Thursday, March 26
Shadow

Author: Bashir Ahmed

An Hango ‘yan bìndìgà 300 a kan babura dauke da muggan makamai suna tafiya daga Zamfara zuwa jihar Naija

An Hango ‘yan bìndìgà 300 a kan babura dauke da muggan makamai suna tafiya daga Zamfara zuwa jihar Naija

Duk Labarai
Akalla mutane 300 da ake zargin ‘yan bindiga ne, dauke da muggan makamai Akan babura, an hango su suna ketare hanyar Kontagora zuwa Minna, tsakanin Kampanin Bobby da Wamba a Karamar Hukumar Mariga ta Jihar Neja. Lamarin ya faru ne da rana tsaka, inda hakan ya sa direbobi da fasinjoji suka tsere domin kare rayukansu. Wani ganau ya bayyana cewa, an yi imanin cewa ‘yan bindigar sun fito ne daga Jihar Zamfara, kuma suna tafiya cikin 'yanci zuwa Karamar Hukumar Mashegu ba tare da gamuwa da jami’an tsaro ba. Wani direba da ya shaida lamarin ya ce babu ko da jami’in tsaro guda daya a lokacin da lamarin ke faruwa. Shugaban Karamar Hukumar Mariga, Abbas Kasuwa Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da aka tuntube shi. Ya bayyana cewa an tura hadin gwiwar jami’an tsaro zuwa yankin d...
Duk Wanda Ya Yi Silar Haduwata Da Adam A. Zango, Na Yi Alkawarin Zan Ba Shi Tukwicin Naira Dubu Dari Biyar, Inji Matashi Sharhabilu Musa Malumfashi

Duk Wanda Ya Yi Silar Haduwata Da Adam A. Zango, Na Yi Alkawarin Zan Ba Shi Tukwicin Naira Dubu Dari Biyar, Inji Matashi Sharhabilu Musa Malumfashi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Duk Wanda Ya Yi Silar Haduwata Da Adam A. Zango, Na Yi Alkawarin Zan Ba Shi Tukwicin Naira Dubu Dari Biyar, Inji Matashi Sharhabilu Musa Malumfashi
Shugaban APC, Ganduje yayi magana bayan cece-kuce yayi yawa kan Bidiyon da aka ga dansanda na gyara masa takalmi

Shugaban APC, Ganduje yayi magana bayan cece-kuce yayi yawa kan Bidiyon da aka ga dansanda na gyara masa takalmi

Duk Labarai
A jiyane Bidiyo ya bayyana inda aka ga Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a tsaye, dansandansa ya duka yana daure masa takalmi. Bidiyon ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda akaita bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai. Da yake mayar da martani kan lamarin ta bakin kakakinsa, Aminu Dahiru Ahmad, Ganduje yace wasu ne dake son jawo cece-kuce da kawo rudani a tsakanin al'umma suka fitar da Bidiyon. Yace Ganduje an sanshi mutum ne me haba-haba da mutane sannan kuma yana da kyakkyawar alaka tsakaninsa da masu masa aiki shiyasa aka ga abinda dansandan yayi.
Idan Namiji ya miki Ba daidai ba kina son yin maganinshi, kawai ki kalamai sharrin cewa ya miki Fyàdè>>Inji Wannan matar

Idan Namiji ya miki Ba daidai ba kina son yin maganinshi, kawai ki kalamai sharrin cewa ya miki Fyàdè>>Inji Wannan matar

Duk Labarai
Wata mata ta dauki hankula bayan da ta bayyana cewa hanya mafi sauki ta yin maganin maza itace kala musu sharrin fyade. Ta bayyana hakane ta shafinta na sada zumunta inda abin ya baiwa mutane mamaki. A kwanannan ne dai Sanata Natasha Akpoti ta zargi kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio da nemanta da lalata.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yace zai fara baiwa ‘yan Cirani da basu da takardu Dala Dubu daya kyauta kowannensu dan su fice su koma kasashensu

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yace zai fara baiwa ‘yan Cirani da basu da takardu Dala Dubu daya kyauta kowannensu dan su fice su koma kasashensu

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, maimakon ya rika aika jirage suna mayar da mutane kasashensu, zai fara baiwa 'yan Cirani dala dubu 1 dan su rika biyan kudin jirgi suna komawa kasashensu. Ma'aikatar tsaro ta Department of Homeland Security ce ta bayyana hakan a sanarwar da ta fitar inda tace duk dan cirani da bashi da takardun zama a kasar da ya yadda zai koma kasarsa, za'a bashi dala $1000. Hukumar tace wannan ce hanya mafi sauki wadda kuma ba sai an kama mutum an wulakantashi ba kamin ya bar kasar. Tace kamawa da tsarewa da mayar da mutane kasarsu yanasa kasar ta Amurka kashe Dala $17,000 akan kowane mutum. Dan haka baiwa mutane dala $1000 ya fi sauki idan sun yadda su koma kasarsu.
Kalli Bidiyo:Ni fa banda lokacin da zan tsaya ina rokon Allah ya bani Miji>>Inji Wannan matashiyar

Kalli Bidiyo:Ni fa banda lokacin da zan tsaya ina rokon Allah ya bani Miji>>Inji Wannan matashiyar

Duk Labarai
Wata matashiya ta baiwa mutane mamaki bayan da ta fito take bayyana cewa, bata da lokacin tsayawa tana rokon Allahbya bata miji. Bidiyon maganarta ya watsu sosai inda akai ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai. https://www.tiktok.com/@boh_360_hub/video/7500652540866874629?_t=ZM-8w7cKkjSc1n&_r=1 Hakan na zuwane yayin da wasu matan ke neman Allah ya hadasu da maza na gari.
Ali Nuhu yayi Tsokaci kan wannan hoton na Ango da Amarya, Rarara da A’isha Humaira

Ali Nuhu yayi Tsokaci kan wannan hoton na Ango da Amarya, Rarara da A’isha Humaira

Duk Labarai
A jiyane bayan Aure, Dauda Kahutu Rarara ya saki sabbin hotuna tare da Amaryarsa, A'ishatulhumaira. Hotunan sun kayatar sosai ta inda mutane suka yaba musu musamman ma ganin cewa, Sai bayan aure ne Rarara da Amaryarsa suka saki hotunan, abinda ba kasafai aka cika gani ba. Ali Nuhu ma ba'a barshi a baya ba, ya saka hoton inda yace yana kara taya ma'auratan murna.
Muguntar da El-Rufai yayi a baya ce take binsa saboda Alhaki kwikwiyo ne, Kuma ba zai yi nasara ba, saboda mutane da yawa basu yadda dashi ba saboda mayaudari ne kuma maciyin amanane>>Buba Galadima

Muguntar da El-Rufai yayi a baya ce take binsa saboda Alhaki kwikwiyo ne, Kuma ba zai yi nasara ba, saboda mutane da yawa basu yadda dashi ba saboda mayaudari ne kuma maciyin amanane>>Buba Galadima

Duk Labarai
Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa, Tsohon gwamnan Kaduna, Malan Nasiru Ahmad El-Rufai ba zai yi nasara ba a kokarin da yake na hada kan 'yan jam'iyyar Adawa da kuma kalubalantar Gwamnatin Tinubu a zaben shekarar 2027. Buba Galadima ya bayyana hakane a wata hira da jaridar Punchng ta yi dashi wadda shafin hutudole ya bibiya. Yace El-Rufai ya saba ya shiga jam'iyya wadda me karfi ce tana kan hanyar Nasara shima ya samu Nasara. Yace amma yanzu da yake kokarin farowa daga farko a yanzu ne zai gane wahalar da ake sha wajan gina jam'iyya da siyasa. Yace amma matsalar El-Rufai itace bashi da alaka me kyau da mutane, ya taka mutane da yawa kuma mayaudari ne maci yin amanane dan haka babu wanda ya yadda dashi kuma dalili kenan da yasa ba zai yi nasara ba. Yace El-Rufai yayi maga...
Za’a samu gagarumin faduwar farashin man fetur a Najeriya

Za’a samu gagarumin faduwar farashin man fetur a Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa ana tsammanin gagarumin faduwar farashin Man fetur da gas a Najeriya. Hakan ya biyo bayan faduwar farashi danyen man fetur a kasuwar Duniya. 'Yan kasuwar man fetur na Najeriya sun tabbatarwa da kafar Punchng hakan saidai sun ce ba za'a ga faduwar farashin da sauri ba har sai idan farashin danyen man fetur din ya ci gaba da faduwa. A ranar Litinin, Hutudole ya samu cewa, farashin Danyen Man fetur na Brent ya kai dala $59.80 akan kowace ganga