Saturday, December 13
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kada wanda muka sake jin ya biya masu Gàrkùwà da mutane kudin fansa>>Me baiwa shugaban kasa shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu ya gargadi ‘yan Najeriya

Kada wanda muka sake jin ya biya masu Gàrkùwà da mutane kudin fansa>>Me baiwa shugaban kasa shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu ya gargadi ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Babban me baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya gargadi 'yan Najeriya da cewa, kada wanda ya sake baiwa masu garkuwa da mutane kudin fansa. Ya bayyana hakane a Kaduna yayin da yake karbar wasu da aka yi garkuwa dasu amma jami'an tsaro suka kubutar dasu mutane 60. Nuhu Ribadu ya bayyana cewa, biyan masu garkuwa da mutanen kudin fansa yana kara karfafa musu gwiwa kuma hakanne zai sa su ci gaba da neman kudin fansar. Yace Gwamnati na iya bakin kokarinta na ganin ta bisu har maboyarsu ta yi maganinsu.
Rashin tsaro da kashe-kashe sun ragu da kashi 90% a Najeriya, in ji NSA, Ribadu

Rashin tsaro da kashe-kashe sun ragu da kashi 90% a Najeriya, in ji NSA, Ribadu

Duk Labarai
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya bayyana cewa Najeriya ta samu raguwar rashin tsaro da kashe-kashe da kusan kashi 90 a gwamnatin shugaba Bola Tinubu. Ribadu ya bayyana haka ne a garin Jos na jihar Filato a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da kwamandan rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Janar Folusho Oyinlola a ofishinsa, biyo bayan harin da yan indiga suka kai kan al’ummar Bokkos wanda ya yi sanadin mutuwar mazauna garin da dama. A cewarsa, gwamnatin shugaba Tinubu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan. “A cikin shekaru 1-10 da suka wuce, an rage yawan da kusan kashi 90 cikin 100 a kasarmu. "Muna da kididdigar ta shekarar 2022 da 2023, inda aka nuna cewa wadanda s...
Da wuya ka ga kasar da ta ci gaba a karkashin tsarin mulkin Dimokradiyya>>Inji Shugaban kasar Burkina Faso, Captain Ibrahim Traoré

Da wuya ka ga kasar da ta ci gaba a karkashin tsarin mulkin Dimokradiyya>>Inji Shugaban kasar Burkina Faso, Captain Ibrahim Traoré

Duk Labarai
shuganan kasar Burkina Faso, Captain Ibrahim Traore ya bayyana cewa da wuya ka ga kasar da ta samu ci gaba a karkashin tsarin Dimokradiyya. Ya bayyana hakane a fadarsa yayin kaddamar da wani shiri. Yace yawanci sai kasa ta samu daidaito ne sai daga baya ta koma kan tsarin Dimokradiyya. Yace amma ci gaba ana samunsa ne ta hanyar juyin juya hali.
An kama soja, Private Sadiq Sani bisa zargin fashi da makami

An kama soja, Private Sadiq Sani bisa zargin fashi da makami

Duk Labarai
' Yan sanda a jihar Naija sun kama soja, Private Sadiq Sani bisa zargin aikata Fashi da makami. An kamashi kuma da zargin cin zaafin wani dan kasuwa me suna Abdulrahman Salihu. Rahoton yace, Soja Sadiq ya je shagon Abdulrahman Salihu da sallah inda ya sayi kaya, sai yace a bashi account Number ya tura kudi. Saidai bayan da ya karbi account number din dan kasuwar yayi zargin wani abu inda yace ba zai bashi kayan ba sai ya ga Alert. Daga nan ne sai sojan ya aika da alert din karya. Ko da dan kasuwar ya ga haka sai rikici ya barke tsakaninsu inda sojan ya fitar da wuka ya yanki dan kasuwar sannan ya tsere. An sanar da 'yansanda inda suka bi sojan har gidansa dake Limawa a garin Minna suka kamashi. An kaiwa hukumar soji rahoton abinda sojan ya aikata inda wani babba...
Kalli Bidiyo: Allah ya min Arziki ta yanda babu dakin da zai iya dauke yawan rigunan da nike dinkawa a shekara>>Sheikh Kabir Gombe ya fada bayan Tonon Sililin da Dan Bello yayi

Kalli Bidiyo: Allah ya min Arziki ta yanda babu dakin da zai iya dauke yawan rigunan da nike dinkawa a shekara>>Sheikh Kabir Gombe ya fada bayan Tonon Sililin da Dan Bello yayi

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Kabir Gombe ya bayyana irin Arzikin da Allah ya masa. Malam ya bayyana hakane a wani bidiyo da ya bayyana inda aka ganshi yana wa'azi. Yace riguna da suke ta dinkawa, inda za'a tarasu babu dakin da zai daukesu, yace amma ba ba konawa suke ba, bayarwa suke yi ga bayin Allah inda yace a shekara yakan yo kyauta da riguna 100. Kalli Bidiyon anan: https://www.tiktok.com/@hayatudden.jafar/video/7490612201175141638?_t=ZM-8vM1sX1l7A6&_r=1 Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da Dan Bello ya fitar da bayanai kan zargin shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau da aikata ba daidai ba da dukiyar gina azuzuwa.
Farashin ɗanyen man fetur ya yi mummunar faɗuwa a kasuwar duniya wadda rabon da aka irinta tun shekaru 5 da suka gabata, kudin shigar Najeriya zasu samu Gibi

Farashin ɗanyen man fetur ya yi mummunar faɗuwa a kasuwar duniya wadda rabon da aka irinta tun shekaru 5 da suka gabata, kudin shigar Najeriya zasu samu Gibi

Duk Labarai
Farashin ɗanyen man fetur samfurin Brent - wanda aka fi yawan ƙayyade farashi da shi a duniya - ya yi faɗuwa mafi muni cikin shekara biyar. Faɗuwar da kusan kashi 3.2 cikin 100 - zuwa dala 63.49 kowace ganga - ta faru ne a yau Litinin da misalin ƙarfe 11:00 agogon Najeriya da Nijar. Rabon ya yi irin faɗuwar tun watan Afrilun 2021. Shi ma samfurin West Texas Intermediate (WTI) ya faɗi zuwa kashi 3.58, kamar yadda kamfanin labarain na Reuters ya ruwaito. Faɗuwar farashin ta faru ne sakamakon sanarwar da Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar ta ƙaƙaba wa dukkan ƙasashen duniya ƙarin harajin shifgar da kaya ƙasarsa. Hakan ya sa samfurin Brent ya faɗi da kashi 10.9 cikin 100, yayin da shi ma WTI ya faɗi da 10.8.
Saudiyya ta ayyana ranar da masu aikin Umrah za su fice daga kasar

Saudiyya ta ayyana ranar da masu aikin Umrah za su fice daga kasar

Duk Labarai
Ma'aikatar aikin Hajj da Umrah ta Saudi Arabiya ta kebe ranar 1 ga watan Dhul Qada, wadda ta zo dai-dai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ya shiga kasar domin yin Umrah ya fice. Ma'aikatar ta ce ta dauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa. Cikin wata sanarwa, ma'aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi dai-dai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga kasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita. Ma'aikatar ta jaddada cewa duk wanda aka samu ya ci gaba da zama a kasar har ya wuce lokacin da kebe, to ko shakka babu ya saba ka'ida sannan kuma zai fuskanci hukunci. Daga nan ta bukaci mutane da ma kamfanonin da ke shirya zuwa aikin Umrah da su kiyaye da wadannan lokuta da aka kay...
Gwamnonin APC sun kai wa Muhammadu Buhari ziyara

Gwamnonin APC sun kai wa Muhammadu Buhari ziyara

Duk Labarai
Kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya karkashin jagorancin shugabanta gwamnan Imo Sanata Hope Uzodinma, ta kai wa tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyarar ban girma a gidansa da ke Kaduna. Bayan shugaban kungiyar, sauran gwamnonin da suke cikin tawagar ma su ziyarar sun hada da gwamnan Kaduna da na Gombe da Kwara da Nasarawa da Ebonyi da Kebbi da Edo da Kogi da Ondo da Ekiti da kuma Benue. Sauran 'yan tawagar sun hadar da mataimakin gwamnan Jigawa da ministan kasafin kudi da tsare-tsare.
Najeriya da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar yaƙi da miyagun ƙwàyòyì

Najeriya da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar yaƙi da miyagun ƙwàyòyì

Duk Labarai
Najeriya da Saudi Arabiyya sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimta domin karfafa yaki da hada-hadar kwayoyi. A ranar Litinin Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta Najeriya da kuma Hukumar da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Saudiyya GDNC, suka sanya hannu kan yarjejeniyar a Riyadh. Cikin wata sanarwar da daraktan yada labarai na hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ya ce kasashen biyu sun amince su kara karfafa yaki da fataucin miyagun kwayoyi a dukkan iyakokinsu. Da ya ke magana a wajen sanya hannu kan yarjejeniyar, shugaban hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa, mai ritaya, ya ce dukkan kasashen sun jima suna yin hadaka da bangarori daban daban. Marwa, wanda ya samu rakiyar darakta a sashen bincike da gudanarwa na hukumar, Ahmed Ning...
Mun san ana cutar mu, ba sai wani dan iska Munafiki Dan Bello ya fito ya gaya mana ba>>Inji Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe

Mun san ana cutar mu, ba sai wani dan iska Munafiki Dan Bello ya fito ya gaya mana ba>>Inji Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Babban malamin Addinin Islama, Sheik Adam Muhammad Albany Gombe ya soki Dan Bello kan labarin zargin daya wallafa na cewa, an baiwa shugaban kungiyar Izala, Sheik Bala Lau kudin gina Azuzuwan makarantu daga Gwamnatin tarayya amma bai gina ba. Malam ya bayyana Dan Bello a matsayin wanda yake can kasar waje yake gayawa mutane cewa wai ana cutarsu inda yace 'yan Najeriya sun san ana cutarsu ba sai wani Dan Bello ya fito yana gaya musu ba. Hakanan ya gargadi Dan Bello da cewa zasu ma...