Sunday, March 22
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Yanda wani matashi ya hau Saman karfen Sabis yace ba zai sauko ba sai Atiku Abubakar ya biyashi bashin Naira Miliyan 15 da yake binsa ko kuma ya kàshè kansa

Kalli Yanda wani matashi ya hau Saman karfen Sabis yace ba zai sauko ba sai Atiku Abubakar ya biyashi bashin Naira Miliyan 15 da yake binsa ko kuma ya kàshè kansa

Duk Labarai
ina Bin Atiku Abubakar Bashi Naira miliyan 15 yakasa Binaya, Wani Matashi yayi Barazanar Kashe kansa Matuƙar Atiku Abubakar Bai Biya Shi Bashinsa Ba Wani Mutum Ya Hau Hasumiyar Sadarwa Don Neman Atiku Abubakar ya Biya shi Bashin Naira Miliyan 15. Da yake binsa. A wani lamari da ya jawo hankalin jama'a, wani mutum ya hau saman wata hasumiyar sadarwa a Najeriya, yana barazanar kashe kansa a matsayin matakin nuna fushi. Mutumin mai suna Musa Inuwa, ya ƙi saukowa daga hasumiyar duk da kokarin da ake yi na shawo kansa. Ya nace cewa sai an tilasta wa tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, biyan sa Naira miliyan 15 da yake ikirarin cewa ana binsa sakamakon wani aiki da ya gudanar masa. Rahotanni sun nuna cewa ya bayyana a fili cewa ba zai sauko ba sai dai idan 'yan sanda su...
TURKASHI: Wani Matashi da ya Sadaukar da ransa da rayuwarsa ga, Sen. Barau I jibrin

TURKASHI: Wani Matashi da ya Sadaukar da ransa da rayuwarsa ga, Sen. Barau I jibrin

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani Matashi da ya Sadaukar da ransa da rayuwarsa ga, Sen. Barau I jibrin. Shin zaka iya irin Wannan Sadaukarwa ga Dan Siyasa ?
Kalli Bidiyo: Abin Kunya Yanda aka dauke wuta yayin da me kamfanin Facebook ya zo Najeriya yana tsaka da ganawa mutane

Kalli Bidiyo: Abin Kunya Yanda aka dauke wuta yayin da me kamfanin Facebook ya zo Najeriya yana tsaka da ganawa mutane

Duk Labarai
Me kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg ya zo Najeriya inda yake jin ta bakin mutane kan shafin nasa. A yayin da wani yake ganawa dashi, kwatsam sai aka dauke wutar lantarki. Lamarin yayi matukar bayar da mamaki da daukar hankali. https://twitter.com/instablog9ja/status/1916179627841630481?t=GGfbmOe37A3WLqa3ezaNbQ&s=19 Da yawa dai sun bayyana lamarin da Abin Kunya.
Kalli Bidiyo yanda aka samu wani shakiyyi yasa Shugaban kasa, Tinubu na rera wakar Hamisu Breaker ta Amanata wadda Hisbah ta Haramta

Kalli Bidiyo yanda aka samu wani shakiyyi yasa Shugaban kasa, Tinubu na rera wakar Hamisu Breaker ta Amanata wadda Hisbah ta Haramta

Duk Labarai
An samu wani shakiyyi ya hada hoton Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yana rera wakar Hamisu Breaker ta Amanata wadda Hisbah ta jihar Kano ta Haramta Sauraro. Da yawa sun bayyana mabanbanta ra'ayoyi akan hakan. https://www.tiktok.com/@prince_abduoll0/video/7497320735979916550?_t=ZM-8vsfxMU9TpV&_r=1 Wakar dai ta samu watsuwa sosai fiye da yanda ake tsamani bayan haramcin Hisbah.
Kalli Bidiyon Lamine Yamal na chasewa da wakar Shake Body ta Skales bayan lashe kofin Copa Del Rey

Kalli Bidiyon Lamine Yamal na chasewa da wakar Shake Body ta Skales bayan lashe kofin Copa Del Rey

Duk Labarai
Wannan Bidiyon na Lamine Yamal da abokan wasansa a Barcelona suna chasewa sa wakar Shake Body ta Skales a dakin canja kaya bayan lashe kofin Copa Del Rey ya dauki hankula. Dama dai a can baya Lamine Yamal ya chase da wannan waka. https://www.tiktok.com/@juanlopezf10/video/7497781397294222614?_t=ZM-8vsepjaX16s&_r=1 https://twitter.com/AfricaFactsZone/status/1916416737517490564?t=uEWb0Q2wEpVAzfyPgpksow&s=19 Barcelona ta lashe kofinne bayan lallasa Real Madrid da ci 3-2.
Ji Yanda Tsohon Ministan Sufuri Amaechi ya bayar da labarin yanda Allah ya tuka motarsa bayan da bacci ya kwasheshi yana tsaka da tuki daga Kaduna zuwa Abuja

Ji Yanda Tsohon Ministan Sufuri Amaechi ya bayar da labarin yanda Allah ya tuka motarsa bayan da bacci ya kwasheshi yana tsaka da tuki daga Kaduna zuwa Abuja

Duk Labarai
Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayar da labarin cewa, akwai sanda ya tuka mota daga kaduna zuwa Abuja yana bacci inda yace allah ne ya tuka motar ya kaisu Abuja lafiya. Ya ce a lokacin sun je Kanone sun nada sarki, zasu koma sai aka hana sayar musu da tikitin jirgin sama. Yace sai ya kira tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar dashi inda Kwankwason yace masa ya je gidan gwamnatin jihar. Saidai yace a yayin da yake shirin tafiyane sai shugabab DSS na Kano ya sameshi yace masa duk abinda yake ciki ya fice daga garin Kano dan ba zai iya bashi tabbacin kariyar rayuwarsa ba. Yace ya gayawa shugaban DSS din yanda suka yi da Gwamna, yace masa amma kada ya sake ya je gidan gwamnatin, su fice daga Kano kawai. Amachi yace tare dashi akwai Goje, Baraje da Pro...
Ji yanda aka kama wasu ‘yan Najeriya na shirin shiga kasar Ingila da wani yaro da suka sata daga Najeriya

Ji yanda aka kama wasu ‘yan Najeriya na shirin shiga kasar Ingila da wani yaro da suka sata daga Najeriya

Duk Labarai
Hukumomin kula da iyaka na kasar Ingila sun kama wasu mutane biyu mace da namiji daga Najeriya wanda suka yi yunkurin shiga kasar da wani yaro da aka yi amannar satoshi suka yi. Hukumomin kula da iyakar a filin jirgin sama na Manchester sun tsargu da mutanen bayan ganin yanda suke tafiya da yaron. Ko da aka bincikesu sai namijin me suna Raphael Ossai yace shine mahaifin yaron sannan kuma matar da suke tare Oluwakemi Olasanoye wai itace mahaifiyar yaron. Saidai da bincike yayi tsanani, an gano cewa, akwai kuma wata takardar haihuwa data bayyana wata mata dake zaune a kasar ta Ingila wadda aka bayyana da cewa itace mahaifiyar yaron. Tuni dai aka kama matar da namijin.
Allah Sarki:Ji yanda wata mata me ciki ta rasu a Babban Asibitin Minna ana tsaka da mata aiki Nepa suka dauke wuta kuma babu fetir a cikin Janareta

Allah Sarki:Ji yanda wata mata me ciki ta rasu a Babban Asibitin Minna ana tsaka da mata aiki Nepa suka dauke wuta kuma babu fetir a cikin Janareta

Duk Labarai
Labarin wata mata me ciki da ta rasu a babban asibitin garin Minna na jihar Naija, Babbangida Aliyu General Hospital yayin da ake mata aiki ya yadu sosai a kafafen sada zumunta. Mijin matar ne ya wallafa labarin a shafinsa inda labarin ya watsu sosai. Yace an farawa matar tasa aiki da wutar Nepa, sai aka dauke. Ashe Janaretan ba man fetur, sai da aka je aka siyo mai aka zubawa janaretan amma yaki tashi, yace sai da aka je aka kira makanike. Yace a yayin da ake duk wannan abin, matarsa na cikin dakin tiyatar an fara mata aiki ba'a gama ba. Danga nan ne ta rasu. Muna fatan Allah ya jikanta