Dangantaka ta yi tsami sosai tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da na Israela, Benjamin Netanyahu, shi kuma Trump baya son raini dan haka yace zai amince da kasar Falasdinawa ya ga tsiya
Rahotanni sun bayyana cewa, dangantaka ta yi tsami sosai tsakanin shugaban kasar Amurka Donald Trump da na Israela, Benjamin Netanyahu.
Tun da farko dai hakan ya bayyana ne bayan da kasar Amurka ta amince ta taimakawa kasar Saudiyya mallakar tashar makamin Kare dagi, Nokiliya, ba tare da saka kasar Israela a cikin maganar ba.
Kasar Israyla a baya itace take shigewa Amurka gaba akan kowane lamarin da ya shafi hulda da kasashen Gabas ta tsakiya, saidai a yanzu gashi an yi maganar makamashin nokiliya tsakanin Amurka da Saudiyya babu ita.
Hakanan Amurka ta yi sulhu da mayakan kasar Yemen wanda shima ba'a saka kasar Israela cikin tattaunawar ba, a wasu rahotanni ma ance Amurkar bata ce kada mayakan Yemen su kaiwa kasar Israela hari ba a tattaunawar, ita dai kada a taba kadarorin ta.
...








