Dan Datti Baba Ahmad wanda shine ke da jami'ar Base ta Abuja ya kammala Karatu daga jami'ar Queen Mary University London dake kasar Ingila.
Lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu ke cewa me yasa bai yi karatu a jami'ar babansa dake Najeriya ba.
Hukumomi a jihar Katsina sun kama matashi me suna Anas Muhammad Game saboda yayi zanga-zanga kan matsalar tsaron dake damun jihar.
An kamashi ne kwanaki 6 da suka gabata a wajan zanga-zangar lumana ta nuna rashin jin dadin matsalar tsaron dake damun jihar.
Tun wancan lokacin dai Muhammad Game ke tsare ba tare da Beli ba.
Da yawa sun hau kafafen sada zumunta inda suke Allah wadai da ci gaba da tsareshi da neman a sakeshi da gaggawa.
Dan majalisar tarayya karkashin jam'iyyar ADC, Leke Abejide ya bayyana cewa ba zasu bar jam'iyyar su a hannun baki ba da suka musu kaka gida ba.
Yace zai hada kai da 'yan Asalin jam'iyyar ADC din dan su kwato jam'iyyar daga hannun wanda suka musu kaka gida.
Hakan na zuwane kwana daya bayan da tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, Nafiu Bala daga jihar Gombe ya bayyana kansa a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na kasa na riko.
A wani labarin me kama da wannan, Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya bayyana cewa ba zai koma jam'iyyar ADC ba.
Malamin Addinin Islama, Sheikh Kabir Gombe ya bayyana cewa a lokacin da aka kirkiri Najeriya, baya tsammanin shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu ya balaga.
Ya bayyana cewa amma kuma yanzu shine shugaban kasa, Shine Ja gaba ko ka yadda ko baka yadda ba.
Malam ya bayyana cewa, dole a hakura sai sanda mulkinsa ya kare.
Ya kawo wannan misali ne ga wasu malaman darika a baya dake cewa su yarane da suke sukar Darika.
https://www.tiktok.com/@saleemyusufmuhammadsambo/video/7533765736884391224?_t=ZS-8yXIaBqYGGX&_r=1
Malamin Addinin Islama, Ibrahim Matayassara ya bayyana cewa, 'yan nanaye na Kannywood sun fi masa Shehunan Darika.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa dake ta yawo a kaffen sada zumunta.
Malam yace kuma Marigayi, Sheikh Abubakar Mahmood Gumi yafi sauran manyan Shehunan Darika.
https://www.tiktok.com/@assiddiqassalafyrlemo/video/7533755445920435462?_t=ZS-8yXH43efOxF&_r=1
ZABEN 2027: Ina Da Tabbacin Cewa Kafin 12 Na Rana Tinubu Ya Lashe Shugaban Kasa, Cewar Nazir Ɗanhajiya.
Shugaban ƙungiyar wayar da kan matasa reshen Jihar Kano kuma Fitaccen Furodusan a masana'antar Kannywood, Nazir Ɗanhajiya ya bayyana cewa yana da tabbacin cewa kafin 12 na rana shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaɓensa 2027.
Ɗanhajiya, wanda ya bayyana haka ta cikin wata tattaunawarsa da Dokin Ƙarfe TV, ya ƙara da cewa kaso 90 na ƴan Najeriya masoya Tinubu ne.
"Idan ka duba za ka ga kashi 1 ne zuwa 5 ake ba wa na Data suke Furofaganda a Social Media ba wai masoya ƙasar ba ne. Mu ne muka san masu zaɓe, mu ne muke tare da masu zaɓe". Inji shi.
Nazir ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su mara wa Tinubu baya ya yi shekara 8 ɗinsa domin gyara da ci gaban da yake kawo w...
Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Nuhu ta bayyana cewa, akwai sanda ake ta son aurenta amma bata maida hankali ba.
Tace amma yanzu ta na son ta yi aure kamin komawa ga mahaliccinta.
Ummi ta bayyana hakane a sabuwar hirar da BBChausa ta yi da ita inda tace ko makiyinta bata son ya shiga wahala rayuwar data shiga.
Saidai Ummi tace ida kuma Allah ya kaddaro cewa a haka zata mutu ba tare da yin aure ba, zata rungumi kaddararta.
https://www.tiktok.com/@arewa.update8/video/7533855056240610566?_t=ZS-8yXEjKhL2wq&_r=1
An fara jin halin da Ummi ke ciki nw bayan hirar da Hadiza Gabon ta yi da ita a shirin ta na Gabon Show da ta ke yi a YouTube channel dinta.
https://www.tiktok.com/@arewa.update8/video/7533854497441991992?_t=ZS-8yXFBpDuDFx&_r=1
Da yawa dai sun...
Bidiyo ya nuna gwamnan jihar Naija, Umar Bago Yana rawa da wakar Rarara wadda yawa shugaban kasa ta Omologo.
A Bidiyon an ga yanda Gwamnan ya taka rawa sosai.
Wasu sun yaba inda wasu kuma suka kushe.
https://www.tiktok.com/@umarfaruq.scanty/video/7533753499444628742?_t=ZS-8yXDzHoNHNp&_r=1
Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan wata za ta fara yin rajistar masu zaɓe a faɗin ƙasar gabanin zaɓukan 2027.
Cikin wata sanarwa da INEC ta wallafa a shafinta na X ranar Juma'a, ta ce za ta fara rajistar masu zaɓen ta yanar gizo a ranar 18 gawatn Agustan da muke ciki.
Hukumar zaɓen ta kuma saka ranar Litinin 25 ga watan Agustan a matsayin ranar fara rajistar a ofisoshinta da ke ƙananan hukumomi da sauran wuraren da ta ware don gudanar da aikin.
INEC ta ce za a riƙa gudanar da aikin ne daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana a ranakun Litinin zuwa Juma'a.
Kan hakan ne hukumar ta buƙaci waɗanda ba su da rajistar su yi amfani da damar wajen mallakar rajistar.
Hukumar ta ƙayyade shekara 18 a matsayin mafi ƙanƙantar shekarun yin rajistar zaɓe a Najeriya....
Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Bin Uthman ya bayar da labarin yanda aka aika masa Kiristoci masu bushara har su biyu dan su mayar dashi kirista.
Malam yace har gida suka sameshi.
Ya jawo hankalin iyaye su kula da 'ya'yansu.
https://www.tiktok.com/@voice_of_sahaba/video/7533616957417983288?_t=ZS-8yWdSYiTGVd&_r=1