DA DUMI-DUMI: Abubakar Malami da El-Rufai sun yi wata ganawar sirri.
Kuna ganin tsohon Gwamnan da tsohon ministan Shara'ar suna da tasirin da zai tashi hankalin Gwamnatin Tinubu ko APC?
Wani matashi ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta bayan da yayi ikirarin cewa bai taba samun farin ciki kamar a zamanin mulkin Tinubu ba.
Yace da mata daya gareshi, amma yanzu ya kara aure, hakanan sannan kuma kasuwarsa ta kara habaka.
Yace a karamar hukumar Jibia yake zasu tafi gida aka ce su bari sai da magariba, alamar cewa tsaro ya samu.
https://twitter.com/Realoilsheikh/status/1919463062735577586?t=91zXI0pWCdlgjk8cTFNrcQ&s=19
Najeriya ce kasa ta daya a Afrika sannan ta Biyu a Duniya wajan yawan yaran da basa samun Abinci me gina jiki kamar yanda hukumar kula da yara ta majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta bayyana.
Wakiliyar UNICEF, Nemat Hajeebhoy ce ta bayyana hakan a wajan shirin magance matsalar rashin abinci me gina jiki da ake shiryawa yaran jihohin Adamawa, Borno, da Yobe.
Tace akwai yara guda 600,000 dake fama da matsalar rashin abinci me gina jiki kuma kusan rabinsu na fuskantar kara tsanantar matsalar.
Tace yaran dake fama da matsalar matsananciyar rashin abinci me gina jiki zasu iya mutuwa.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a kokarin karfafa tattalin arzikin Najeriya ya hana sayo kayan da ake iya yinsu a cikin gida daga kasashen waje.
Majalisar zartaswa tuni ta amince da wannan kudirin a zamanta na ranar Litinin inda aka bayyana cewa an yi hakanne dan karfafa masana'antun gida Najeriya.
Da yake magana ga manema labarai bayan zaman, ministan yada labarai, Mohammed Idris yace an dauki wannan mataki ne dan karfafa amfani da kayan da aka kerasu a cikin gida.
Yace sun kwaimwayi shugaban kasar Amurka, Donald Trump ne a kokarin da yake na karfafa masana'antun kasarsa ta Amirka
Wannan wani Bidiyo ne da tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta wallafa a shafinta na Tiktok.
https://www.tiktok.com/@hadizaaliyugabon/video/7500697867263298838?_t=ZM-8w6oK1bxD66&_r=1
Saidai da yawa sun ce basu gane ta ba da farko sai da suka nutsu.
Ana ta caccakar wani ɗansanda saboda ya ɗaura wa Ganduje takalmi.
Wani ɗansanda na shan matsin lamba a kafafen sada zumunta bayan da aka gan shi ya na ɗaura wa Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC mai mulki, igiyar takalmi.
A cikin wani bidiyo da ya karade intanet, an ga Ganduje tsaye yayin da dansandan da ba a bayyana sunansa ba ya durƙusa ya na ɗaura masa igiyar takalmi.
Bidiyon da ya bayyana a yanar gizo ranar Litinin ya janyo ce-ce-ku-ce daga jama’a.
Wasu sun yi mamakin yadda dan sanda da ke cikin kayan aiki zai aikata irin wannan abu, yayin da wasu kuma suka ce wata kila Ganduje ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar dan sandan.
Fadar Shugaban Kasa ta karyata maganganun Adesina kan ci gaban Najeriya
Fadar Shugaban Ƙasa ta karyata maganganun da aka danganta wa Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Akinwumi Adesina, inda ya ce halin da ‘yan Najeriya ke ciki a yanzu ya fi na shekarar 1960 muni.
Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin yada labarai , ya wallafa a shafinsa na X cewa Adesina ya dogara da wasu ƙididdiga “da ba su dace da bayanan da ake da su ba.”
A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, “Babu wani mai lura da gaskiya da zai ce Najeriya ba ta samu ci gaba ba tun daga 1960. Yanzu haka, yayin da muke jiran sabon tsarin ƙididdigar GDP daga NBS, za mu iya cewa ba tare da jayayya ba cewa ya ninka na lokacin 'yancin kan mu sau 50, ko ma sau 100.”
Onanuga ya zargi Adesina da yin ...
Fiye da ɗalibai miliyan 1.5 sun samu ƙasa da maki 200 a jarrabawar UTME ta 2025.
Daga cikin ɗalibai 1,955,069 da suka zauna jarrabawar UTME ta shekarar 2025, fiye da miliyan 1.5 daga cikinsu sun samu ƙasa da maki 200 a jarrabawar.
VANGUARD ta rawaito cewa rahoton kididdiga na sakamakon UTME na shekarar 2025 da Hukumar Jarrabawa ta JAMB ta fitar a ranar Litinin ya nuna cewa ɗalibai 420,415 kawai ne suka samu sama da maki 200 a wannan jarrabawar.
A yayin da ɗalibai 4,756 suka samu sama da maki 320, kimanin ɗalibai 7,658 ne suka samu tsakanin maki 300 da 319.
Akwai haɗari kwanciya da waya a ƙarƙashin matashi-kai - Kwararre.
Wani ƙwararre mai ba da shawara kan harkokin fasaha a TMB Tech, Akin Ibitoye, a yau Litinin ya gargadi ‘yan Najeriya game da lafiya da kuma illolin da ke tattare da kwanciya da wayoyin hannu a karkashin matashin kai ko a gefen gadajensu.
Da ya ke magana a shirin Brief Morning a gidan Talabijin na Channels, Ibitoye ya jaddada cewa na'urorin tafi da gidanka na iya hana barci, da shafar lafiyar kwakwalwa da kuma haifar da hadarin gobara saboda tsananin zafi da batirin lithium-ion ka iya haddasa wa.
"Kada ku kwana da wayar salula a ƙarƙashin matashin ku,” in ji shi. Ba ku sani ba."
Kafar mu kafar Kwankwaso a siyasa - Abba Gida Gida
Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya sake jaddada kudurinsa na mara wa Sanata Rabiu Kwankwaso baya a dukkan harkokin siyasa.
Gwamna Yusuf ya sha alwashin bin tafarkin siyasar Kwankwaso, yana mai cewa, "duk inda ya dosa a siyasa, magoya bayansa za su bishi."
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi ga kansiloli 484 daga kananan hukumomi 44 a fadar gwamnati ranar Lahadi.
Abba ya kuma karyata zarge-zargen da tsohon sakataren gwamnatin jiha, Baffa Bichi, ya yi masa, inda ya kira shi da "makaryaci marar kunya," yana mai bayyana zarge-zargen a matsayin karya kuma abin dariya.
Gwamnan ya fi mayar da hankali kan zargin cewa Kwankwaso na karɓar Naira biliyan biyu duk wata daga gwamnatin jihar Kano, yana mai cewa wannan zar...