Jami’ar MAAUN ta rufe gidajen kwanan ɗalibai mata bisa zargin aikata rashin tarbiyya
Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN) ta ba da umarnin gaggawa na rufewa tare da janye amincewa da gidajen kwanan dalibai mata na Al-Ansar Indabo da ke Hotoro da titin UDB a birnin Kano.
Wata sanarwa daga Mataimakin Shugaban Jami’ar mai kula da Rayuwar Dalibai, Dr. Hamza Garba, a ranar Lahadi, ya bayyana cewa wannan matakin rufe gidajen kwanan wani bangare ne na kokarin da jami’ar ke yi domin tabbatar da kwanan dalibai cikin aminci, tsaro da tsafta, da kuma ci gaba da nuna matsayinta na kin yarda da duk wata dabi’a ta lalata daga kowanne ɗalibi.
“Na samu umarni daga hukumar gudanarwa na rubuta wannan sako don sanar da iyaye da dalibanmu masu daraja cewa jami’a ta janye amincewarta da GIDAJEN KWANAN DALIBAI MATA NA AL-ANSAR INDABO da ke titin ...








