Dokar-ta-ɓaci: Magoya bayan Fubara na gudanar da gangamin maida shi kan kujerarsa
Daruruwan magoya bayan dakatatcen gwamnan jihar River Siminalayi Fubara ne suka fito zanga-zanga a yau Talata, su na masu kira da a mayar da shi kan kujerar sa ta gwamna.
RFI ta rawaito cewa sun dai faro tattakin ne daga kan hanyar Aggrey, inda suke rike da alluna masu ɗauke da rubuce-rubucen cewa "muna tare da gwamna Sim Fubara", "muna buƙatar a maido mana da gwamnanmu da muka zaɓa", da dai sauransu.
Wannan ce dai gangami na baya-bayan nan da magoya bayan gwamnan suka gudanar, tun bayan dakatar da shi da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar 18 ga watan daya gaba.
A tattakin da su ke yi, sun riƙa rera wakoki da kade-kade da raye-raye tare da rera addu'o'in fatan a dawo da Fubara kan karagar sa ta mulkin jihar Rivers.
Dakatarwar dai ta shafi mataimakiyarsa Ngozi Odu da...








