta an fara baje kolin kayan tarihi a gidan sakamakon shiga bukin maulidin a Kano. Inda aka gano Qaribu Kabara tare da rike wani Reshe da ake cewa reshen bishiyar Annabi Adamu ne da aka kawo masa daga kasar Saudiyya a matsayin kyautar bangirma saboda haɗinkan da ya bayar wajen daƙile Sheikh Abduljabbar Kabara ɗan uwansa da ake zargin zai shiga Shi'a.Rahoton: Shawus Assufy NaTa'ala
Me za ku ce!
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Najeriya da kasar Brazil sun kulla huldar kasuwanci data hada da Kudi, Harkar lafiya, da sufuri da kuma huldar diflomasiyya.
Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace a yanzu sun kulla huldar tashin jirage daga Najeriya zuwa kasar Brazil Kai tsaye.
Sannan akwai maganar kimiyya da fasaha da sauransu.
Malamin Addinin Islama, Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya bayar da labarun irin mutanen da ya kara dasu a baya kuma basu kai labari ba.
Malam yace daga cikinsu akwai wanda yace idan Izala Gaskiyace kada Allah ya kaishi shekara me zuwa kuma baikai shekarar me zuwa ba.
Malam ya bayyana hakane a wajan tafsir da yake yi.
https://www.tiktok.com/@saleemyusufmuhammadsambo/video/7541886797857426695?_t=ZS-8zCarB4l1tI&_r=1
Wata daliba a jami'ar Niger Delta University dake jihar Bayelsa ta kama malaminta da fada bayan da ya kwace mata waya saboda kamata tana satar amsa.
Rahotanni dai sun ce dalibar ta fara dukan malaminta inda shima ya zage ya rama.
A Bidiyon da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta an ga Malamin shima ya dage yana dukar dalibar.
https://twitter.com/dammiedammie35/status/1959999856295989379?t=x-kuJAwxEllVbygVlbWqZw&s=19
A dazu ne muka ji labarin cewa, jirgin kasar dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja ya fadi bayan ya taso daga Abuja.
Zuwa yanzu dai babu sanarwar ko an ji rauni ko asarar dukiya ko ta rai.
Bidiyo ya bayyana na yanda lamarin ya faru.
https://twitter.com/_UncleDara/status/1960345192990404899?t=AMYO3G8AkF4U5W_ujH3u7A&s=19
https://twitter.com/TheNationNews/status/1960322832262410424?t=BcRiUZrk37MHuHuLxYC_Kw&s=19
Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma jigo a jam'iyyar PDP, Gbenga Olawepo-Hashim ya zargi jam'iyyar PDP din da yunkurin taimakin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sake cin zabe.
Ya bayyana hakane bayan da jam'iyyar PDP tace dan kudu zata tsayar takarar shugaban kasa inda Gbenga yace hakan yunkuri ne na taimakawa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ci zabe a 2027.
Ya bayyana hakane a yayin hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace masu neman a tsayar da dan kudu takarar shugaban kasar irin wanda suka raba kafa ne a PDP suna cewa, suna tare da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu amma kuma suna cikin PDP.