Sheikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi Ya Jagoranci Tawagar Kungiyar Mu’assasa Domin Yiwa Gwamna Raɗɗa Ta’aziyyar Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari
Sheikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi Ya Jagoranci Tawagar Kungiyar Mu'assasa Domin Yiwa Gwamna Raɗɗa Ta'aziyyar Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari.
Tawaga ta musamman daga gidauniyar Shehun Malamin nan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibrahim Ɗahiru Usman Bauchi, sun ziyarci Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON, domin yi mashi ta'aziyyar rasuwar Tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Tawagar ƙarƙashin jagorancin ɗan Shehin Malamin Ɗariƙar Tijjaniyya Khalifa Ibrahim Ɗahiru Bauchi sun ziyarci Gwamnan ne a gidan gwamnatin jihar Katsina a yau Lahadi 20 ga watan Yuli 2025.
Da yake gabatar da jawabin dalilin ziyarar ta su Khalifa Ibrahim Ɗahiru Bauchi, ya bayyana sun zo ne a madadin mahaifin nasu domin yiwa iyalai, Gwamnan, da kuma a al'ummar jihar Katsina t...








