Gwamnatin taraiya ta umurci WAEC da NECO su koma zana jarrabawa ta na’ura mai ƙwaƙwalwa
Gwamnatin taraiya ta umurci WAEC da NECO su koma zana jarrabawa ta na'ura mai ƙwaƙwalwa.
Gwamnatin Taraiya ta umurci Hukumar Shirya Jarabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) da Hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO) da su fara gudanar da dukkan jarabawarsu ta hanyar amfani da Kwamfuta (CBT) daga shekarar 2026.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan yayin da yake sa ido kan jarabawar da ake gudanarwa tare da jami'an JAMB, a Bwari, ranar Litinin.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa fiye da dalibai miliyan biyu ne suka yi rajistar jarabawar da ake gudanarwa a fiye da cibiyoyi 800 a fadin kasar nan.
Alausa ya bayyana cewa daga watan Nuwamba mai zuwa, WAEC da NECO za su fara gudanar da jarabawarsu ta bangaren tambayoyi (objective) ta hanyar CBT.
A ...








