Bincike:Miliyan shidda ake biya a kullun a Asibitin da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kwanta a Landan, Da yawa ‘yan kasar Ingila basa iya kwanciya a asibitin saboda tsadar sa
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rasu a Asibitin London Clinic wanda da yawa da jin sunan sun dauka karamin Asibiti ne kamar yanda ake cewa Clinic a Najeriya.
London Clinic na daya daga cikin manyan Asibitoci masu zaman kansu a kasar Ingila wanda ke duba manya mutane da suka hada da 'yan siyasa daga kasashe daban-daban na Duniya.
Hatta Iyalin Masarautar Ingila na zuwa wanna Asibiti.
Ana biyan kudade masu tsada waja kwanciya a wannan Asibiti wanda shiyasa da yawa 'yan kasar basa iya zuwansa sai masu inshorar Lafiya me tsada sosai.
Wasu likitocin Najeriya dake aiki a kasar Ingila da jaridar Punchng ta zanta dasu sun bayyana irin kudaden da ake biya wajan kwanciya a wanan asibiti.
Daya daga ciki yace, Idan mutum zuwa kawai zai yi a dubashi a Asibitin ya koma gida ana ...








