Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Karya kake, ‘Yansanda suka gayawa basaraken Yashikira na jihar Kwara bayan da yace sabuwar Kungiyar masu ikirarin jìhàdì sun bayyana a karkashin masarautarsa

Karya kake, ‘Yansanda suka gayawa basaraken Yashikira na jihar Kwara bayan da yace sabuwar Kungiyar masu ikirarin jìhàdì sun bayyana a karkashin masarautarsa

Duk Labarai
Basaraken Yashirika na karamar hukumar Baruten jihar Kwara ya bayyana cewa maganar bullar 'yan Bindiga a karkashin masarautarsa gaskiyane. Yace amma abin takaici shine yanda jami'an tsaro ke karyata ikirarin nasu. Yace sun sayo motar da 'yan banga ke amfani da ita suna samar da tsaro a yankin nasu amma wadannan sabbin 'yan Bindiga masu suna Mamuda sun lalata motar. Yace kuma maganar kisan da 'yan Bindigar sukawa mutanensu gaskiya ne amma bai kai 15 ba da ake cewa inda yace kuma kowane bangare ya fuskanci asara. Saidai hukumar 'yansandan jihar ta bakin kakakinta,  SP Adetoun Ejire-Adeyemi tace maganar kisan mutane 15 da aka ce an yi karyane. Sannan yace sun bincika basu gano wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda me suna Mamuda ba. Yace suna baiwa mutane tabbacin samar da tsar...
Matsalar tsaron Najeriya bata yi munin da za’a ce mutane su fara tashi suna kare kansu ba>>Inji Gwamnan jihar Jigawa

Matsalar tsaron Najeriya bata yi munin da za’a ce mutane su fara tashi suna kare kansu ba>>Inji Gwamnan jihar Jigawa

Duk Labarai
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya bayyana cewa matsalar tsaron Najeriya bata yi munin da za'a fara cewa 'yan Najeriya su tashi su kare kansu ba. A hirar da aka yi dashi a Channels TV yace karfafa mutane su rika kare kansu daga harin 'yan Bindiga zai kai ga kara munana lamarin. Ya bayyana hakane biyi bayan maganar tsohon Ministan tsaro, T.Y Danjuma da yace mutane su rika tashi tsaye suna kare kansu daga masu kai musu hare-hare inda yace gwamnati ka dai ba zata iya ba Saidai Gwamna Umar Namadi yace Danjuma mutum ne wanda bai da wasa amma shi a nashi ganin Gwamnatin tarayya tana kokari duk da yake cewa ba duka matsalar take iya magancewa ba amma tana iya bakin kokarinta. Yace a kokarin magance matsalar rikicin makiyaya da manoma, yayi amfani da Sulhu wanda yace kuma an samu Na...
Ji yanda ‘yansanda suka kamo hadda matar aure a wani samame da suka kai Otal a Jihar Naija, Abinda mijin matar ya mata a ofishin ‘yansanda ya bayar da mamaki

Ji yanda ‘yansanda suka kamo hadda matar aure a wani samame da suka kai Otal a Jihar Naija, Abinda mijin matar ya mata a ofishin ‘yansanda ya bayar da mamaki

Duk Labarai
'Yansanda a jihar Naija sun kai samame a wani otal inda suka kama mutane maza da mata ciki hadda wata matar aure. 'Yansandan sun kai samame otal dinne bayan samun bayanan dake cewa 'yan sara suka na amfani da otal din a matsayin mafakarsu. Mataimakin Gwamnan jihar, Yakubu Garba ne ya bayar da umarnin kai samame maboyar 'yan sara sukan saboda yanda suka addabi mutane. Majiyar tace 'yansanda basu san matar na da aure ba, sai bayan da aka fara kiran dangin wadanda aka kama, mijinta ya je ofishin 'yansandan inda ya mata saki uku nan take. 'Yansandan sun ce basu san abinda ya kai matar auren otal din ba dan haka zasu gudanar da bincike
JIYA BA YAU BA: Kalli Shugaban Nijeriya, Alhaji Bola Ahmed Tinubu Da Uwargidansa Oluremi Tinuba A Shekarun Baya

JIYA BA YAU BA: Kalli Shugaban Nijeriya, Alhaji Bola Ahmed Tinubu Da Uwargidansa Oluremi Tinuba A Shekarun Baya

Duk Labarai
An yi hoton a farkon shekarun 1980's. Kuma Allah ya albarkaci wannan aure da 'ya'ya uku, sune; Zainab, Habibat da Olayinka. Sai dai kafin kafin auren sa da Oluremi, Tinubu yana da wasu 'ya'yan guda uku, wadanda ba Remi bace mahaifiyarsu. Sune; Kazeem Tinubu, Folashade Tinubu da Oluwaseyi Tinubu. Amma Allah Ya yi wa Kazeem rasuwa a birnin London cikin shekarar 2017.
Kai Duniya kalli Hotuna: Ji yanda aka iske gawar Sheriff Salifu da Budurwarsa, Blessing tsirara a dakinsa

Kai Duniya kalli Hotuna: Ji yanda aka iske gawar Sheriff Salifu da Budurwarsa, Blessing tsirara a dakinsa

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan a jihar Kogi tace ta iske gawar wani matashi me suna Sheriff Salifu da budurwarsa, Blessing tsirara a daki. Lamarin ya farune a karamar hukumar Akpan ranar Juma'a April 18, 2025 inda 'yansandan suka ce sun iske gawar masoyan tsirara a dakin matashin. Kakakin 'yansandan jihar, SP William Aya ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar ga manema labarai a ranar Asabar. Yace Blessing Adama dalibace a kwalejin ilimi ta jihar Kogi yayin da shi kuma Sheriff dan kasuwane. Yace sun kai gawar masoyan Mutuware kuma sun fara bincike kan lamarin.
Ji yanda ‘yansanda suka kama wani matashi da ya Kàshè mahaifinsa yayi gunduwa-gunduwa da gawarsa

Ji yanda ‘yansanda suka kama wani matashi da ya Kàshè mahaifinsa yayi gunduwa-gunduwa da gawarsa

Duk Labarai
'Yansanda a jihar Legas sun kama matashi dan kimanin shekaru 24 me suna Sowe Temidayo Igbekele bisa zargin kashe mahaifinsa, Babatunde Sowe Kayode da shekaru 60 a Unguwar Oshodi. An kama matashinne ranar Lahadi bayan wata 'yar uwarsu me suna Temidayo Akinola ta kai korafi ofishin 'yansandan. Lamarin ya farune ranar 17 ga watan Afrilu da misalin karfe 9:00 a.m. zuwa yanzu dai ba'a san dalilin dan na aikata abinda ya aikata ba. Tuni 'yansandan suka je suka tattara gawar mahaifin aka tafi bincike. Matashin da ya tsere bayan aikata wannan laifi an bi sahunsa an kamashi.
Fadar shugaban kasa zata saka Solar saboda tsadar kudin Wutar Lantarki da rashin tabbas na wutar

Fadar shugaban kasa zata saka Solar saboda tsadar kudin Wutar Lantarki da rashin tabbas na wutar

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu dake babban birnin tarayya Abuja ta ware Naira Biliyan 10 a cikin kasafin kudinta na shekarar 2025 dan hada sola. Hakan na zuwane yayin da kudin wutar Lantarki yake tashi sannan wutar ba samuwa take ba yanda ake bukata. Rahoton ya nuna za'a saka Solar a fadar shugaban kasar ta yanda fadar zata daina dogaro da wutar Lantarkin Najeriya ta koma amfani da hasken rana. 'Yan Najeriya da yawa da suka hada da kamfanoni tuni suka daina amfani da wutar Lantarkin inda suka koma amfani da hasken rana wajan samawa kansu wutar.